107 - Suratu Al'maaoun
Da sunan Allah Mai rahama
(1) Shin, ka ga wanda ke ƙaryatãwa game da sakamako?

(2) To, wan nan shi ne ke tunkure marãya (daga haƙƙinsa).

(3) Kuma bã ya kwaaitarwa bisa bãyar da abinci ga matalauci.

(4) To, bone yã tabbata ga masallata.

(5) Waɗan da suke masu shagala daga sallar su.

(6) Waɗan da suke yin riya (ga ayyukansu)

(7) Kuma suna hana taimako.