منتديات إنما المؤمنون إخوة (2024 - 2010) The Believers Are Brothers

(إسلامي.. ثقافي.. اجتماعي.. إعلامي.. علمي.. تاريخي.. دعوي.. تربوي.. طبي.. رياضي.. أدبي..)
 
الرئيسيةالأحداثأحدث الصورالتسجيل
(وما من كاتب إلا سيبلى ** ويبقى الدهر ما كتبت يداه) (فلا تكتب بكفك غير شيء ** يسرك في القيامة أن تراه)

soon after IZHAR UL-HAQ (Truth Revealed) By: Rahmatullah Kairanvi
قال الفيلسوف توماس كارليل في كتابه الأبطال عن رسول الله -صلى الله عليه وسلم-: "لقد أصبح من أكبر العار على أي فرد مُتمدين من أبناء هذا العصر؛ أن يُصْغِي إلى ما يظن من أنَّ دِينَ الإسلام كَذِبٌ، وأنَّ مُحَمَّداً -صلى الله عليه وسلم- خَدَّاعٌ مُزُوِّرٌ، وآنَ لنا أنْ نُحارب ما يُشَاعُ من مثل هذه الأقوال السَّخيفة المُخْجِلَةِ؛ فإنَّ الرِّسَالة التي أدَّاهَا ذلك الرَّسُولُ ما زالت السِّراج المُنير مُدَّةَ اثني عشر قرناً، لنحو مائتي مليون من الناس أمثالنا، خلقهم اللهُ الذي خلقنا، (وقت كتابة الفيلسوف توماس كارليل لهذا الكتاب)، إقرأ بقية كتاب الفيلسوف توماس كارليل عن سيدنا محمد -صلى الله عليه وسلم-، على هذا الرابط: محمد بن عبد الله -صلى الله عليه وسلم-.

يقول المستشرق الإسباني جان ليك في كتاب (العرب): "لا يمكن أن توصف حياة محمد بأحسن مما وصفها الله بقوله: (وَمَا أَرْسَلْنَاكَ إِلَّا رَحْمَةً لِّلْعَالَمِين) فكان محمدٌ رحمة حقيقية، وإني أصلي عليه بلهفة وشوق".
فَضَّلَ اللهُ مِصْرَ على سائر البُلدان، كما فَضَّلَ بعض الناس على بعض والأيام والليالي بعضها على بعض، والفضلُ على ضربين: في دِينٍ أو دُنْيَا، أو فيهما جميعاً، وقد فَضَّلَ اللهُ مِصْرَ وشَهِدَ لها في كتابهِ بالكَرَمِ وعِظَم المَنزلة وذَكَرَهَا باسمها وخَصَّهَا دُونَ غيرها، وكَرَّرَ ذِكْرَهَا، وأبَانَ فضلها في آياتٍ تُتْلَى من القرآن العظيم.
(وما من كاتب إلا سيبلى ** ويبقى الدهر ما كتبت يداه) (فلا تكتب بكفك غير شيء ** يسرك في القيامة أن تراه)

المهندس حسن فتحي فيلسوف العمارة ومهندس الفقراء: هو معماري مصري بارز، من مواليد مدينة الأسكندرية، وتخرَّجَ من المُهندس خانة بجامعة فؤاد الأول، اشْتُهِرَ بطرازهِ المعماري الفريد الذي استمَدَّ مَصَادِرَهُ مِنَ العِمَارَةِ الريفية النوبية المَبنية بالطوب اللبن، ومن البيوت والقصور بالقاهرة القديمة في العصرين المملوكي والعُثماني.
رُبَّ ضَارَّةٍ نَافِعَةٍ.. فوائدُ فيروس كورونا غير المتوقعة للبشرية أنَّه لم يكن يَخطرُ على بال أحَدِنَا منذ أن ظهر وباء فيروس كورونا المُستجد، أنْ يكونَ لهذه الجائحة فوائدُ وإيجابيات ملموسة أفادَت كوكب الأرض.. فكيف حدث ذلك؟!...
تخليص الإبريز في تلخيص باريز: هو الكتاب الذي ألّفَهُ الشيخ "رفاعة رافع الطهطاوي" رائد التنوير في العصر الحديث كما يُلَقَّب، ويُمَثِّلُ هذا الكتاب علامة بارزة من علامات التاريخ الثقافي المصري والعربي الحديث.
الشيخ علي الجرجاوي (رحمه الله) قَامَ برحلةٍ إلى اليابان العام 1906م لحُضُورِ مؤتمر الأديان بطوكيو، الذي دعا إليه الإمبراطور الياباني عُلَمَاءَ الأديان لعرض عقائد دينهم على الشعب الياباني، وقد أنفق على رحلته الشَّاقَّةِ من مَالِهِ الخاص، وكان رُكُوبُ البحر وسيلته؛ مِمَّا أتَاحَ لَهُ مُشَاهَدَةَ العَدِيدِ مِنَ المُدُنِ السَّاحِلِيَّةِ في أنحاء العالم، ويُعَدُّ أوَّلَ دَاعِيَةٍ للإسلام في بلاد اليابان في العصر الحديث.


 

 13 - Suratu Al'ra'ad

اذهب الى الأسفل 
كاتب الموضوعرسالة
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 48337
العمر : 71

13 - Suratu Al'ra'ad  Empty
مُساهمةموضوع: 13 - Suratu Al'ra'ad    13 - Suratu Al'ra'ad  Emptyالخميس 15 سبتمبر 2022, 4:53 pm

13 - Suratu Al'ra'ad
Da sunan Allah Mai rahama
(1) A. L̃. M̃.R. Waɗancan ayõyin littãfi ne kuma abin da aka saukar gare ka daga Ubangijinka ne gaskiya, kuma amma mafi yawan mutãne bã su yin ĩmãni.

(2) Allah Shi ne wanda Ya ɗaukaka sammai, bã da ginshiƙai ba waɗanda kuke ganin su. Sa'an nan kuma Ya daidaita a kan Al'arshi, kuma Ya hõre rãnã da watã, kõwane yanã gudãna zuwa ga ajali ambatacce. Yanã shirya al'amari, Yanã rarrabe ãyõyi daki-daki, mai yiwuwa ne ku yi yaƙĩni da haɗuwa da Ubangijinku.

(3) Kuma shĩ, ne wanda Ya shimfiɗa kasa, kuma Ya sanya duwãtsu da kõguna a cikinta, kuma daga dukan 'ya'yan itãce Ya sanya ma'aura biyu cikinsu. Yanã sanya dare ya rufe yini. Lalle ne a cikin wancan, haƙĩƙa akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda suke yin tunãni.

(4) Kuma a cikin ƙasa akwai yankuna mãsu maƙwabtaka, da gõnaki na inabõbi da shũka da dabĩnai iri guda, da waɗanda bã iri guda ba, anã shayar da su da ruwa guda. Kuma Munã fĩfĩta sãshen sa a kan sãshe a wajen ci. Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi ga muiãne waɗan da suke hankalta.

(5) Kuma idan ka yi mãmãki, to, mãmãkin kam shi ne maganarsu, "Shin, idan muka kasance turɓãya, zã mu zama a cikin wata halitta sãbuwa?" Waɗancan ne waɗanda suka kãfirta da Ubangijinsu, kuma waɗanda akwai ƙuƙumai a cikin wuyõyinsu, kuma waɗancan ne abõkan wuta. Sũ, a cikinta, mãsu dawwama ne.

(6) Kuma sunã nẽman ka da gaggãwa da azãba a gabãnin rahama, alhãli kuwa abũbuwan misãli sun gabãta a gabãninsu. Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Ma'abũcin gãfara ne ga mutãne a kan zãluncinsu, kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Mai tsananin uƙũba ne.

(7) Kuma waɗanda suka kãfirta sunã cẽwa don me ba a saukar da wata ãyã a gare shi ba daga Ubangijin sa? Abin sani kawai, kai dai mai gargaɗi ne kuma a cikin kõwaɗanne mutãne akwai mai shiryarwa.

(8) Allah Yanã sanin abin da kõwace mace take ɗauke da shi a cikinta da abin da mahaifu suke ragẽwa* da abin da suke ƙãrãwa. Kuma dukkan kõme, a wurinSa, da gwargwado yake.
* Ragõwar lõkacin cikin ko ƙãruwarsa.

(9) Shi ne Masanin fake da bayyane, Mai girma, Maɗaukaki.

(10) Daidai ne daga gare ku, wanda ya asirta magana da wanda ya bayyana game da ita, da wanda yake shi mai nẽman ɓõyewa ne da dare, da mai bayyana a cikin tafiyarsa a hanya da rãna*.
* Hasken rãnã mai kama da ruwa ga idon mai dũbi daga nesa.

(11) (Kowannenku) Yanã da waɗansu malã'iku mãsu maye wa jũna a gaba gare shi da bãya gare shi, sunã tsare shi daga umurnin Allah. Lalle ne Allah bã Ya canja abin da yake ga, mutãne sai sun canja abin da yake ga zukatansu. Kuma idan Allah Ya yi nufin wata azãba game da mutãne, to, bãbu mai mayar da ita, kuma bã su da wani majiɓinci* baicin Shi.
* Bãbu wani majiɓinci baicin Allah, wanda zai iya tsĩrar da su daga azãbarsa.

(12) Shĩ ne Wanda Yake nũna muku walƙiya dõmin tsõro da tsammãni, kuma Ya ƙãga halittar girãgizai mãsu nauyi.

(13) Kuma arãdu tanã tasbĩhi game da gõde Masa, da malã'iku dõmin tsoronsa. Kuma Yanã aiko tsãwawwaki, sa'an nan Ya sãmi wanda Yake so da su alhãli kuwa sũ, sunã jãyayya a cikin (al'amarin) Allah kuma shĩ ne mai tsananin hĩla.*
* Hĩla, ita ce mãkirci, Allah Yanã azabta mãsu yin hĩla ga addininsa, da azãba mai tsanani, kuma Ya kãmã su da hĩlarsu ta hanyar da ba su sani ba.

(14) Yanã da kiran gaskiya, kuma waɗanda (kãfirai) suke kira baicinsa, bã su karɓa musu da kõme fãce kamar mai shimfiɗa tãfukansa Zuwa ga ruwa (na girgije) dõmin (ruwan) ya kai ga bãkinsa, kuma shi bã mai kaiwa gare shi ba. Kuma kiran kãfirai (ga wanin Allah) bai zama* ba fãce yanã a cikin ɓata.
* Allah Mamallakin ruwa, Yanã kiran mutãne dõmin Ya bã su ruwan su shã. Su kuma kãfirai sunã kiran waɗansu abũbuwa dabam waɗanda kõ karɓa musu kiran bã zã su iya yi ba, kuma sunã neman ruwa daga gare su, alhãli kuma ba su mallaki kõme ba. Watau Mai abu Yanã kiran su dõmin Ya bã su, sun ƙi karɓa Masa sai sunã kiran wani wanda bai mallaki kõme ba, sunã rõƙon Sa ruwa.

(15) Kuma sabõda Allah wanda yake a cikin sammai da ƙasa suke yin sujada, so da ƙi, kuma da inuwõyinsu, a sãfe da maraice.

(16) Ka ce: "Wãne ne Ubangijin sammai da ƙasa?" Ka ce: "Allah". Ka ce: "Ashe fa, kun riƙi waɗansu masõya baicin Shi, waɗanda ba su mallaka wa kansu wani amfãni ba kuma haka bã su tũre wata cũta?" Ka ce: "Shin makãho da mai gani sunã daidaita? Kõ shin duhu da haske sunã daidaita? ko sun sanya ga Allah waɗansu abõkan tãrayya waɗanda suka yi halitta kamar halittarSa sa'an nan halittar ta yi kama da jũna a gare su?" Ka ce: "Allah ne Mai halitta kõme kuma Shĩ ne Maɗaukaki, Marinjãyi."

(17) Ya saukar da ruwa daga sama*, sai magudanai suka gudãna da gwargwadonsu, Sa'an nan kõgi ya ɗauki kumfa mai ƙãruwa, kuma daga abin da suke zuga a kansa (azurfa ko zinari kõ ƙarfe) a cikin wuta dõmin nẽman ado kõ kuwa kãyan ɗãki akwai kumfa misãlinsa (kumfar ruwa). Kamar wancan ne Allah Yake bayyana gaskiya da ƙarya. To, amma kumfa, sai ya tafi ƙẽƙasasshe, kumaamma abin da yake amfãnin mutãne sai ya zauna a cikin ƙasa. Kamar wancan ne Allah Yake bayyana misãlai.
* Idan ruwa ya sauka daga sama sa'an nan ya gudãna a cikin rãfuna zai yi kumfa. Sai ruwa mai amfãnin mutãne ya nutse a ƙasa ya zauna, sa'an nan kumfan kuma ya ƙeƙashe ya lãlãce. Haka kuma idan an sanya ƙarfe na zinãri kõ na azurfa kõ baƙin ƙarfe a cikin wuta, aka zuga ta a kansa, zai fitar da kumfa, wãtau tsakin tama wanda zã a fitar dõmin rashin amfãninsa, dõmin zĩnariyar ƙwarai mai amfãni ta wanzu. To haka ga kõme akwai kumfa marashin amfãni da mai kyãwo mai amfani.

(18) Ga waɗanda* suka karɓa wa Ubangijinsu akwai abu mafi kyau a gare su, kuma waɗanda suke ba su karɓa Masa ba, to, lalle dã sunã da abin da yake a cikin ƙasa gaba ɗaya da misãlinsa tãre da shi, haƙĩƙa, dã sun yi fansa da shi. Waɗancan sunã da mummunan bincike kuma matabbatarsu Jahannama ce, kuma tir da ita ta zama shimfida.
* Bãyan da ya faɗi cewa Allah Yanã kira, kiran gaskiya a cikin ãyã ta l4, kuma waɗansu mutãne sun ƙi karɓar kiran Allah, sai sunã kiran waɗansu abũbuwa dabam, sai ya bayyana, a nan, sakamakon wanda ya karɓi kiran Allah sãmun ruwan sha, sabõda Mai abu ne Ya kirãwo shi, Ya kuma bã shi, ya sha a hankali kwance, sa'an nan kuma Allah zai bã shi abin da ya fi ruwan kyau, watau Aljanna. Amma wanda ya ƙi karɓãwa, to, yã yi hasãra biyu, bai sãmi ruwan da ya yi kiran wani ya bã shi ba, sa'an nan kuma ya haɗu da azãbar da take zai iya bãyar da dukan abin da ya mallaka dõmin ya yi fansar kansa da ita.

(19) Shin, fa, wanda yake sanin cẽwa lalle abin da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka ne gaskiya yanã zama kamar wanda yake makãho? Abin sani kawai masu hankali sũ ke yin tunãni.

(20) Sũ ne waɗan da suke cikãwa da alkawarin Allah, kuma bã su warware alkawari.

(21) Kuma sũ ne waɗan da suke sãdar da abin da Allah Ya yi umurni da shi dõmin a sãdar da shi kuma sunã tsõron Ubangijinsu, kuma sunã tsõron mummũnan bincike.

(22) Kuma waɗanda suka yi haƙuri dõmin nẽman yardar Ubangijinsu, kuma suka tsayar da salla, kuma suka ciyar da abin da Muka azurta su da shi, a asirce da bayyane, kuma sunã tunkuɗe mummunan aiki da mai kyau. Waɗancan sunã da ãƙibar gida mai kyau.

(23) Gidãjen Aljannar zama sunã shigarsu, sũ da waɗandasuka kyautatu daga iyãyensu, da mãtansu da zũriyarsu. Kuma malã'iku sunã shiga zuwa gunsu ta kõwace kõfa.

(24) "Aminci* ya tabbata a kanku sabõda abin da kuka yi wa haƙuri. Sãbõda haka madalla da ni'imar ãƙibar gida."
* Sallamar malã'iku a kansu idan sun shiga a gare su, ita ce su ce musu: "Aminci ya tabbata a gare ku.".

(25) Kuma waɗanda* suka warware alkawarin Allah daga bãyan ƙulla shi, kuma sunã yanke abin da Allah Ya yi umurui da shi dõmin a sãdar da shi kuma sunã ɓarna a cikin ƙasar. Waɗancan sunã da wata la'ana, kuma sunã da mũnin gida.
* Bayãnin siffõfin waɗanda suka ƙi karɓar kiran Allah. Watau akasin waɗanda aka yi bayaninsu a bãyã.



13 - Suratu Al'ra'ad  2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 48337
العمر : 71

13 - Suratu Al'ra'ad  Empty
مُساهمةموضوع: رد: 13 - Suratu Al'ra'ad    13 - Suratu Al'ra'ad  Emptyالخميس 15 سبتمبر 2022, 4:53 pm


(26) Allah ne Yake* shimfiɗa arziki ga wanda Yake so, kuma Yanã ƙuntatãwa. Kuma sun yi farin ciki da rãyuwar dũniya, alhalikuwa rãyuwar dũniya ba ta zama ba dangane ga ta Lãhira fãce jin dãɗi kaɗan.
* Ta'aƙĩbi da tambĩhi ne da ƙãrin bayãni ga mai hankali dõmin ya zãbura ga karɓar kiran Allah.

(27) Kuma wanɗanda suka kãfirta, sunã cẽwa, "Don me ba a saukar da wata ãyã ba a kansa daga Ubangijinsa?" Ka ce: "Lalle ne Allah Yanã ɓatar da wanda Yake so kuma Yanã shiryar da wanda ya tũba zuwa gare shi."

(28) Waɗanda suka yi ĩmãni kuma zukãtansu sukan natsu da ambaton Allah. To, da ambaton Allah* zukãta suke natsuwa.
* Ambaton Allah, shĩ ne bin hukunce-hukuncensa ga kõme. Umar ɗan Khattãb ya ce: "Mafificin ambaton Allah, shi ne wanda aka yi a wurin umurninsa ko haninsa. Wanda yake yin zikirin bãki ba da yanã aiki da hukunce-hukuncen Allah ba a cikin ibãdarsa da mu'amalarsa, to, shi mai izgili kawai ne da sũnan Ubangijinsa, ba mai yin zikiri ba ne.".

(29) Waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata aiki nagari, farin ciki yã tabbata a gare su, da kyakkyawar makõma.

(30) Kamar wancan ne Muka aika ka a cikin al'umma wanda take waɗansu al'ummai sun shũɗe daga gabaninta, dõmin ka karanta musu abin da Muka yi wahayi zuwa a gare ka, alhãli kuwa sũ, sunãkãfirta da Rahaman.* Ka ce: "Shi ne Ubangijĩna, bãbu abin, bautãwa fãce Shi, a gare Shi na dõgara, kuma zuwa gare Shi tũbãta take."
* Sũnan Allah Rahmãn, daga rahama, watau Mai Rahama wadda yake dukan alheri yanã shiga a cikin ma'anarta a wajen halitta da rãyuwa da bãyar da lãfiya da shiryarwa. Mafi girman nĩ'imarsa shĩ ne aikõwar Manzon Allah daga gare mu zuwa gare mu. Kãfirai ba su yi tunãni ba a kan waɗannan rahamõmi, balle su yi gõdiya, sabõda haka sai kãfirci suke yi.

(31) Kuma dã lalle an saukar da wani littafi abin karatu wanda ake tafiyar da duwãtsu game da shi, kõ kuma aka yanyanke ƙasa da shi, ko kuwa aka yi magana da matattu da shi (dã ba su yi ĩmãni ba). Ã'a ga Allah al'amari yake gabã ɗaya! Shin fa, waɗanda suka yi ĩmãni ba su yanke tsammãni ba da cẽwa da Allah Yã so, dã Yã shiryar da mutãne gabã ɗaya? Kuma waɗanda suka yi kãfirci ba zã su gushe ba wata masĩfa tanã samun su sabõda abin da suka aikata, kõ kuwa ka saukã* kusa da gidãjẽnsu, har wa'adin Allah ya zo. Kuma lalle ne Allah bã ya sãɓã wa lõkacin alkawari.
* Annabi ya sauka kusa da gidãjen Ƙuraishãwa a rãnar bũɗe Makka. Kuma wannan hukunci yanã nan yanã aiki ga mãsu ƙiyayya da addini, kullum masĩfu sunã aukuwa a kansu har rãnar da Musulunci ya rinjãye su.

(32) Kuma lalle ne, haƙĩƙa, an yi izgili da Manzanni kãfinka, sai Na yi jinkiri ga waɗanda suka kãfirta, sa'an nan Na kãma su. To, yãya uƙũbãta take?

(33) Shin fa, wanda shĩ Yake tsaye a kan kõwane rai game da abin da ya tanada (zai zama kamar wanda ba haka ba)? Kuma suka sanya abõkan tãrayya ga Allah! Ka ce: "Ku ambaci sũnãyensu."Ko kunã bai wa Allah lãbãri ne game da abin da bai sani ba a cikin ƙasa? Kõ da bayyananniyar magana kuke yin shirka, (banda a cikin zũciya)? Ã'a, an dai ƙawãta wa waɗanda suka kafirta mãkircinsu kuma an kange su daga hanya. Kuma wanda Allah Ya ɓatar to, bãbu wani mai shiryarwa a gare shi!"

(34) Sunã da wata azãba a cikin rãyuwar dũniya, kuma haƙĩƙa azãbar Lãhira ce mafi tsanani kuma bãbu wani mai tsare su daga Allah.

(35) Misãlin Aljanna wadda aka yi alkawarinta ga mãsu taƙawa, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinta. Abincinta yana madawwami da inuwarta. Waccan ce ãƙibar waɗanda suka yi taƙawa, kuma ãƙibar kãfirai, ita ce wuta,

(36) Kuma waɗanda Muka bã su Littãfi sunã farin ciki da abin da aka saukar zuwa gare ka, kuma daga ƙungiyõyi akwai mai musun sãshensa. Ka ce: "Abin sani kawai, an umurce ni da in bauta wa Allah kuma kada in yi shirka da Shi, zuwa gare Shi nake kira, kuma zuwa gare Shi makõmata take."

(37) Kuma kamar wancan ne Muka saukar da shi*, Hukunci a cikin Lãrabci. Kuma lalle ne idan kã bi son zuciyõyinsu a bãyan abin da ya zo maka na ilmi, bãbu wani masõyi a gare ka mai kãre ka daga Allah, kuma bãbu matsari.
* Kamar yadda littattafan farko suke, haka Alƙur'ãni yake daga Allah, sai dai shi Alƙur'ãni an saukar da shi a cikin Lãrabci.

(38) Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun aika waɗansu manzanni, daga gabãninka, kuma Muka sanya mãtan aure a gare su da zũriyya, kuma ba ya kasancẽwa ga wani Manzo ya zo da wata ãyã, sai da iznin Allah. Ga kõwane ajali* akwai littãfi.
* Aikõwar Manzanni da littattafai ba ya hana Allah Ya aiko wani Manzo daga bãya da wani littãfi wanda ya shãfe abin da yake cikin littattafan farko. Allah Yã tabbatar da abin da yake so na hukunce-hukuncen da suka gabãta dõmin dõgewar aikinsu ga mutãne har yanzu, kuma Ya shãfe abin da yake so sabõda amfãninsu da hukuncinsu yã shige, sabõda wata hikima da Allah Ya sani amma asalin littattãfan duka wanda bã zai canja ba a cikin sanin Allah, yanã wurinsa.".

(39) Allah Yanã shafe abin da Yake so, kuma Yanã tabbatarwa kuma a wurinsa asalin Littãfin yake.

(40) Kuma imma lalle Mu nũna* maka sãshen abin da Muke yi musu wa'adi, kõ kuwa lalle Mu karɓi ranka to abin sani kawai iyarwa ce a kanka, kuma hisãbi yana gare Mu.
* Idan Mun so Mu yi musu azãba a gaban idonka zã Mu yi musu, kuma idan Mun so Mu jinkirta musu har a bãyan ka mutu, wannan bã aikinka ba ne, Nãmu ne. Abin da yake aikinka shĩ ne iyar da manzanci kawai. Yin hisãbi a kansu alhakin Allah ɗai ne.

(41) Shin, kuma ba su gani ba cẽwa lalle ne, Muna jẽ wa ƙasar (su), Munã rage ta daga gẽfunanta? Kuma Allah ne Yake yin hukuncinsa. Babu mai bincike ga hukuncinsa. Kuma shĩ ne Mai gaggãwar sakamako.*
* Gaggãwar sakamako ga wanda ya ƙi bin umurnin Allah wanda Annabinsa ya iyar zuwa gare shi. Asalin hisãbi, shine bincike dõmin a sãmi abin da aka yi na alhħri kõ na sharri amma abin da ake nufi a nan maƙasũdin bincike shĩ ne sakamako da alhħri kõ da azãba, gwargwadon nufinSa.

(42) Kuma lalle ne waɗanda suke a gabãninsu sun yi mãkirci. To, ga Allah mãkircin yake gabã ɗaya. Ya san abin da kõwane rai yake tãnada. Kuma kãfirai zã su sani, ga wane ãƙibar gida take.

(43) Kuma waɗanda suka kãfirta sunã cẽwa: "Ba a aiko ka ba." Ka ce, "Allah Yã isa zama shaida a tsakãnina da tsakãninku da wanda yake a wurinsa akwai ilmin* Littãfi."
* Allah Yã isa zama shaida, haka wanda yake a kan wani ilmi daga Allah kamar Yahudu da Nasãra sunã isa zama shaida a tsakãnĩna da ku a kan gaskiyar da'awã ta cewa nĩ abin aikõwa ne daga Allah zuwa gare ku dõmin akwai wannan magana a cikin littattafanku.



13 - Suratu Al'ra'ad  2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
 
13 - Suratu Al'ra'ad
الرجوع الى أعلى الصفحة 
صفحة 1 من اصل 1
 مواضيع مماثلة
-
» 30 - Suratu Ar'rum
» 5 - Suratu Al'ma'ida
» 95 - Suratu At'tín
» 30 - Sûratu'r-Rûm
» 114 - Suratu Al'nas

صلاحيات هذا المنتدى:لاتستطيع الرد على المواضيع في هذا المنتدى
منتديات إنما المؤمنون إخوة (2024 - 2010) The Believers Are Brothers :: (English) :: Group Forums No. 14 :: The Holy Quran is translated :: Hausa-
انتقل الى: