96 - Suratu Al'alaq
Da sunan Allah Mai rahama
(1) Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda Ya yi halitta.

(2) Ya hahitta mutum daga gudan jini.

(3) Ka yi karatu, kuma Ubangijinka shi ne Mafi karimci.

(4) Wanda Ya sanar (da mutum) game da alƙalami.

(5) Ya sanar da mutum abin da bai sani ba.

(6) A'aha! Lalle, ne mutum haƙĩƙa, yana girman kai (ya ƙi karatu).

(7) Dõmin yã ga kansa, yã wadãta.

(8) Lalle ne zuwa ga Ubangijinka makoma take.

(9) Shin, kã ga wanda ke hana.

(10) Bãwã idan yã yi salla?

(11) Ashe, kã gani, idan (shi bãwan) ya kasance a kan shiriya?

(12) Ko ya yi umurni da taƙawa?

(13) Ashe, kã gani, idan (shi mai hanin) ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya?

(14) Ashe, bai sani ba cewa Allah Yanã gani?

(15) A'aha! Lalle ne, idan bai hanu ba, lalle ne zã Mu ja gãshin makwarkwaɗa.

(16) Makwarkwaɗa maƙaryaciya, mai laifi.

(17) Sai ya kirayi ƙungiyarsa.

(18) Zã Mu kirayi zabaniyãwa (mala'iku mãsu girma).

(19) A'aha kada ka bĩ shi. Kuma ka yi tawali'u,* kuma ka nemi kusanta (zuwa ga Ubangijinka).
* Wato salla da sauran ibãdu.