أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn مؤسس ومدير المنتدى
عدد المساهمات : 52644 العمر : 72
| موضوع: 95 - Suratu Al'teen الإثنين 19 سبتمبر 2022, 4:43 pm | |
| 95 - Suratu Al'teen Da sunan Allah Mai rahama (1) Inã rantsuwa da Attinu da Azzaitũn.* * Ibn Abbas ya ce: 'Attinu shi ne masallacin Nuhu a kan Judiyyi, Azzaitun Masallacin Baitil Muƙaddas.'.
(2) Da Dũr Sĩnĩna.* * Dutsen da Allah Ya yi magana da Musa a kansa. Ma'anarsa dutse mai albarka sabõda itacen da ke kansa.
(3) Da wannan gari* amintacce. * Gari amintacce shi ne Makkah.
(4) Lalle ne, Mun halitta mutum a cikin mafi kyawon tsayuwa.
(5) Sa'an nan, Muka mayar da shi mafi ƙasƙantar masu rauni
(6) Face waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, saboda haka suna da sakamako wanda bã ya yankewa.
(7) To, bãyan haka mẽ ya sanya ka ka ƙaryata sakamako (wanda za a yi a bãyan Tãshin ¡iyãma)?
(8) Ashe Allah bã Shi ne Mafi mãsu hukunci kyãwon hukunci ba?* * Ana son wanda ya karanta sũrar har ƙarshe ya ce بلى ,wato na'am, Allah Ya fi kowa kyãwon hukunci. |
|