92 - Suratu Al'lail
Da sunan Allah Mai rahama
(1) Inã rantsuwa da dare a lõkacin da yake rufẽwa.

(2) Da yini a lõkacin da yake kuranyẽwa.

(3) Da abin da ya halitta namiji da mace.

(4) Lãlle ne ayyukanku, dabam-dabam suke.

(5) To, amma wanda ya yi kyauta, kuma ya yi taƙawa.

(6) Kuma ya gaskata kalma* mai kyãwo.
* Kalma mai kyãwo ita ce Kalmar shahãda da abin da ta ƙunsa na addinin Musulunci, wanda yake yinsa kamar yadda Allah Ya ce, ta hanyan Manzon Sa, shi ne taƙawa.

(7) To, zã Mu sauƙaƙe masa har ya kai ga sauƙi.

(8) Kuma amma wanda ya yi rõwa, kuma ya wadãtu da kansa.

(9) Kuma ya ƙaryatar da kalma mai kyãwo.

(10) To, zã Mu sauƙaƙke masa har ya kai ga tsanani.

(11) Kuma dũkiyarsa ba ta wadãtar masa da kõme ba, a lõkacin da ya gangara (a wuta).

(12) Lãlle aikin Mu ne, Mu bayyana shiriya.

(13) Kuma lalle ne Lãhira da duniya Namu ne.

(14) Sabõda haka, Na yi maku gargaɗi da wuta mai babbaka.

(15) Bãbu mai shigarta sai mafi Tabewa

(16) Wanda ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya.

(17) Kuma mafi taƙawa* zai nisance ta.
* Mafi taƙawa da Mafi shaƙãwa suna ma'anar mai taƙawa da shaƙiyyi.

(18) Wanda yake bãyar da dũkiyarsa, alhãli yana tsarkaka.

(19) Alhãli bãbu wani mai wata ni'ima wurinsa wadda ake nẽman sakamakonta.

(20) Fãce dai nẽman yardar Ubangijinsa Mafi ɗaukaka.

(21) To, lalle ne zai yarda (da sakamakon da zã a bã shi).