أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn مؤسس ومدير المنتدى
عدد المساهمات : 52644 العمر : 72
| موضوع: 88 - Suratu Algashiyah الإثنين 19 سبتمبر 2022, 4:32 pm | |
| 88 - Suratu Algashiyah Da sunan Allah Mai rahama (1) Lalle ne labãrin (¡iyãma) mai rufe mutãne da tsoronta yã zo maka?
(2) Wasu huskõki a rãnar nan ƙasƙantattu ne.
(3) Mãsu aikin wahala ne, mãsu gajiya.
(4) Zã su shiga wata wuta mai zãfi.
(5) Ana shãyar da su daga wani marmaro mai zãfin ruwa.
(6) Ba su da wani abinci fãce dai daga danyi.
(7) Bã ya sanya ƙiba, kuma bã zai wadãtar daga yunwa ba.
(8) Wasu huskõki a rãnar nan mãsu ni'ima ne.
(9) Game da aikinsu, masu yarda ne.
(10) (Suna) a cikin Aljanna maɗaukakiya.
(11) Bã zã su ji yãsassar magana ba, a cikinta.
(12) A cikinta akwai marmaro mai gudãna.
(13) A cikinta akwai gadãje maɗaukaka.
(14) Da kõfuna ar'aje.
(15) Da filõli* jẽre, * Matãsan kai.
(16) Da katifu shimfiɗe.
(17) Ashe to bã zã su dũbãwa ba ga rãƙumã yadda aka halitta su?
(18) Da zuwa ga sama yadda aka ɗaukaka ta?
(19) Da zuwa ga duwãtsu yadda aka kafa su?
(20) Da zuwa ga ƙasa yadda aka shimfiɗã ta?
(21) sabõda haka, ka yi wa'azi, kai mai yin wa'azi ne kawai.
(22) Ba ka zama mai ĩkon tanƙwasãwa a kansu ba.
(23) Fãce dai duk wanda ya jũya bãya, kuma ya kãfirta.
(24) To, Allah zai yi masa azãba, azãbar nan da take mafi girma.
(25) Lalle ne, zuwa gare Mu kõmõwarsu take.
(26) Sa'an nan lalle ne aikinMu ne Mu yi musu hisãbi. |
|