أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn مؤسس ومدير المنتدى
عدد المساهمات : 52644 العمر : 72
| موضوع: 82 - Suratu Al'ifidar الإثنين 19 سبتمبر 2022, 4:14 pm | |
| 82 - Suratu Al'ifidar Da sunan Allah Mai rahama (1) Idan sama ta tsãge.
(2) Kuma idan taurãri suka wãtse.
(3) Kuma idan tẽkuna aka facce su.
(4) Kuma idan kaburbura aka tõne su.
(5) Rai yã san abin da ya gabatar, da abin da yã jinkirtar.
(6) Yã kai mutum! Mẽ ya rũɗe ka game da Ubangijinka, Mai karamci.
(7) Wanda Ya halitta ka sa'an nan ya daidaitã ka, Ya kuma tsakaitã ka.
(8) A cikin kõwace irin sũra Ya so Ya ginã ka a kanta.
(9) A'aha, bã haka ba, kuna ƙaryatãwa game da sakamako!
(10) Lalle ne, a kanku, haƙiƙa akwai matsara.
(11) Mãsu daraja, marubũta.
(12) Sunã sanin abin da kuke aikatãwa.
(13) Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah, dãhir, suna cikin ni'ima.
(14) Kuma lalle ne, fãjirai, dãhir, sunã cikin Jahĩm.
(15) Zã su shigẽ ta a rãnar sakamako.
(16) Bã zã su faku daga gare ta ba.
(17) Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa ranar sakamako?
(18) Sa'an nan, mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rãnar sakamako?
(19) Rãnã ce da wani rai ba ya iya mallakar kõme dõmin wani rai al'amari, a rãnar nan, ga Allah (ɗai) yake. |
|