منتديات إنما المؤمنون إخوة (2024 - 2010) The Believers Are Brothers

(إسلامي.. ثقافي.. اجتماعي.. إعلامي.. علمي.. تاريخي.. دعوي.. تربوي.. طبي.. رياضي.. أدبي..)
 
الرئيسيةالأحداثأحدث الصورالتسجيل
(وما من كاتب إلا سيبلى ** ويبقى الدهر ما كتبت يداه) (فلا تكتب بكفك غير شيء ** يسرك في القيامة أن تراه)

IZHAR UL-HAQ

(Truth Revealed) By: Rahmatullah Kairanvi
قال الفيلسوف توماس كارليل في كتابه الأبطال عن رسول الله -صلى الله عليه وسلم-: "لقد أصبح من أكبر العار على أي فرد مُتمدين من أبناء هذا العصر؛ أن يُصْغِي إلى ما يظن من أنَّ دِينَ الإسلام كَذِبٌ، وأنَّ مُحَمَّداً -صلى الله عليه وسلم- خَدَّاعٌ مُزُوِّرٌ، وآنَ لنا أنْ نُحارب ما يُشَاعُ من مثل هذه الأقوال السَّخيفة المُخْجِلَةِ؛ فإنَّ الرِّسَالة التي أدَّاهَا ذلك الرَّسُولُ ما زالت السِّراج المُنير مُدَّةَ اثني عشر قرناً، لنحو مائتي مليون من الناس أمثالنا، خلقهم اللهُ الذي خلقنا، (وقت كتابة الفيلسوف توماس كارليل لهذا الكتاب)، إقرأ بقية كتاب الفيلسوف توماس كارليل عن سيدنا محمد -صلى الله عليه وسلم-، على هذا الرابط: محمد بن عبد الله -صلى الله عليه وسلم-.

يقول المستشرق الإسباني جان ليك في كتاب (العرب): "لا يمكن أن توصف حياة محمد بأحسن مما وصفها الله بقوله: (وَمَا أَرْسَلْنَاكَ إِلَّا رَحْمَةً لِّلْعَالَمِين) فكان محمدٌ رحمة حقيقية، وإني أصلي عليه بلهفة وشوق".
فَضَّلَ اللهُ مِصْرَ على سائر البُلدان، كما فَضَّلَ بعض الناس على بعض والأيام والليالي بعضها على بعض، والفضلُ على ضربين: في دِينٍ أو دُنْيَا، أو فيهما جميعاً، وقد فَضَّلَ اللهُ مِصْرَ وشَهِدَ لها في كتابهِ بالكَرَمِ وعِظَم المَنزلة وذَكَرَهَا باسمها وخَصَّهَا دُونَ غيرها، وكَرَّرَ ذِكْرَهَا، وأبَانَ فضلها في آياتٍ تُتْلَى من القرآن العظيم.
المهندس حسن فتحي فيلسوف العمارة ومهندس الفقراء: هو معماري مصري بارز، من مواليد مدينة الأسكندرية، وتخرَّجَ من المُهندس خانة بجامعة فؤاد الأول، اشْتُهِرَ بطرازهِ المعماري الفريد الذي استمَدَّ مَصَادِرَهُ مِنَ العِمَارَةِ الريفية النوبية المَبنية بالطوب اللبن، ومن البيوت والقصور بالقاهرة القديمة في العصرين المملوكي والعُثماني.
رُبَّ ضَارَّةٍ نَافِعَةٍ.. فوائدُ فيروس كورونا غير المتوقعة للبشرية أنَّه لم يكن يَخطرُ على بال أحَدِنَا منذ أن ظهر وباء فيروس كورونا المُستجد، أنْ يكونَ لهذه الجائحة فوائدُ وإيجابيات ملموسة أفادَت كوكب الأرض.. فكيف حدث ذلك؟!...
تخليص الإبريز في تلخيص باريز: هو الكتاب الذي ألّفَهُ الشيخ "رفاعة رافع الطهطاوي" رائد التنوير في العصر الحديث كما يُلَقَّب، ويُمَثِّلُ هذا الكتاب علامة بارزة من علامات التاريخ الثقافي المصري والعربي الحديث.
الشيخ علي الجرجاوي (رحمه الله) قَامَ برحلةٍ إلى اليابان العام 1906م لحُضُورِ مؤتمر الأديان بطوكيو، الذي دعا إليه الإمبراطور الياباني عُلَمَاءَ الأديان لعرض عقائد دينهم على الشعب الياباني، وقد أنفق على رحلته الشَّاقَّةِ من مَالِهِ الخاص، وكان رُكُوبُ البحر وسيلته؛ مِمَّا أتَاحَ لَهُ مُشَاهَدَةَ العَدِيدِ مِنَ المُدُنِ السَّاحِلِيَّةِ في أنحاء العالم، ويُعَدُّ أوَّلَ دَاعِيَةٍ للإسلام في بلاد اليابان في العصر الحديث.

أحْـلامٌ مِـنْ أبِـي (باراك أوباما) ***

 

 74 - Suratu Al'mudathir

اذهب الى الأسفل 
كاتب الموضوعرسالة
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 52644
العمر : 72

74 - Suratu Al'mudathir  Empty
مُساهمةموضوع: 74 - Suratu Al'mudathir    74 - Suratu Al'mudathir  Emptyالإثنين 19 سبتمبر 2022, 8:00 am

74 - Suratu Al'mudathir
Da sunan Allah Mai rahama
(1) Yã wanda ya lulluɓa da mayãfi.

(2) Ka tãshi dõmin ka yi gargaɗi

(3) Kuma Ubangijinka, sai ka girmama Shi,

(4) Kuma tutãfinka, sai ka tsarkake su,

(5) Kuma gumãka, sai ka ƙaurace musu.

(6) Kada ka yi kyauta kana nẽman ƙãri

(7) Kuma sabõda Ubangijinka? Sai ka yi haƙure

(8) To, idan aka yi bũsa a cikin ƙaho.

(9) To, wannan, a rãnar nan, yini ne mai wuya

(10) A kan kãfirai, bã mai sauƙi ba ne.

(11) Ka bar Ni da wanda Na halitta, yana shi kaɗai,

(12) Kuma Na sanya masa dũkiya shimfiɗaɗɗiya

(13) Da ɗiyã halartattu,

(14) Kuma Na shimfiɗa? masa kõme shimfiɗãwa.

(15) Sa'an nan, yanã kwaɗayin in yi masa ƙãri!

(16) Faufau! Lalle ne, shĩ yã kasance, ga ãyõyin Mu, mai tsaurin kai.

(17) Zã Ni kallafa masa wahala mai hauhawa.

(18) Lalle ne, Shi, yã yi tunãni, kuma yã ƙaddara (abin da zai faɗã game da Alƙur'ãni)

(19) Sabõda haka, aka la'ane shi, kamar yadda ya ƙaddara.

(20) Sa'an nan, aka la'ane shi kamar yadda ya ƙaddara.

(21) Sa'an nan, ya yi tunãni

(22) Sa'an nan, ya gintse huska? kuma ya yi murtuk.

(23) Sa'an nan, ya jũya bãya, kuma ya bunƙãsa,

(24) Sai ya ce: "Wannan abu dai bã kõme ba ne fãce wani sihiri, wanda aka ruwaito."

(25) "Wannan maganar mutum dai ce."



74 - Suratu Al'mudathir  2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 52644
العمر : 72

74 - Suratu Al'mudathir  Empty
مُساهمةموضوع: رد: 74 - Suratu Al'mudathir    74 - Suratu Al'mudathir  Emptyالإثنين 19 سبتمبر 2022, 8:00 am


(26) Zã Ni ƙõna shi da Saƙar.

(27) Kuma mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽwa Saƙar!

(28) Bã ta ragẽwa, kuma bã ta bari.

(29) Mai nãcẽwa ga jiki ce (da (ƙũna).

(30) A kanta akwai (matsara) gõma shã tara.

(31) Kuma ba Mu sanya ma'abũta wutã (wãto matsaranta) ba, fãce malã'iku, kuma ba Mu sanya adadinsu (gõma sha tara) ba, fãce dõmin fitina ga waɗanda suka kãfirta domin waɗanda aka bai wa littãfi su sãmi yaƙĩni kuma waɗanda suka yi ĩmãni su ƙãra ĩmãni, kuma waɗanda aka bai wa littãfi da mũminai bã zã su yi shakka ba, kuma domin wa ɗanda a cikin zukatansu akwai wata cuta da kãfirai su ce: "Mẽ Allah Yake nufi da wannan, ya kasance misãli?" Haka dai Allah ke ɓatar da wanda Ya so, kuma Ya shiryar da wanda ya so. Kuma bãbu wanda ya san mayãƙan Ubangijinka fãce Shi, kuma ita (wutar) ba ta kasance ba fãce wata tunãtarwa ce ga mutum.

(32) A'aha! Ina rantsuwa da watã.

(33) Da dare a lõkacin da ya jũyar da baya.

(34) Da sãfiya idan ta wãye.

(35) Ita (wutar) ɗayan manyan masĩfũ? ce.

(36) Mai gargaɗĩ ce ga mutum.

(37) Ga wanda ya so, daga cikinku, ya gabãta ko ya jinkirta.

(38) Kõwane rai ga abin da ya aikata jingina ce.

(39) Fãce mutãnen dãma.

(40) A cikin Aljanna suna tambayar jũna.

(41) Game da mãsu laifi.

(42) (Su ce musu) "Me ya shigar da ku a cikin Saƙar?"

(43) Suka ce: "Ba mu kasance munã a cikin mãsu salla ba."

(44) "Kuma ba mu kasance muna ciyar da matalautã ba."

(45) "Kuma mun kasance muna kũtsãwa tãre da mãsu kũtsãwa."

(46) "Mun kasance munã ƙaryata rãnar sãkamako."

(47) "Har gaskiya (wãto mutuwa) ta zo mana."

(48) Sabõda haka cẽton mãsu cẽto bã zai amfãne su ba.

(49) Haba! Me ya same su, suka zama mãsu bijirewa daga wa'azin gaskiya.

(50) Kamar dai sũ, jãkuna firgitattu ne.



74 - Suratu Al'mudathir  2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 52644
العمر : 72

74 - Suratu Al'mudathir  Empty
مُساهمةموضوع: رد: 74 - Suratu Al'mudathir    74 - Suratu Al'mudathir  Emptyالإثنين 19 سبتمبر 2022, 8:00 am


(51) Sun gudu daga zãki.

(52) A'aha! Kõwãne mutum daga cikinsu yanã son a zo masa da takardu (da sũnansa) ana wãtsãwa

(53) A'aha! Kai dai, bã su jin tsõron Lãhira.

(54) A'aha! Lalle ne, shi (Alƙur'ãni) tunãtarwa ce.

(55) Dõmin wanda ya so, ya tuna.

(56) Kuma bã zã su tuna ba fãce idan Allah Ya so, Shi ne Ya cancanta a bi Shi da taƙawa kuma Ya cancanta ga Ya yi gãfara.



74 - Suratu Al'mudathir  2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
 
74 - Suratu Al'mudathir
الرجوع الى أعلى الصفحة 
صفحة 1 من اصل 1
 مواضيع مماثلة
-
» 24 - Sûratu'n-Nûr
» 26 - Suratu Ach - Chu'ara
» 107 - Suratu Al - Ma'un
» 11 - Suratu Hud
» 13 - Suratu Al'ra'ad

صلاحيات هذا المنتدى:لاتستطيع الرد على المواضيع في هذا المنتدى
منتديات إنما المؤمنون إخوة (2024 - 2010) The Believers Are Brothers :: (English) :: The Holy Quran is translated :: Hausa-
انتقل الى: