62 - Suratu Al'Jumu'a
Da sunan Allah Mai rahama
(1) Abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin kasã sunã tasbĩhi ga Allah, Mamallaki, Mai tsarki' Mabuwãyi, Mai hikima.

(2) Shĩ ne wanda Ya aika, a cikin mabiya al'ãdu,* wani Manzo daga gare su yanã karanta ãyõyin Sa a kansu, kuma yanã tsarkake su, kuma yanã sanar da su littafin da hikimarsa kõ da yake sun kasance daga gabãninsa lalle sunã a cikin ɓata bayyanãnna.
* Lãrabawa sũ ne mabiya al'ãdu, watau ummiyyũn daga ummu, watau uwa watau kamar yadda uwãye suka haife su dõmin bã su da wani littãfi da suke bi sai al'ãdunsu da hukunce-hukuncen shaihunansu.

(3) Da waɗansu mutãne* daga gare su, ba su i da riskuwa da sũ ba, alhãli kuwa shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima.
* Su ne Ajamãwan da zã su musulunta su bi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Kõ kuwa duk wanda ya musulunta a bãyan sahabban Annabi. Wannan yanã nunã falalar sahabbai a kan waɗansunsu.

(4) Waccan wata falalar Allah ce Yanã bãyar da ita ga wanda Yake so. Kuma Allah ne Ma'abũcin dukan falala mai girma.

(5) Misãlin waɗanda aka ɗõra wa ɗaukar Attaura sa'an nan ba su ɗauke ta ba, kamar misãlin jãki ne Yanã ɗaukar littattafai. Tir da misãlin mutãnen* nan da suka ƙaryatã game da ãyõyin Allah! Kuma Allah bã Yã shiryar da mutãnẽ azzãlumai.
* Tir da wanda ya yi siffa da irin siffõfin Yahũdu daga Musulmi wajen ɗaukar karãtun Alƙur'ãni amma kuma bai yi aiki da shi ba. Yahaya bn Yamãni ya ce: "Sunã rubuta nadĩsi bã su fahimtarsa, kuma bã su kula da ma' anarsa." Watau sunã wahala wajen ɗaukar ilmin da aka ɗõra musu ɗaukarsa amma kuma bã su yin amfãni da shi a wajen aikinsu da mu'ãmalõlinsu.

(6) Ka ce: "Yã kũ waɗanda suka tũba (Yahũdu)! Idan kun riya cẽwa kũ ne zãɓaɓɓun Allah bã sauran mutanẽ ba, sai ku yi gũrin mutuwa* idan kun kasance mãsu gaskiya."
* Ba a sãduwa da Allah sai a bãyan mutuwa. Masõyi nã bũrin sãduwa da masõyinsa, kuma bã zai yi gudun sababin sãduwar ba.

(7) Kuma bã zã su yi gũrinta ba har abadã sabõda abin da hannãyen su suka gabãtar. Kuma Allah ne masani ga azzãlumai

(8) Ka ce "Lalle mutuwar nan da kuke gudũ daga gareta, to, lalle ita mai haɗuwa da ku ce sa'an nan kuma anã mayar da kũ zuwa ga masanin fake da bayyane, dõmin Ya bãku lãbãri game da abin da kuka kasance kunã aikatãwa."

(9) Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan anyi kirã zuwã ga salla a rãnar Jumu'a, sai ku yi aiki zuwa ga ambaton Allah, kuma ku bar* ciniki. Wancan ɗinku ne mafi alhẽri a gare ku idan kun kasance kunã sani.
* Ba a hana Musulmi aiki ba a kõwace rãna, sai dai an hana duk wanda Jumu'a ta lazimta a kansa da ya yi wani aiki wanda bã na tattalin salla ba a rãnar Jumma'a, a bãyan kiran salla. Anã nufi da kiran salla na biyu a bãyan limãmi ya zauna a kan mumbarinsa, dõmin wannan kiran aka sani azãmanin Annabi da Abubakar da Umar. Amma kira na farko, Usman bn Affãn ne ya fãra shi dõmin farkar da mutãne, a bãyan sun yi yawa kuma sun kama sana'õ'i. Kuma a bãyan an ƙãre salla, sai a wãtse zuwa ga ayyuka da neman abinci. Bã a tsayãwa yin wata nãfila a bãyan sallar Jumu'a, sai dai an so yin raka'a biyu a bãyan fita daga masallãci kamar yadda Annabi ke yi. A farko, anã yin huɗubar sallar Jumma'a a bãyan salla har a lõkacin da ãyarin Dihyatul Kalbi ya kõmo daga shãm (Syria) da abinci,ya sauka a Baƙĩ'a, suka buga ganga, sai Sahabbai suka fita dõmin neman sayen abincin a gabãnin a ƙãre huɗubar suka bar mutum gõma shã biyu tãre da Annabi. Sai aka mayar da huɗubar a gabãnin salla. Kuma an fahimci cewa anã yin huɗuba a tsaye. Kuma ba a kafa Jumu'a, sai a kafaffen gari, amma Jumu'a nã ƙulluwa da mutum gõma sha biyu da lĩman.

(10) Sa'an nan idan an ƙarẽ salla, Sai ku wãtsu a cikin ƙasã kuma ku nẽma daga falalar Allah, kuma ku ambaci sũnan Allah da yawa ɗammãninku, ku sãmi babban rabo.

(11) Kuma idan suka ga wani fatauci kõ kuma wani wasan shagala, sai su yi rũgũguwar fita zuwa gare su, kuma su bar ka kanã tsaye. Ka ce: "Abin da yake a wurin Allah ne mafi alhẽri daga fataucin, alhãli kuwa Allah ne Mafi alhẽrin mãsu arzũtãwa."