منتديات إنما المؤمنون إخوة (2024 - 2010) The Believers Are Brothers

(إسلامي.. ثقافي.. اجتماعي.. إعلامي.. علمي.. تاريخي.. دعوي.. تربوي.. طبي.. رياضي.. أدبي..)
 
الرئيسيةالأحداثأحدث الصورالتسجيل
(وما من كاتب إلا سيبلى ** ويبقى الدهر ما كتبت يداه) (فلا تكتب بكفك غير شيء ** يسرك في القيامة أن تراه)

IZHAR UL-HAQ

(Truth Revealed) By: Rahmatullah Kairanvi
قال الفيلسوف توماس كارليل في كتابه الأبطال عن رسول الله -صلى الله عليه وسلم-: "لقد أصبح من أكبر العار على أي فرد مُتمدين من أبناء هذا العصر؛ أن يُصْغِي إلى ما يظن من أنَّ دِينَ الإسلام كَذِبٌ، وأنَّ مُحَمَّداً -صلى الله عليه وسلم- خَدَّاعٌ مُزُوِّرٌ، وآنَ لنا أنْ نُحارب ما يُشَاعُ من مثل هذه الأقوال السَّخيفة المُخْجِلَةِ؛ فإنَّ الرِّسَالة التي أدَّاهَا ذلك الرَّسُولُ ما زالت السِّراج المُنير مُدَّةَ اثني عشر قرناً، لنحو مائتي مليون من الناس أمثالنا، خلقهم اللهُ الذي خلقنا، (وقت كتابة الفيلسوف توماس كارليل لهذا الكتاب)، إقرأ بقية كتاب الفيلسوف توماس كارليل عن سيدنا محمد -صلى الله عليه وسلم-، على هذا الرابط: محمد بن عبد الله -صلى الله عليه وسلم-.

يقول المستشرق الإسباني جان ليك في كتاب (العرب): "لا يمكن أن توصف حياة محمد بأحسن مما وصفها الله بقوله: (وَمَا أَرْسَلْنَاكَ إِلَّا رَحْمَةً لِّلْعَالَمِين) فكان محمدٌ رحمة حقيقية، وإني أصلي عليه بلهفة وشوق".
فَضَّلَ اللهُ مِصْرَ على سائر البُلدان، كما فَضَّلَ بعض الناس على بعض والأيام والليالي بعضها على بعض، والفضلُ على ضربين: في دِينٍ أو دُنْيَا، أو فيهما جميعاً، وقد فَضَّلَ اللهُ مِصْرَ وشَهِدَ لها في كتابهِ بالكَرَمِ وعِظَم المَنزلة وذَكَرَهَا باسمها وخَصَّهَا دُونَ غيرها، وكَرَّرَ ذِكْرَهَا، وأبَانَ فضلها في آياتٍ تُتْلَى من القرآن العظيم.
المهندس حسن فتحي فيلسوف العمارة ومهندس الفقراء: هو معماري مصري بارز، من مواليد مدينة الأسكندرية، وتخرَّجَ من المُهندس خانة بجامعة فؤاد الأول، اشْتُهِرَ بطرازهِ المعماري الفريد الذي استمَدَّ مَصَادِرَهُ مِنَ العِمَارَةِ الريفية النوبية المَبنية بالطوب اللبن، ومن البيوت والقصور بالقاهرة القديمة في العصرين المملوكي والعُثماني.
رُبَّ ضَارَّةٍ نَافِعَةٍ.. فوائدُ فيروس كورونا غير المتوقعة للبشرية أنَّه لم يكن يَخطرُ على بال أحَدِنَا منذ أن ظهر وباء فيروس كورونا المُستجد، أنْ يكونَ لهذه الجائحة فوائدُ وإيجابيات ملموسة أفادَت كوكب الأرض.. فكيف حدث ذلك؟!...
تخليص الإبريز في تلخيص باريز: هو الكتاب الذي ألّفَهُ الشيخ "رفاعة رافع الطهطاوي" رائد التنوير في العصر الحديث كما يُلَقَّب، ويُمَثِّلُ هذا الكتاب علامة بارزة من علامات التاريخ الثقافي المصري والعربي الحديث.
الشيخ علي الجرجاوي (رحمه الله) قَامَ برحلةٍ إلى اليابان العام 1906م لحُضُورِ مؤتمر الأديان بطوكيو، الذي دعا إليه الإمبراطور الياباني عُلَمَاءَ الأديان لعرض عقائد دينهم على الشعب الياباني، وقد أنفق على رحلته الشَّاقَّةِ من مَالِهِ الخاص، وكان رُكُوبُ البحر وسيلته؛ مِمَّا أتَاحَ لَهُ مُشَاهَدَةَ العَدِيدِ مِنَ المُدُنِ السَّاحِلِيَّةِ في أنحاء العالم، ويُعَدُّ أوَّلَ دَاعِيَةٍ للإسلام في بلاد اليابان في العصر الحديث.

أحْـلامٌ مِـنْ أبِـي (باراك أوباما) ***

 

 44 - Suratu Al'dukhan

اذهب الى الأسفل 
كاتب الموضوعرسالة
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 52644
العمر : 72

44 - Suratu Al'dukhan Empty
مُساهمةموضوع: 44 - Suratu Al'dukhan   44 - Suratu Al'dukhan Emptyالأحد 18 سبتمبر 2022, 10:19 pm

44 - Suratu Al'dukhan
Da sunan Allah Mai rahama
(1) Ḥ. M̃.

(2) Inã rantsuwa da Littãfi Mabayyani.

(3) Lalle ne, Mũ, Muka saukar da shi a cikin wani dare mai albarka. Lalle Mũ' Mun kasance Mãsu yin gargaɗi.

(4) A cikinsa (shi daren) ake rarrabe kõwane umurui bayyananne.

(5) Umurni na daga wurin Mu. Lalle Mũ ne Muka kasance Mãsu aikãwã.

(6) Sabõda rahama daga Ubangijinka. Lalle Shĩ, Shi ne Mai ji, Mãsani.

(7) (Shĩ ne) Ubangijin sammai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu yaƙĩni (za ku gãne haka).

(8) Babu abin bautãwa fãce Shi. Yana rãyarwa Kuma Yana kashẽwa. (Shi ne) Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko.

(9) A'a sũ, sunã wãsã a cikin shakka.

(10) Sabõda haka, ka dakata rãnar da sama zã tã zo da hayãƙi bayyananne.

(11) Yanã rufe mutãne. Wannan wata azãba ce mai raɗaɗi.

(12) Ya Ubangijinmu! Ka kuranye mana azãba. Lalle Mũ, mãsu ĩmãni ne.

(13) Inã tunãwa take a gare su, alhãli kuwa, haƙĩƙa, Manzo mai bayyanãwa Ya je musu (da gargaɗin saukar azãbar, ba su karɓa ba)?

(14) Sa'an nan suka jũya baya daga gare shi, Kuma suka ce: "Wanda ake gayãwa* ne, mahaukaci."
* Sunã nufin waɗansu mutãne ne ke gaya wa Annabi Alƙur'ãni, kõ kuma daga alãma watau wai Annabi taɓaɓɓe ne, mahaukaci. Taɓaɓɓe da mahaukaci duka ma'anarsu guda ce, watau marashin hankali,wanda aka yi wa alãma da rashin hankali.

(15) Lalle Mũ, Mãsu kuranyẽwar azãba ne, a ɗan lõkaci kaɗan, lalle kũ, mãsu kõmãwa ne (ga laifin).

(16) Rãnar da Muke damƙa, damƙa mafi girma, lalle ne Mũ mãsu azãbar rãmuwa ne.

(17) Kuma lalle ne haƙĩƙa a gabaninsu, Mun fitini mutãnen Fir'auna, kuma wani Manzo karĩmi ya jẽ musu.

(18) (Mazon ya ce): "Ku kãwo mini (ĩmãninku) ya bayin Allah! Lalle ni, Manzo ne amintacce zuwa gare ku."

(19) "Kuma kada ku nẽmi ɗaukaka a kan Allah. Lalle nĩ mai zo muku ne da dalĩli bayyananne."

(20) "Kuma lalle nĩ na nẽmi tsari da Ubangijĩna, kuma Ubangijinku, dõmin kada ku jẽfe ni."

(21) "Kuma idan ba ku yi ĩmãni sabõda nĩ ba, to, ku nĩsance ni."

(22) Sai ya kirayi Ubangjinsa cẽwa waɗannan mutãnene mãsu laifi.

(23) (Allah Ya ce): "To, ka yi tafiyar dare da bayiNa, da dare. Lalle kũ, waɗanda ake bĩ ne (dõmin a kãma ku.)"

(24) "Kuma ka bar tẽku rarrabe. Lalle sũ, runduna ce abar nutsarwa."

(25) Da yawa suka bar gõnaki da marẽmari.



44 - Suratu Al'dukhan 2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 52644
العمر : 72

44 - Suratu Al'dukhan Empty
مُساهمةموضوع: رد: 44 - Suratu Al'dukhan   44 - Suratu Al'dukhan Emptyالأحد 18 سبتمبر 2022, 10:19 pm


(26) Da shuke-shuke da matsayi mai kyau.

(27) Da wata ni'ima da suka kasance a cikinta sunã mãsu hutu.

(28) Kamar haka! Kuma Muka gãdar da ita ga waɗansu mutãne na dabam.

(29) Sa'an nan samã da ƙasã ba su yi kũka *a kansu ba, Kuma ba su kasance waɗanda ake yi wa jinkiri ba.
* Watau sama da ƙasa ba su girgizu ba sabõda halaka su da aka yi kamar ba a yi, kõme ba.

(30) Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun tsĩrar da Banĩ Isrã'ĩla daga, azãba mai wulãkantãwa.

(31) Daga Fir'auna. Lalle shi, ya kasance maɗaukaki daga cikin mãsu ɓarna.

(32) Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun zãɓe su sabõda wani ilmi (na Taurata) a kan mutãne.

(33) Kuma Muka bã su, daga ãyõyin mu'ujizõji, abin da yake a cikinsa, akwai ni'ima bayyananna*
* An bai wa Banĩ lsrã'ĩla ni'imar ilmi na Taurãta, an ɗaukaka su, sabõda aiki da ilmin, a kan sauran mutãnen zãmaninsu, kuma aka bã su ãyõyin mu'ujiza kamar tsãge teku da mannu da salwa da sauransu, amma kuma dukkan waɗannan ni'imomĩn sai da suka gushe a lõkacin da suka sãɓawa umurnin Allah, sai kuma ƙasƙanci ya maye musu daga bãya. Wannan kuma wa'azi ne ga Musulmi waɗanda Allah Ya ɗaukaka su da Alƙur'ãni a kan sauran mutãne, idan sun kauce masa zã su wulãkantu.

(34) Lalle waɗannan mutãne*, haƙĩka, sunã cẽwa,
* Anã nufin mutãnen zãmanin Annabi Muhammadu, tsĩra da aminci su tabbata a gare shi, waɗanda ake kiran su zuwa ga Musulunci.

(35) "Babu wani abu sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba."

(36) "Sai ku zo da ubanninmu, idan kun kasance mãsu gaskiya."

(37) shin, sũ ne mafĩfĩta kõ kuwa mutãnen Tubba'u, kuma da waɗanda ke a gabãninsu? Mun halaka su, lalle sũ, sun kasance mãsu laifi.

(38) Kuma ba Mu halitta slmmai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu ba, alhãli kuwa Munã mãsu wãsã.

(39) Ba Mu halitta su ba fãce da manufa ta gaskiya, kuma amma mafi yawansu, ba su sani ba.

(40) Lalle rãnar rarrabẽwa, ita ce lõkacin wa'adinsu gabã ɗaya.

(41) Rãnar da wani zumu bã ya amfãnin wani zumu da kõme kuma ba su zama anã taimakon su ba.

(42) fãce wanda Allah Ya yi wa rahama. Lalle Shi (Allah), shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.

(43) Lalle itãciyar zaƙƙũm (ɗanyen wutã),

(44) Ita ce abincin mai laifi.

(45) Kamar narkakken kwalta yanã tafasa a cikin cikunna.

(46) Kamar tafasar ruwan zãfi.

(47) (A cẽ wa malã'ikun wutã), "Ku kãmã shi, sa'an nan ku fizge shi zuwa ga tsakiyar Jahĩm."

(48) "Sa'an nan ku zuba, a kansa, daga azãbar ruwan zãfi."

(49) (A ce masã), "Ka ɗanɗana! Lalle kai, kai ne mabuwãyi mai girma!"

(50) "Lalle wannan, shi ne abin da kuka kasance kunã shakka game da shi."



44 - Suratu Al'dukhan 2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 52644
العمر : 72

44 - Suratu Al'dukhan Empty
مُساهمةموضوع: رد: 44 - Suratu Al'dukhan   44 - Suratu Al'dukhan Emptyالأحد 18 سبتمبر 2022, 10:20 pm


(51) Lalle mãsu taƙawa sunã cikin matsayi amintacce.

(52) A cikin gidãjen Aljanna da marẽmari.

(53) Sunã tufanta daga tufãfin alharĩni raƙĩƙi, da mai kauri, sunã mãsu zaman fuskantar jũna.

(54) Kamar haka, kuma Mun aurar da su da mãtã mãsu kyawun idãnu, mãsu girmansu.

(55) Sunã kira, a cikinsu (gidẽjen) ga dukan 'ya'yan itãcen marmari, sunã amintattu (daga dukan abin tsõro).

(56) Bã su ɗanɗanar mutuwa, a cikinsu, fãce mutuwar farko, kuma (Allah), Ya tsare musu azãbar Jahĩm.

(57) Sabõda falala daga Ubangijinka. Wancan shi ne babban rabo, mai girma.

(58) Dõmin haka kawai Muka sauƙaƙar da shi (Alƙur'ãni) da harshenka, tsammãninsu, su riƙa tunãwa.

(59) Sai ka yi jira. Lalle sũ, mãsu jira ne.*

* Mãsu jira ne ga abin da zai sãme su idan ba su yi ĩmãni ba, watau ni'imar da aka ba su zã ta gushe ke nan dõmin ba su aiwatar da ita ba a kan umuruin Allah.



44 - Suratu Al'dukhan 2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
 
44 - Suratu Al'dukhan
الرجوع الى أعلى الصفحة 
صفحة 1 من اصل 1
 مواضيع مماثلة
-
» 24 - Sûratu'n-Nûr
» 26 - Suratu Ach - Chu'ara
» 107 - Suratu Al - Ma'un
» 11 - Suratu Hud
» 13 - Suratu Al'ra'ad

صلاحيات هذا المنتدى:لاتستطيع الرد على المواضيع في هذا المنتدى
منتديات إنما المؤمنون إخوة (2024 - 2010) The Believers Are Brothers :: (English) :: The Holy Quran is translated :: Hausa-
انتقل الى: