منتديات إنما المؤمنون إخوة (2024 - 2010) The Believers Are Brothers

(إسلامي.. ثقافي.. اجتماعي.. إعلامي.. علمي.. تاريخي.. دعوي.. تربوي.. طبي.. رياضي.. أدبي..)
 
الرئيسيةالأحداثأحدث الصورالتسجيل
(وما من كاتب إلا سيبلى ** ويبقى الدهر ما كتبت يداه) (فلا تكتب بكفك غير شيء ** يسرك في القيامة أن تراه)

soon after IZHAR UL-HAQ (Truth Revealed) By: Rahmatullah Kairanvi
قال الفيلسوف توماس كارليل في كتابه الأبطال عن رسول الله -صلى الله عليه وسلم-: "لقد أصبح من أكبر العار على أي فرد مُتمدين من أبناء هذا العصر؛ أن يُصْغِي إلى ما يظن من أنَّ دِينَ الإسلام كَذِبٌ، وأنَّ مُحَمَّداً -صلى الله عليه وسلم- خَدَّاعٌ مُزُوِّرٌ، وآنَ لنا أنْ نُحارب ما يُشَاعُ من مثل هذه الأقوال السَّخيفة المُخْجِلَةِ؛ فإنَّ الرِّسَالة التي أدَّاهَا ذلك الرَّسُولُ ما زالت السِّراج المُنير مُدَّةَ اثني عشر قرناً، لنحو مائتي مليون من الناس أمثالنا، خلقهم اللهُ الذي خلقنا، (وقت كتابة الفيلسوف توماس كارليل لهذا الكتاب)، إقرأ بقية كتاب الفيلسوف توماس كارليل عن سيدنا محمد -صلى الله عليه وسلم-، على هذا الرابط: محمد بن عبد الله -صلى الله عليه وسلم-.

يقول المستشرق الإسباني جان ليك في كتاب (العرب): "لا يمكن أن توصف حياة محمد بأحسن مما وصفها الله بقوله: (وَمَا أَرْسَلْنَاكَ إِلَّا رَحْمَةً لِّلْعَالَمِين) فكان محمدٌ رحمة حقيقية، وإني أصلي عليه بلهفة وشوق".
فَضَّلَ اللهُ مِصْرَ على سائر البُلدان، كما فَضَّلَ بعض الناس على بعض والأيام والليالي بعضها على بعض، والفضلُ على ضربين: في دِينٍ أو دُنْيَا، أو فيهما جميعاً، وقد فَضَّلَ اللهُ مِصْرَ وشَهِدَ لها في كتابهِ بالكَرَمِ وعِظَم المَنزلة وذَكَرَهَا باسمها وخَصَّهَا دُونَ غيرها، وكَرَّرَ ذِكْرَهَا، وأبَانَ فضلها في آياتٍ تُتْلَى من القرآن العظيم.
(وما من كاتب إلا سيبلى ** ويبقى الدهر ما كتبت يداه) (فلا تكتب بكفك غير شيء ** يسرك في القيامة أن تراه)

المهندس حسن فتحي فيلسوف العمارة ومهندس الفقراء: هو معماري مصري بارز، من مواليد مدينة الأسكندرية، وتخرَّجَ من المُهندس خانة بجامعة فؤاد الأول، اشْتُهِرَ بطرازهِ المعماري الفريد الذي استمَدَّ مَصَادِرَهُ مِنَ العِمَارَةِ الريفية النوبية المَبنية بالطوب اللبن، ومن البيوت والقصور بالقاهرة القديمة في العصرين المملوكي والعُثماني.
رُبَّ ضَارَّةٍ نَافِعَةٍ.. فوائدُ فيروس كورونا غير المتوقعة للبشرية أنَّه لم يكن يَخطرُ على بال أحَدِنَا منذ أن ظهر وباء فيروس كورونا المُستجد، أنْ يكونَ لهذه الجائحة فوائدُ وإيجابيات ملموسة أفادَت كوكب الأرض.. فكيف حدث ذلك؟!...
تخليص الإبريز في تلخيص باريز: هو الكتاب الذي ألّفَهُ الشيخ "رفاعة رافع الطهطاوي" رائد التنوير في العصر الحديث كما يُلَقَّب، ويُمَثِّلُ هذا الكتاب علامة بارزة من علامات التاريخ الثقافي المصري والعربي الحديث.
الشيخ علي الجرجاوي (رحمه الله) قَامَ برحلةٍ إلى اليابان العام 1906م لحُضُورِ مؤتمر الأديان بطوكيو، الذي دعا إليه الإمبراطور الياباني عُلَمَاءَ الأديان لعرض عقائد دينهم على الشعب الياباني، وقد أنفق على رحلته الشَّاقَّةِ من مَالِهِ الخاص، وكان رُكُوبُ البحر وسيلته؛ مِمَّا أتَاحَ لَهُ مُشَاهَدَةَ العَدِيدِ مِنَ المُدُنِ السَّاحِلِيَّةِ في أنحاء العالم، ويُعَدُّ أوَّلَ دَاعِيَةٍ للإسلام في بلاد اليابان في العصر الحديث.


 

 29 - Suratu Al'ankabout

اذهب الى الأسفل 
كاتب الموضوعرسالة
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 48824
العمر : 71

29 - Suratu Al'ankabout Empty
مُساهمةموضوع: 29 - Suratu Al'ankabout   29 - Suratu Al'ankabout Emptyالخميس 15 سبتمبر 2022, 11:33 pm

29 - Suratu Al'ankabout
Da sunan Allah Mai rahama
(1) A. L̃. M̃.

(2) Ashe, mutãne sun yi zaton a bar su su ce: "Mun yi ĩmãni," alhãli kuwa bã zã a Jarrabe su ba?"

(3) Kuma lalle Mun fitini waɗanda ke a gabãninsu, dõmin lalle Allah Ya san waɗanda suka yi gaskiya, kuma lalle Ya san maƙaryata.

(4) Kõ waɗanda ke aikata miyãgun ayyuka sun yi zaton su tsẽre Mana? Abin da suke hukuntãwa ya mũnana.

(5) Wanda ya kasance yanã fãtan gamuwa da Alah to lalle ajalin Allah mai zuwa ne, kuma (Allah) Shĩ ne Mai ji, Masani.

(6) Kuma wanda ya yi jihãdi, to, yanã yin jihãdin ne dõmin kansa. lalle Allah haƙĩƙa waɗatacce ne daga barin tãlikai.

(7) Kuma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, lalle Munã kankare musu miyãgun ayyukansu, kuma lalle Munã sãka musu da mafi kyaun abin da suka kasance sunã aikatãwa.

(8) Kuma Mun yi wa mutum wasiyyar kyautatãwa ga uwayensa, kuma idan sun tsananta maka dõmin ka yi shirki da Ni game da abin da bã ka da ilmi gare shi, to, kada ka yi musu ɗã'ã. Zuwa gare Ni makõmarku take sa'an nan In bã ku lãbari ga abin da kuka kasance kunã aikatãwa.

(9) Kuma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, lalle Munã shigar da su a cikin mutãnen kirki.

(10) Kuma daga cikin mutãne akwai mai cẽwa, 'Mun yi ĩmãni da Allah" sa'an nan idan aka cũce shi wajen aikin Allah, sai ya sanya fitinar mutãne kamar azãbar Allah kuma lalle idan taimakon Ubangijinka ya zo, haƙĩƙa, ya kan ce: "Lalle mũ mun kasance tãre da ku." shin, Allah bai zama Mafi sani ba ga abin da ke a cikin ƙirãzan halittun Sa?

(11) Kuma lalle Allah na sanin waɗanda suka yi ĩmãni kuma lalle Yanã sanin munafukai.

(12) Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce wa waɗanda suka yi ĩmãni, "Ku bi hanyarmu, kuma Mu ɗauki laifuffukanku," alhãli kõwa ba su zamo mãsu ɗauka da a kõme ba daga laifuffukansu. Lalle sũ maƙaryata ne.

(13) Kuma lalle sunã ɗaukar kãyan nauyinsu da waɗansu nauyãyan kãya tãre da kãyan nauyinsu, kuma lalle zã a tambaye su a Rãnar ¡iyama game da abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa na ƙarya.

(14) Kuma lalle Mun aika Nũhu zuwa ga mutãnensa, sai ya zauna a cikinsu shẽkara dubu fãce shẽkara hamsin, sa'an nan cikowar (¦ũfãna) ta kãmã su, alhãli kuwa sũ ne mãsu zãlunci.

(15) Sa'an nan Muka tsĩrar da shi da mutãnen jirgin, kuma Muka sanya jirgin ya zama wata ãyã ga tãlikai.

(16) Da Ibrãhĩm a lõkacin da ya ce wa mutãnensa, "Ku bautã wa Allah ku bĩ Shi da taƙawa. Wannan Shĩ ne alhẽri a gare ku idan kun kasance kunã sani.

(17) "Abin da dai kuke bautãwa, baiein Allah, gumaka ne, kuma kun ƙirƙira ƙarya. Lalle waɗannan da kuke bauta wa baicin Allah, bã su mallakã muku arziki. Sabõda haka ku nẽmi arziki a wurin Allah kawai, kuma ku bauta Masa, kuma ku yi gõdiya zuwa gare Shi. Zuwa gare Shi ake mayar da ku.

(18) "Kuma idan kun ƙaryata, to, lalle waɗansu al'ummõmi a gabãninku sun ƙaryata, kuma bãbu abin da ke kan Manzo, fãce ayar da manzanci, iyarwa bayyananna."

(19) Shin, ba su* ga yadda Allah ke fãra yin halitta ba, sa'an nan kuma Ya mayar da ita? Lalle wannan abu ne mai sauƙi ga Allah.
* Ga wata ƙirã'a, ba ku ga da Iamĩrin abõkan magana waɗanda Ibrahĩm ke yi wa magana. A kan wannan ƙirã'a, maganar Ibrãhĩm ba ta yanke ba har ƙarshen ãya ta 23

(20) Ka ce: "Ku yi tafiya cikin ƙasa, sa'an nan ku dũba yadda (Allah) Ya fãra yin halitta, sa'an nan kuma Allah Yanã ƙãga wata halittar mayarwa. Lalle Allah Mai ikon yi ne a kan kõme.

(21) "Yanã azabta wanda Ya so, kuma Yanã jin ƙan wanda Ya so. Kuma zuwa gare shi ake jũyaku."

(22) "Kuma ba ku zamo mãsu buwãya ba a cikin ƙasã, kuma haka a cikin sama kuma bã ku da wani majiɓinci wanda ba Allah ba, kuma ha ku da wani mataimaki."

(23) Kuma waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Allah da gamuwa da shi, waɗannan sun yanke ƙauna daga rahamaTa kuma waɗannan sunã da wata azãba mai raɗaɗi.

(24) Sa'an nan bãbu abin da ya kasance jawãbin mutãnensa (Ibrãhĩm) fãce dai suka ce: "Ku kashe shi kõ, ku ƙõnã shi," Sai Allah Ya tsĩrar da shi daga wutã. Lallea cikin wannan akwai ayõyi ga mutãnen da ke yin ĩmãni.

(25) Kuma Ibrahĩm ya ce "Bãbu abin da kuka yi sai dai kub bar Allah kun riƙi gumãka sabõda sõyayyar tsakãninku a cikin rãyuwar dũniya, a'an nan a Rãnar ¡iyãma sãshinku zai kãfirce wa sãshi, kuma makõmarku ita ce wutã kuma bã ku da waɗansu mataimaka."



29 - Suratu Al'ankabout 2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 48824
العمر : 71

29 - Suratu Al'ankabout Empty
مُساهمةموضوع: رد: 29 - Suratu Al'ankabout   29 - Suratu Al'ankabout Emptyالخميس 15 سبتمبر 2022, 11:34 pm


(26) Sai Lũɗu ya yi ĩmãni da shi. Kuma Ibrãhĩm ya ce: "Lallenĩ mai ƙaura ne zuwa ga Ubangijina. Lalle Shĩ Shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima."

(27) Kuma Muka bã shi Ishãƙa da Ya'aƙũba, kuma Muka sanya Annabci da littãfi a cikin zuriyarsa. Kuma Mun bã shi sakamakonsa a dũniya, kuma lalle shĩ a Lãhira, tabbas, yanã a cikin sãlihai.

(28) Da Lũɗu, a lõkacin daya ce wa mutãnensa, "Lalle kũ, haƙĩƙa kunã jẽ wa alfãsha wadda wani mahalũƙi daga cikin dũniya bai riga ku gare ta ba.

(29) "Ashe, lalle kũ kunã je wa maza, kuma ku yi fashin hanya kuma ku je, a cikin majalisarku da abin da bã shi da kyau? To, jawãbin mutãnensa bai kasance ba fãce dai sun ce: 'Ka zo mana da azãbar Allah, idan ka kasance daga mãsu gaskiya.'"

(30) Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka taimake ni a kan mutãnen nan maɓarnata."

(31) Kuma a lõkacin da Manzannin Mu suka jẽ wa Ibrãhĩm da bushãra suka ce: "Lalle mu mãsu halaka mutãnen, wannan alƙarya ne. Lalle mutãnenta sun kasance mãsu zãlunci."

(32) Ya ce: "Lalle akwai Lũɗu a cikinta!" Suka ce: "Mũ ne mafiya sani ga waɗanda suke a cikinta, lalle munã tsĩrar da shi da mutãnensa, fãce fa mãtarsa ta kasance a cikin mãsu wanzuwa."

(33) Kuma a lõkacin da Manzannin Mu suka je wa Lũɗu ya ɓãta rai sabõda su, kuma yã ƙuntata ga kirji sabõda su. Kuma suka ce: "Kada ka ji tsõro kuma kada ka yi baƙin ciki lalle mũ mãsu tsĩrar da kai ne da iyãlanka, fãce dai matarka ta kasance daga mãsu wanzuwa.

(34) "Lalle mũ, mãsu saukar da azãba ne daga sama a kan mutãnen wannan alƙarya sabõda abin da suka kasance sunã yi na fãsiƙanci."

(35) Kuma lalle Mun bar wata ãyã bayyananna daga gare ta ga mutãne mãsu hankalta.

(36) Kuma zuwa ga Madyana, Mun aika ɗan'uwansu shu'aibu, sai ya ce: "Ya mutãnena! Ku bauta wa Allah kuma ku yi fatan (rahamar) Rãnar Lãhira, kuma kada ku yi ɓarna a cikin ƙasã, alhãli kuwa kunã mãsu lãlãtarwa."

(37) Sai suka ƙaryata shi, sabõda haka tsãwa ta kãmã su, dõmin haka suka wãyi gari sunã guggurfãne.

(38) Da Ãdawa da Samũdãwa alhãli kuwa lalle alãmun azãba sun bayyana a gare su daga gidãjensu kuma Shaiɗan ya ƙawãta musu ayyukansu, sabõda haka ya kange su daga hanyar Allah, kuma sun kasance mãsu basĩra!

(39) Kuma ¡ãrũna da Fir'auna da Hãmãna, kuma lalle Mũsaya je musu da hujjõji, sai suka yi girman kai a cikin ƙasã kuma ba su kasance mãsu tsẽrẽwa ba.

(40) Sabõda haka kõwanensu Mun kama shi da laifinsa. Watau daga cikinsu akwai wanda Muka aika iskar tsakuwa a kansa kuma daga cikinsu akwai wanda tsãwa ta kãmã, kuma daga cikinsu akwai wanda Muka birkice ƙasã da shi kuma daga cikinsu akwai wanda Muka nutsar. Bã ya yiwuwa ga Allah Ya zãlunce su, amma sun kasance kansu suke zãlunta.

(41) Misãlin waɗanda suka riƙi waɗansu masõya waɗanda bã Allah ba, kamar misãlin gizõgizo ne wanda ya riƙi wani ɗan gida, alhãli kuwa lalle mafi raunin gidãje, shĩ ne gidan gizogizo, dã sun kasance sunã sane.

(42) Lalle Allah Yanã sane da abin da suke kira wanda bã Shi ba na wani abu duka kuma shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima.

(43) Kuma waɗancan misãlan Munã bayyana su ga mutãne kuma bãbu mai hankalta da su sai mãsu ilmi.

(44) Allah Ya halitta sammai da ƙasa da gaskiya. Lalle cikin wancan akwai ãyã ga mũminai.

(45) Ka karanta abin da ake yin wahayi zuwa gare ka daga Littãfi, kuma ka tsayar da salla. Lalle salla tanã hanãwa daga alfãsha da abni ƙyãma, kuma lalle ambaton Allah yafi girma, kuma Allah Yanã sane da abin da kuke aikatãwa.

(46) Kada ku yi jayayya da mazowa Littãfi sai fa da magana wadda ta fi kyau, sai fa waɗanda suka yi zãlunci daga gare su, kuma ku ce, "Mun yi ĩmãni da abin da aka saukar a gare mu kuma aka saukar a gare ku, kuma Abin bautãwarmu da Abin bautãwarku Guda ne, kama mũ mãsu sallamãwa ne a gare shi."

(47) Kuma kamar haka Muka saukar da Littafi a gare ka, to, waɗannan da Muka bai wa Littãfi sanã ĩmãni da shi, daga cikin wãɗannan akwai mai ĩmãni da shi, kuma bãbu mai musun ãyõyin Mu, fãce kãfirai.

(48) Kuma ba ka kasance kana karãtun wani littãfi ba a gabãninsa, kuma bã ka rubũtunsa da dãmanka dã haka yã auku, dã mãsu ɓarnã sun yi shakka.

(49) Ã'a, shĩ ãyõyi ne bayyanannu a cikin ƙirãzan waɗanda aka bai wa ilmi. Kuma bãbu mai musun ãyõyin Mu fãce azzãlumai.

(50) Kuma suka ce: "Don me ba a saukar masa da ãyõi ba daga Ubangijinsa? "Ka ce: "Su ãyõyi a wurin Allah kawai suke, kuma lalle ni mai gargaɗi kawai ne, mai bayyanãwa."



29 - Suratu Al'ankabout 2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 48824
العمر : 71

29 - Suratu Al'ankabout Empty
مُساهمةموضوع: رد: 29 - Suratu Al'ankabout   29 - Suratu Al'ankabout Emptyالخميس 15 سبتمبر 2022, 11:34 pm


(51) Shin bai ishe su ba cẽwa lalle Mũ, Mun saukar da Littãfin akanka, anã karanta shi a kansu? Lalle a cikin wancan haƙĩƙa akwai rahama da tunãtawa ga mutanen da ke yin ĩmãni.

(52) Ka ce: "Allah Yã isa shaida a tsakãnĩna da tsakãnĩnku Yanã sane da abin da ke a cikin sammai da ƙasã, kuma waɗanda suka yi ĩmãni da ɗarya kuma suka kãfirta da Allah, waɗannan sũ nemãsu hasãra."

(53) Kuma suna nẽman ka da gaggauta azãba, to, bã dõmin ajali ƙayyadadde ba, dã azãba ta jẽ musu kuma lalle dã tanã iske su bisa ia abke, alhãli kuwa sũ ba su sani ba.

(54) Sunã nẽman ka da gaggauta azãba, kuma lalle Jahannama, tabbas, mai kẽwayewa ce gakãfirai.

(55) Rãnar da azãba ke rufe su daga samansu da kuma ƙasan ƙafafunsu kuma Ya* ce: "Ku ɗanɗani abin da kuka kasance kunã aikatãwa."
* Ga wata ruwãyar "Mu" matsayin "Ya" watau Malã'ika waki1in azãbarsu.

(56) Yã bãyiNa, waɗanda suka yi ĩmãni! Lalle fa ƙasãTa mai yalwã* ce, sabãda haka ku bauta Mini.
* Tun da ƙasa nã da yalwã, sai mutum ya yi hijira zuwa wurin da yake mai sauƙi a gareshi, ya bauta wa Allah da sauƙi, idan garinsu ya buwãye shi.

(57) Kõwane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne, sa'an nan zuwa gare Mu ake mayar da ku.

(58) Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, lalle zã Mu zaunar da su daga cikin Aljanna a gidãjen bẽne, ƙoramu nã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwama a cikinsu. To, madalla da sakamakon mãsu aikin ƙwarai.

(59) Waɗanda suka yi haƙuri, kuma sunã dõgara ga Ubangijinsu kawai.

(60) Kuma da yawa* dabba wadda bã ta ɗaukar abincinta Allah Yanã ciyar da ita tãre da ku, kuma Shĩ ne Mai ji, Mai ilmi.
* Sabõda haka tunãnin abinci kada ya hana ku yin hijira zuwa wurin yardar Allah, Mai ciyar da dabbõbin da bã su tattalin abincinsu.

(61) Lalle idan ka tambaye su: "Wãne ne ya halitta sammai da ƙasã kuma ya hõre rãnã da watã?" Lalle sunã cẽwa Allah ne. TO, yãya ake karkatar da su*?
* Yãya ake karkatar da su daga hijira dõmin tsõron yankewar abinci, alhãli kuwa sun tafi wurin yardar wanda Ya halicci sammai da ƙasã? Yin hijira yanã a cikin jarrabãwar Allah ga Musulmi.

(62) Alah ne ke shimfiɗa arziki ga wanda Yake so daga cikin bãyinsa kuma Yanã ƙuntãtãwa ga (wanda, Yake so). Lalle Allah, Masani ne ga dukan kõme.

(63) Kuma lalle idan ka tambaye su. "Wãne ne ya saukar da ruwa daga sama, har ya rãyar da ƙasã game da shi a bãyan mutuwarta?" Lalle sunã cẽwa, "Allah ne." Ka ce: "Gõdiya tã tabbata ga Allah." Ã'a, mafi yawansu bã su hankalta.

(64) Kuma wannan rãyuwa ta dũniya ba ta zamo ba, fãce abar shagala da wãsã kuma lalle Lãhira tabbas, ita ce rãyuwa, dã sun kasance sunã sani.

(65) To, a lõkacin da suka shiga cikin jirgin ruwa, sun kirãyi Allah sunã mãsu tsarkake addini a gare shi, to, a lõkacin da Ya tsĩrar da su zuwa ga tudun ƙasã, sai gã su sunã shirki.

(66) Dõmin su kãfirce wa abin da Muka bã su kuma dõmin su ji dãɗi sa'an nan kuma zã su sani.

(67) Shin, ba su ga cẽwa, lalle Mun sanya Hurumi amintacce ba alhãli kuwa anã fisge mutãne a gẽfensu? Shin, da ɓãtaccen abu suke ĩmãni kuma da ni'imarAllah suka kãfirta?

(68) Kuma wãne ne ya fi zãlunci bisa ga wanda ya ƙirƙira ƙarya ya jingina ta ga Allah, kõ kuma ya ƙaryata gaskiya a lõkacin da ta je masa? Ashe a cikin Jahannama bãbu mazauna ga kãfirai?

(69) Kuma wadannan da suka yi ƙõƙari ga nẽman yardarMu, lalle Munã shiryar da su ga hanyõyinMu, kuma lalle Allah, tabbas, Yanã tãre da mãsu kyautatãwa (ga addĩninsu).



29 - Suratu Al'ankabout 2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
 
29 - Suratu Al'ankabout
الرجوع الى أعلى الصفحة 
صفحة 1 من اصل 1
 مواضيع مماثلة
-
» 30 - Suratu Ar'rum
» 5 - Suratu Al'ma'ida
» 95 - Suratu At'tín
» 30 - Sûratu'r-Rûm
» 114 - Suratu Al'nas

صلاحيات هذا المنتدى:لاتستطيع الرد على المواضيع في هذا المنتدى
منتديات إنما المؤمنون إخوة (2024 - 2010) The Believers Are Brothers :: (English) :: Group Forums No. 14 :: The Holy Quran is translated :: Hausa-
انتقل الى: