أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn مؤسس ومدير المنتدى
عدد المساهمات : 52644 العمر : 72
| موضوع: 87 - Suratu Al'a'ala الإثنين 19 سبتمبر 2022, 4:31 pm | |
| 87 - Suratu Al'a'ala Da sunan Allah Mai rahama (1) Ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mafi ɗaukaka.
(2) Wanda Yã yi halitta sa'an nan Ya daidaita abin halittar.
(3) Kuma Wanda Ya ƙaddara (abin da Ya so) sannan Ya shiryar, (da mutum ga hanyar alhẽri da ta sharri).
(4) Kuma Wanda Ya fitar da makiyãyã.
(5) Sa'an nan Ya mayar da ita ƙeƙasassa, baƙa.
(6) Za mu karantar da kai (Alƙur'ãni) sabõda haka bã zã ka mantã (shi) ba.
(7) Fãce abin da Allah Ya so, lalle ne Shi (Allah) Ya san bayyane da abin da yake bõye.
(8) Kuma za Mu sauƙaƙe maka (al'amari) zuwa ga (Shari'a) mai sauƙi.
(9) Sabõda baka, ka tunãtar, idan tunatarwa zã ta yi amfãni.
(10) Wanda yake tsõron (Allah) Zai tuna.
(11) Kuma shaƙiyyi, zai nisanceta,
(12) Wanda zai shiga wutar da tã fi girma.
(13) Sa'an nan bã zai mutu ba a cikinta, kuma bã zai rãyu ba.
(14) Lalle ne wanda ya tsarkaka (da ĩmãni) yã sãmu babban rabo.
(15) Kuma ya ambaci sũnan* Ubangijinsa, sa'an nan yã yi salla. * Ya ambaci sũnan Allah ga ayyukansa duka, ya yi sallolin nan biyar da sauran.
(16) Ba haka ba! Kunã zãɓin rãyuwa ta kusa dũniya.* * Rayuwa iri biyu ce, ta dũniya da ta Lãhira.
(17) Alhãli Lãhira ita ce mafi alheri kuma mafi wanzuwa.
(18) Lalle ne, wannan* yanã a cikin littafan farko. * Kamanta rãyuwar ciyãwa da rãyar da ummiyyi da ilmi bãbu mantuwa, da rãyar da mãtattu cikin sa'ãda ko cikin shaƙãwa yana cikin litaffan farko.
(19) Littaffan Ibrãhĩm da Mũsã. |
|