85 - Suratu Al'burouj
Da sunan Allah Mai rahama
(1) Inã rantsuwa da sama mai taurãrin lissafin shekara.

(2) Da yinin da aka yi alkawarin zuwansa,*
* Rãnar Ƙiyãma.

(3) Da yini mai shaidu, da yini da ake halarta* a cikinsa
* Rãnar Arafa.

(4) An la'ani mutãnen rãmi.*
* Mutãnen Najiran ne suka yi rãmi suka hũra wuta a ciki, dõmin su ƙõne wanda yã yi ĩmãni da addinin Masĩh Ĩsa dõmin su hana yãɗuwarsa. Suka umurci kõwane Musulmi ya jefa kansa a ciki, su kuma suna zazzaune suna kallo.

(5) Wato wuta wadda aka hura.

(6) A lõkacin da suke a kan (gefen) ta a zazzaune.

(7) Alhãli sũ, bisa ga abin da suke aikatãwa ga mũminai, sunã halarce.

(8) Kuma ba su tuhumce su ba, fãce kawai domin sun yi ĩmãni da Allah Mabuwãyi, wanda ake gõdewa.

(9) Wanda Yake shi ne da mulkin sammai da ƙasa, kuma Allah a kan kõme halarce Yake.

(10) Lalle ne waɗanda suka fitini mũminai maza da mũminai mãta, sa'an nan ba su tũba ba to, sunã da azãbar Jahannama, kuma sunã da azãbar gõbara.

(11) Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashin gidãjen. Wancan abu fa shi ne rabo babba.

(12) Lalle ne damƙar Ubangijinka mai tsanani ce ƙwarai.

(13) Lalle ne Shĩ, Shi ne Mai ƙãga halitta, kuma Ya mayar da ita (bãyan mutuwa).

(14) Kuma Shi ne Mai gãfara, Mai bayyana sõyayya.

(15) Mai Al'arshi mai girma

(16) Mai aikatãwa ga abin da Yake nufi.

(17) Ko lãbãrin rundanõni yã zo maka.

(18) Fir'auna da samũdãwa?

(19) Ã'aha! waɗanda suka kãfirta sunã cikin ƙaryatãwa.

(20) Alhãli, Allah daga bãyansu, Mai kẽwaye su ne (da sanin Sa).

(21) Ã'aha! Shi Alƙur'ãni ne mai girma.

(22) A cikin Allo tsararre.