أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn مؤسس ومدير المنتدى
عدد المساهمات : 52644 العمر : 72
| موضوع: 83 - Suratu Almudaffifeen الإثنين 19 سبتمبر 2022, 4:26 pm | |
| 83 - Suratu Almudaffifeen Da sunan Allah Mai rahama (1) Bone ya tabbata ga mãsu naƙƙasãwa.
(2) Waɗanda suke idan suka auna daga mutãne suna cika mũdu.
(3) Kuma idan sun auna musu da zakka* ko da sikẽli, suna ragẽwa * Mũdu.
(4) Ashe! Waɗancan bã su tabbata cẽwa lalle sũ, ana tãyar da su ba?
(5) Domin yini mai girma.
(6) Yinin da mutãne ke tãshi zuwa ga Ubangijin halitta?
(7) Haƙĩƙa lalle ne littãfin fãjirai dãhir, yana a cikin Sijjĩn.
(8) Kuma, mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽ wa Sijjĩn?
(9) Wani ittãfi ne rubũtacce.
(10) Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa.
(11) Waɗanda suke ƙaryatãwa game da rãnar sakamako.
(12) Babũ mai ƙaryatãwa gare shi fãce dukan mai ƙẽtare haddi mai yawan zunubi.
(13) Idan ana karãtun ãyõyinmu, a kansa, sai ya ce: tãtsũniyõyin mutãnen farko ne.
(14) A'aha! Bã haka ba, abin da suka kasance suna aikatãwa dai, yã yi tsãtsa a cikin zukãtãnsu.
(15) A'aha! Haƙĩƙa, lalle ne sũ daga Ubangijinsu, rãnar nan, waɗanda ake shãmakancẽwa ne.
(16) Sa'an nan, lalle ne, sũ mãsu shiga cikin Jahĩm ne.
(17) Sa'an nan a ce: "Wannan shi ne abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi."
(18) A'aha! Haƙĩƙa lalle ne littãfin mãsu ɗã'ã yana a cikin Illiyyĩna?
(19) Kuma mẽne ne yã sanar da kai abin da ake cẽwa Illiyyũna?
(20) Wani littãfi ne rubũtacce.
(21) Muƙarrabai* suke halarta shi. * Malã'iku masu daraja.
(22) Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah tabbas suna cikin ni'ima.
(23) A kan karagu, suna ta kallo.
(24) Kana sani a cikin fuskõkinsu, akwai kwarjinin ni'ima.
(25) Ana shãyar da sũ daga wata giya wadda aka yunƙe a kan rufinta.
|
|
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn مؤسس ومدير المنتدى
عدد المساهمات : 52644 العمر : 72
| موضوع: رد: 83 - Suratu Almudaffifeen الإثنين 19 سبتمبر 2022, 4:26 pm | |
| (26) ¡arshen kurɓinta miski ne. To, a cikin wannan, mãsu gwagwarmaya su yi ta gwagwarmayar nẽma.
(27) Kuma abin da ake gauraya ta da shi, daga tasnĩm yake.
(28) (Wato) wani marmaro ne wanda muƙarrabai ke sha daga gare shi.
(29) Lalle ne, waɗanda suka kãfirta sun kasance (a dũniya) suna yi wa waɗanda suka yi ĩmãni dãriya.
(30) Kuma idan sun shuɗe su sai su dinga yin zunɗe.
(31) Kuma idan suka jũya zuwa ga iyãlansu, sai su tafi suna kãkãci.
(32) Kuma idan sun gan su sai su ce: "Lalle waɗannan ɓatattu ne."
(33) Alhãli kuwa, ba a aike su ba dõmin su zama mãsu tsaro a kansu.
(34) To, yau fa (a Lãhira] waɗanda suka yi ĩmãni, sũ ke yi wa kãfirai dãriya.
(35) A kan karagu, suna ta kallo.
(36) Shin an sãka ma kãfirai abin da suka kasance suna aikatawa?* * Amsar tambaya "na'am.".
|
|