منتديات إنما المؤمنون إخوة (2024 - 2010) The Believers Are Brothers

(إسلامي.. ثقافي.. اجتماعي.. إعلامي.. علمي.. تاريخي.. دعوي.. تربوي.. طبي.. رياضي.. أدبي..)
 
الرئيسيةالأحداثأحدث الصورالتسجيل
(وما من كاتب إلا سيبلى ** ويبقى الدهر ما كتبت يداه) (فلا تكتب بكفك غير شيء ** يسرك في القيامة أن تراه)

IZHAR UL-HAQ

(Truth Revealed) By: Rahmatullah Kairanvi
قال الفيلسوف توماس كارليل في كتابه الأبطال عن رسول الله -صلى الله عليه وسلم-: "لقد أصبح من أكبر العار على أي فرد مُتمدين من أبناء هذا العصر؛ أن يُصْغِي إلى ما يظن من أنَّ دِينَ الإسلام كَذِبٌ، وأنَّ مُحَمَّداً -صلى الله عليه وسلم- خَدَّاعٌ مُزُوِّرٌ، وآنَ لنا أنْ نُحارب ما يُشَاعُ من مثل هذه الأقوال السَّخيفة المُخْجِلَةِ؛ فإنَّ الرِّسَالة التي أدَّاهَا ذلك الرَّسُولُ ما زالت السِّراج المُنير مُدَّةَ اثني عشر قرناً، لنحو مائتي مليون من الناس أمثالنا، خلقهم اللهُ الذي خلقنا، (وقت كتابة الفيلسوف توماس كارليل لهذا الكتاب)، إقرأ بقية كتاب الفيلسوف توماس كارليل عن سيدنا محمد -صلى الله عليه وسلم-، على هذا الرابط: محمد بن عبد الله -صلى الله عليه وسلم-.

يقول المستشرق الإسباني جان ليك في كتاب (العرب): "لا يمكن أن توصف حياة محمد بأحسن مما وصفها الله بقوله: (وَمَا أَرْسَلْنَاكَ إِلَّا رَحْمَةً لِّلْعَالَمِين) فكان محمدٌ رحمة حقيقية، وإني أصلي عليه بلهفة وشوق".
فَضَّلَ اللهُ مِصْرَ على سائر البُلدان، كما فَضَّلَ بعض الناس على بعض والأيام والليالي بعضها على بعض، والفضلُ على ضربين: في دِينٍ أو دُنْيَا، أو فيهما جميعاً، وقد فَضَّلَ اللهُ مِصْرَ وشَهِدَ لها في كتابهِ بالكَرَمِ وعِظَم المَنزلة وذَكَرَهَا باسمها وخَصَّهَا دُونَ غيرها، وكَرَّرَ ذِكْرَهَا، وأبَانَ فضلها في آياتٍ تُتْلَى من القرآن العظيم.
المهندس حسن فتحي فيلسوف العمارة ومهندس الفقراء: هو معماري مصري بارز، من مواليد مدينة الأسكندرية، وتخرَّجَ من المُهندس خانة بجامعة فؤاد الأول، اشْتُهِرَ بطرازهِ المعماري الفريد الذي استمَدَّ مَصَادِرَهُ مِنَ العِمَارَةِ الريفية النوبية المَبنية بالطوب اللبن، ومن البيوت والقصور بالقاهرة القديمة في العصرين المملوكي والعُثماني.
رُبَّ ضَارَّةٍ نَافِعَةٍ.. فوائدُ فيروس كورونا غير المتوقعة للبشرية أنَّه لم يكن يَخطرُ على بال أحَدِنَا منذ أن ظهر وباء فيروس كورونا المُستجد، أنْ يكونَ لهذه الجائحة فوائدُ وإيجابيات ملموسة أفادَت كوكب الأرض.. فكيف حدث ذلك؟!...
تخليص الإبريز في تلخيص باريز: هو الكتاب الذي ألّفَهُ الشيخ "رفاعة رافع الطهطاوي" رائد التنوير في العصر الحديث كما يُلَقَّب، ويُمَثِّلُ هذا الكتاب علامة بارزة من علامات التاريخ الثقافي المصري والعربي الحديث.
الشيخ علي الجرجاوي (رحمه الله) قَامَ برحلةٍ إلى اليابان العام 1906م لحُضُورِ مؤتمر الأديان بطوكيو، الذي دعا إليه الإمبراطور الياباني عُلَمَاءَ الأديان لعرض عقائد دينهم على الشعب الياباني، وقد أنفق على رحلته الشَّاقَّةِ من مَالِهِ الخاص، وكان رُكُوبُ البحر وسيلته؛ مِمَّا أتَاحَ لَهُ مُشَاهَدَةَ العَدِيدِ مِنَ المُدُنِ السَّاحِلِيَّةِ في أنحاء العالم، ويُعَدُّ أوَّلَ دَاعِيَةٍ للإسلام في بلاد اليابان في العصر الحديث.

أحْـلامٌ مِـنْ أبِـي (باراك أوباما) ***

 

 54 - Suratu Al'kamar

اذهب الى الأسفل 
كاتب الموضوعرسالة
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 52644
العمر : 72

54 - Suratu Al'kamar Empty
مُساهمةموضوع: 54 - Suratu Al'kamar   54 - Suratu Al'kamar Emptyالأحد 18 سبتمبر 2022, 10:44 pm

54 - Suratu Al'kamar
Da sunan Allah Mai rahama
(1) Sã'a ta yi kusa, kuma wata *ya tsãge.
* Ƙuraishãwa suka nemi Annabi ya yi addu'a dõmin wata ya tsãge wani ɓangaren nãsa ya fãɗo a ƙasã; ya yi addu'ar, watã ya tsãge, wani abu daga gare shi ya fãɗo kamar yadda suka nema.

(2) Kuma idan sun ga wata ãyã, sai su juya baya su ce: "Sihiri ne mai dõgẽwa!"

(3) Kuma suka ƙaryata, kuma suka bi son zũciyarsu, alhãli kuwa kõwane al'amari (wanda suke son su tũre daga Annabi) an tabbatar da shi.

(4) Kuma lalle, abin da yake akwai tsãwatarwa a cikinsa na lãbãraiya zo musu.

(5) Hikima cikakka! Sai dai abũbuwan gargaɗi bã su amfãni.

(6) Sabõda haka, ka bar su! Rãnar da mai kiran zai yi kira zuwa ga wani abu abin ƙyama.

(7) ¡asƙantattu ga idanunsu zã su fito daga kaburburansu, kamar dai sũ fãri ne waɗandasuka wãtse.

(8) Sunã gaggãwar tafiya zuwa ga mai kiran, kãfirai na cẽwa, "Wannan yini ne mai wuya!"

(9) Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu, sai suka ƙaryata Bawan Mu, kuma suka ce: "Shi mahaukaci ne." Kuma aka tsãwace shi.

(10) Sabõda haka, ya kira Ubangijinsa (ya ce), "Lalle nĩ, an rinjãye ni, sai Ka yi taimako."

(11) Sai Muka bũɗe kõfõfin sama da ruwa mai zuba.

(12) Kuma Muka ɓuɓɓugar da ƙasã ta zama idãnun ruwa, daɗa ruwa ya haɗu a kan wani umarni da aka riga aka ƙaddara shi.

(13) Kuma Muka ɗauke Nũhu a kan (jirgi) na alluna da ƙũsõshi.

(14) Tanã gudãna, a kan idãnun Mu, dõmin sakamako ga wanda aka yi wa kãfircin.

(15) Kuma lalle, Mun bar ta ta zama ãyã. To, Shin, akwai mai tunãni

(16) To, yãyã azãbã Ta take da gargaɗi Na?

(17) Kuma lalle ne, haƙĩkƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ãni, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?

(18) Ãdãwa sun ƙaryata, to, yãya azãbãTa take, da gargaɗi Na?

(19) Lalle Mũ, Mun aika da iska mai tsananin sauti a kansu, a cikin wani yinin nahĩsa mai dõgẽwa.

(20) Tanã fizgar mutãne kamar dai sũ kututturan dabĩno tumɓukakku ne.

(21) To, yãya azãbã Ta take da gargaɗi Na?

(22) Kuma lalle ne, haƙiƙa Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?

(23) Samũdãwa sun ƙaryata game da gargaɗin.

(24) Sai suka ce: "Wani mutum daga cikinmu, shi kaɗai, wai mu bĩ shi! Lalle mũ a lõkacin, haƙĩƙa mun shiga wata ɓata da haukã.

(25) "Shin, an jẽfa masa Manzancin ne, a tsakãninmu? Ã'a, shĩ dai gawurtaccen maƙaryaci ne mai girman kai!"



54 - Suratu Al'kamar 2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 52644
العمر : 72

54 - Suratu Al'kamar Empty
مُساهمةموضوع: رد: 54 - Suratu Al'kamar   54 - Suratu Al'kamar Emptyالأحد 18 سبتمبر 2022, 10:45 pm


(26) Zã su sani a gõbe, wãne ne gawurtaccen mai ƙaryar, mai girman kan?

(27) Lalle Mũ, mãsu aikãwa da rãƙumar* ne, ta zame musu fitina, sai ka tsare su da kallo, kuma ka yi haƙuri.
* Mutãnen Sãleh sun nemi mu'ujiza da rãƙuma, a fitar da ita daga dũtse, sai aka fitar da ita, kuma aka raba ruwan sha a tsakãninsu da ita.

(28) Kuma ka bã su lãbãri cẽwa ruwa rababbe ne a tsakãninsu (da rãƙumar), kõwane sha, mai shi yanã halartar sa.

(29) Sai suka kira abokinsu, sai ya karɓa, sa'an nan ya sõke ta,

(30) To, yãya azãbaTa take da gargaɗi Na?

(31) Lalle Mũ, Mun aika tsãwa guda a kansu, sai suka kasance kamar yãyin mai shinge.

(32) Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?

(33) Mutãnen Lũɗu sun ƙaryata, game da gargaɗi.

(34) Lalle Mun aika iskar tsakuwa a kansu, fãce mabiyan Lũɗu, Mun tsirar da su a lõkacin asuba.

(35) Sabõda wata ni'ima ta daga gare Mu. Kamar haka Muke sãka wa wanda ya gõde.

(36) Kuma lalle, haƙĩƙa, ya yi musu gargaɗin damƙar Mu, sai suka yi musu game da gargaɗin.

(37) Kuma lalle haƙĩƙa, su, sun nẽme shi ta wajen bãƙinsa, sai Muka shãfe idãnunsu. "To, ku ɗanɗani azãbaTa da gargaɗĩ Na."

(38) Kuma lalle, haƙĩƙa, wata azãba matabbaciya tã wãye musu gari da yãƙi, tun da sãfe.

(39) To, ku ɗanɗani azãbãTa da gargaɗĩ Na.

(40) Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur, ani dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?

(41) Kuma lalle, haƙĩƙa, gargaɗin ya jẽ wa mabiyan Fir'auna.

(42) Sun ƙaryata game da ãyõyin Mu, dukansu sai Muka kãma su, irin kãmun Mabuwãyi, Mai ĩkon yi.

(43) Shin, kãfiranku ne mafi alhẽri daga waɗancan, ko kuwa kunã da wata barã'a a cikin littattafai?

(44) Kõ zã su ce: "Mũ duka mãsu haɗa ƙarfi ne dõmin cin nasara?"

(45) Zã a karya* tãron, kuma su jũya bãya dõmin gudu.
* Bushãra ce ga Annabi, cewa zai yi yãƙi da Kuraishi kuma zai rinjãye su. Sa'an nan yãkin ya auku a Badar.

(46) Ã'a, Sã'a ita cẽ lõkacin wa'adinsu, kuma Sã'ar tã fi tsananin masĩfa, kuma ta fiɗãci.

(47) Lalle ne, mãsu laifi sunã a cikin ɓata da hauka.

(48) Rãnar da zã a jã su a cikin wuta a kan fuskõkinsu. "Ku ɗanɗani shãfar wutar Saƙar."

(49) Lalle Mũ, kõwane irin abu Mun halitta shi a kan tsãri.

(50) Kuma umurnin Mu bai zamo ba fãce da kalma ɗaya, kamar walƙãwar ido.



54 - Suratu Al'kamar 2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 52644
العمر : 72

54 - Suratu Al'kamar Empty
مُساهمةموضوع: رد: 54 - Suratu Al'kamar   54 - Suratu Al'kamar Emptyالأحد 18 سبتمبر 2022, 10:45 pm


(51) Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun halaka irin gayyarku. To, shin, akwai mai tunãni?

(52) Kuma kõwane abu, da suka aikata shi, yanã a cikin littattafai.

(53) Kuma dukkan ƙarami da babba, rubutacce ne.

(54) Lalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna da kõguna.

(55) A cikin mazaunin gaskiya, wurin Mai ikon yi, Mai iya zartaswa.



54 - Suratu Al'kamar 2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
 
54 - Suratu Al'kamar
الرجوع الى أعلى الصفحة 
صفحة 1 من اصل 1
 مواضيع مماثلة
-
» 30 - Suratu Ar'rum
» 5 - Suratu Al'ma'ida
» 95 - Suratu At'tín
» 30 - Sûratu'r-Rûm
» 114 - Suratu Al'nas

صلاحيات هذا المنتدى:لاتستطيع الرد على المواضيع في هذا المنتدى
منتديات إنما المؤمنون إخوة (2024 - 2010) The Believers Are Brothers :: (English) :: The Holy Quran is translated :: Hausa-
انتقل الى: