منتديات إنما المؤمنون إخوة (2024 - 2010) The Believers Are Brothers

(إسلامي.. ثقافي.. اجتماعي.. إعلامي.. علمي.. تاريخي.. دعوي.. تربوي.. طبي.. رياضي.. أدبي..)
 
الرئيسيةالأحداثأحدث الصورالتسجيل
(وما من كاتب إلا سيبلى ** ويبقى الدهر ما كتبت يداه) (فلا تكتب بكفك غير شيء ** يسرك في القيامة أن تراه)

IZHAR UL-HAQ

(Truth Revealed) By: Rahmatullah Kairanvi
قال الفيلسوف توماس كارليل في كتابه الأبطال عن رسول الله -صلى الله عليه وسلم-: "لقد أصبح من أكبر العار على أي فرد مُتمدين من أبناء هذا العصر؛ أن يُصْغِي إلى ما يظن من أنَّ دِينَ الإسلام كَذِبٌ، وأنَّ مُحَمَّداً -صلى الله عليه وسلم- خَدَّاعٌ مُزُوِّرٌ، وآنَ لنا أنْ نُحارب ما يُشَاعُ من مثل هذه الأقوال السَّخيفة المُخْجِلَةِ؛ فإنَّ الرِّسَالة التي أدَّاهَا ذلك الرَّسُولُ ما زالت السِّراج المُنير مُدَّةَ اثني عشر قرناً، لنحو مائتي مليون من الناس أمثالنا، خلقهم اللهُ الذي خلقنا، (وقت كتابة الفيلسوف توماس كارليل لهذا الكتاب)، إقرأ بقية كتاب الفيلسوف توماس كارليل عن سيدنا محمد -صلى الله عليه وسلم-، على هذا الرابط: محمد بن عبد الله -صلى الله عليه وسلم-.

يقول المستشرق الإسباني جان ليك في كتاب (العرب): "لا يمكن أن توصف حياة محمد بأحسن مما وصفها الله بقوله: (وَمَا أَرْسَلْنَاكَ إِلَّا رَحْمَةً لِّلْعَالَمِين) فكان محمدٌ رحمة حقيقية، وإني أصلي عليه بلهفة وشوق".
فَضَّلَ اللهُ مِصْرَ على سائر البُلدان، كما فَضَّلَ بعض الناس على بعض والأيام والليالي بعضها على بعض، والفضلُ على ضربين: في دِينٍ أو دُنْيَا، أو فيهما جميعاً، وقد فَضَّلَ اللهُ مِصْرَ وشَهِدَ لها في كتابهِ بالكَرَمِ وعِظَم المَنزلة وذَكَرَهَا باسمها وخَصَّهَا دُونَ غيرها، وكَرَّرَ ذِكْرَهَا، وأبَانَ فضلها في آياتٍ تُتْلَى من القرآن العظيم.
المهندس حسن فتحي فيلسوف العمارة ومهندس الفقراء: هو معماري مصري بارز، من مواليد مدينة الأسكندرية، وتخرَّجَ من المُهندس خانة بجامعة فؤاد الأول، اشْتُهِرَ بطرازهِ المعماري الفريد الذي استمَدَّ مَصَادِرَهُ مِنَ العِمَارَةِ الريفية النوبية المَبنية بالطوب اللبن، ومن البيوت والقصور بالقاهرة القديمة في العصرين المملوكي والعُثماني.
رُبَّ ضَارَّةٍ نَافِعَةٍ.. فوائدُ فيروس كورونا غير المتوقعة للبشرية أنَّه لم يكن يَخطرُ على بال أحَدِنَا منذ أن ظهر وباء فيروس كورونا المُستجد، أنْ يكونَ لهذه الجائحة فوائدُ وإيجابيات ملموسة أفادَت كوكب الأرض.. فكيف حدث ذلك؟!...
تخليص الإبريز في تلخيص باريز: هو الكتاب الذي ألّفَهُ الشيخ "رفاعة رافع الطهطاوي" رائد التنوير في العصر الحديث كما يُلَقَّب، ويُمَثِّلُ هذا الكتاب علامة بارزة من علامات التاريخ الثقافي المصري والعربي الحديث.
الشيخ علي الجرجاوي (رحمه الله) قَامَ برحلةٍ إلى اليابان العام 1906م لحُضُورِ مؤتمر الأديان بطوكيو، الذي دعا إليه الإمبراطور الياباني عُلَمَاءَ الأديان لعرض عقائد دينهم على الشعب الياباني، وقد أنفق على رحلته الشَّاقَّةِ من مَالِهِ الخاص، وكان رُكُوبُ البحر وسيلته؛ مِمَّا أتَاحَ لَهُ مُشَاهَدَةَ العَدِيدِ مِنَ المُدُنِ السَّاحِلِيَّةِ في أنحاء العالم، ويُعَدُّ أوَّلَ دَاعِيَةٍ للإسلام في بلاد اليابان في العصر الحديث.

أحْـلامٌ مِـنْ أبِـي (باراك أوباما) ***

 

 53 - Suratu Al'najm

اذهب الى الأسفل 
كاتب الموضوعرسالة
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 52644
العمر : 72

53 - Suratu Al'najm Empty
مُساهمةموضوع: 53 - Suratu Al'najm   53 - Suratu Al'najm Emptyالأحد 18 سبتمبر 2022, 10:42 pm

53 - Suratu Al'najm
Da sunan Allah Mai rahama
(1) Inã rantsuwa da taurãron, a lõkacin da ya faku.

(2) Ma'abũcinku bai ɓata ba, kuma bai ƙẽtare haddi ba.

(3) Kuma bã ya yin magana daga son zuciyarsa.

(4) (Maganarsa) ba ta zamo ba, fãce wahayi ne da ake aikõwa.

(5) (Malã'ika) mai tsananin ƙarfi *ya sanar da shi.
* Wahayin da ke zuwa ga Annabi bãbu ɓata a cikinsa dõmin Jibrilu mai kãwo shi ga Annabi, Malã'ika ne mai ƙarfi ƙwarai, wani Shaiɗãni bã ya iya taron sa dõmin ya musanya wahayin, kuma Annabi ya san shi sõsai, kuma idan ya kãwo wahayin, sai ya sauko kusa ƙwarai da Annabi, sa'an nan shi kuma Annabi ba rikitacce ba ne, yanã cikin hankalinsa.

(6) Ma'abũcin ƙarfi da kwarjini, sa'an nan ya daidaita.

(7) Alhãli kuwa yanã a sararin samã mafi daukaka.

(8) Sa'an nan ya kusanta, kuma ya matsa zurõwa.

(9) Har ya kasance gwargwadon zirã'i biyu, kõ kuma abin da ya fi kusa.

(10) Sa'an nan ya yi wahayi zuwa ga bãwan Allah (Muhammadu) da abin da ya faɗa (masa).

(11) Zũciyar (Annabi) bata ƙaryata abin da ya gani ba.

(12) Shin, zã ku yi masa musu a kan abin da yake gani?

(13) Kuma lalle ya gan shi, haƙĩƙatan, a wani lõkacin saukarsa.*
* Lamirin Malã'ika Jibrila ne.

(14) A wurin da magaryar tuƙẽwa take.

(15) A inda taken, nan Aljannar makoma take.

(16) Lõkacin da abin da yake rufe magaryar tuƙẽwa ya rufe ta.

(17) Ganinsa* bai karkata ba, kuma bai ƙetare haddi ba.
* Lamirin Malã'ika Jibrila ne.

(18) Lalle, tabbas, (Annabinku) ya ga waɗanda suka fi girma* daga ãyõyin Ubangijinsa.
* Watau dai Alƙur'ani ya zo daga Allah ta hanya mafi aminci har ya sadu da mutãne dõmin su yi aiki da abin da ke cikinsa.

(19) Shin, kun ga Lãta da uzza?*
* Watau kun bar Alƙur'ani kun kõma wa surkullen da kuke haɗãwa game da gumãka su Lãta da Uzza da Manãta. Kuna cewa sũ wakĩlan Mala'ikun da kuke bautã wa ne kuma su 'ya'yan Allah mãtã ne. Sunã cetonku daga Allah.

(20) Da (wani gunki wai shi) Manãta, na ukunsu?

(21) Ashe, kũ ne da ɗa namiji Shĩ (Allah) kuma da ɗiya mace?

(22) Wannan fa ya zama rabo naƙasasshe.

(23) Waɗannan bã kõme ba ne fãce sũnãye, waɗanda kuka ambace su da su, kũ da uwãyenku. Allah bai saukar da wani dalĩli game da su ba. (Kãfirai) bã su biyar kõme fãce zato da abin da rãyukansu ke so, Alhãli kuwa shiriyar* ta daga wajen Ubangijinsu, ta jẽ musu (sai suka bar ta suka kõma wa zaton).
* Watau Alƙur'ani wanda Mala'ika jibrĩla ya zo wa Annabi da shi. Sun bar shi sun kõma wa tatsũniyõyi da gũrace-gũrace.

(24) Ko (an fai cẽwa) mutum zai sãmi abin da yake gũri?

(25) To, Lãhira da dũniya na Allah kawai ne (wanda ya nẽme su daga wani, yã yi kuskure).



53 - Suratu Al'najm 2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 52644
العمر : 72

53 - Suratu Al'najm Empty
مُساهمةموضوع: رد: 53 - Suratu Al'najm   53 - Suratu Al'najm Emptyالأحد 18 سبتمبر 2022, 10:42 pm


(26) Akwai malã'iku da yawa a cikin sammai cẽtonsu bã ya wadãtar da kõme fãce bãyan Allah Yã yi izni (da shi) ga wanda Yake so, kuma Yake yarda.

(27) Lalle waɗannan da bã su yin ĩmãni da Lãhira, haƙĩƙa sunã kiran malã'iku da sũnan mace.

(28) Kuma bã su da wani ilmi game da shi, bã su bin kõme fãce zato alhãli kuwa lalle zato bã ya amfãnar da kõme daga gaskiya.

(29) Sabõda haka sai ka kau da kai daga wanda ya jũya bãya daga ambaton Mu kuma bai yi nufin kõme ba fãce rãyuwar kusa (dũniya).

(30) Wannan ita ce iyãkar abin da suke iya kai gare shi na ilmi. lalle Ubangijinka Shĩ ne Mafi sanin wanda ya ɓace daga hanyar Sa, kuma Shi ne Mafi sani ga wanda ya nẽmi shiriya.

(31) Kuma abin da ke cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasã na Allah kawai ne, dõmin Yã sãka wa waɗanda suka mũnana da abin da suka aikata, kuma Ya sãka wa waɗanda suki kyautata da sakamakon da ya fi kyau.

(32) Waɗanda ke nĩsantar manyan zunubai da abũbuwan alfãsha, fãce ƙanãnan laifuffuka, lalle Ubangijinka Mai yalwatattar gãfara ne, Shĩ ne Ya fi sani ga abinda ke gare ku a lõkacin da Ya ƙãga halittarku daga ƙasa, kuma a lõkacin da kuke tãyuna a cikin cikannan uwãyenku. Sabõda haka, kada ku tsarkake* kanku, Shĩ ne Mafi sani ga wanda ya yi taƙawa.
* Wanda yake mutumin kirki, Allah Ya san shi. Kada ku dinga tsarkake kanku da bãkunanku dõmin neman girma, kõ dõmin neman wani abu dabam.

(33) Shin, ka ga wannan da ya jũya baya?

(34) Ya yi kyauta kaɗan, kuma ya yi rowa?

(35) Shin, akwai ilmin gaibi a wurinsa, Sabõda haka yanã ganin gaibin?

(36) Ko kuwa ba a ba shi lãbãri ba ga abin da yake a cikin Littafan Mũsã?

(37) Da Ibrãhĩm wanda ya cika alkawari?

(38) Cẽwa wani rai mai kãyan laifi bã ya ɗaukar kãyan laifin wani.

(39) Kuma mutum bã shi da kõme fãce abin da ya aikata.

(40) Kuma lalle, aikinsa zã a gan shi.

(41) Sa'an nan a sãka masa da sakamako wanda yake mafi cikar ma'auni?

(42) Kuma lalle, makõmar zuwa Ubangijinka kawai take?

(43) Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya sanya dariya, kuma Ya sanya kũka.

(44) Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya kashe, kuma Ya rãyar.

(45) Kuma lalle Shĩ ne Ya yi halitta nau'i-nau'i, namiji da mace.

(46) Daga wani ɗigon ruwa guda a lõkacin da ake jẽfa shi a cikin mahaifa.

(47) Kuma a kansa ne ƙãga halitta ta biyu take.

(48) Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya azurta, kuma Ya wadãtar.

(49) Kuma lalle, Shĩ, Shi ne Ubangijin Shi'ira.*
* Sũnan wasu taurãri biyu ne sunã fita a bãyan taurarin Jauza'a sunã tafiya daga kudu zuwa arewa karkace. Kabĩlar Lãrabãwa ta Khuza'a na bauta musu da umurnin Abu Kabshah, ɗaya daga cikin kãkannin Annabi na wajen uwa dõmin haka ne Ƙuraishãwa ke ce wa Annabi Ibn abĩ Kabshah, wanda ya ƙãga sãbon addinĩn da ya sãɓawa na ubanninsa.

(50) Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya halaka Ãdãwa na farko.



53 - Suratu Al'najm 2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 52644
العمر : 72

53 - Suratu Al'najm Empty
مُساهمةموضوع: رد: 53 - Suratu Al'najm   53 - Suratu Al'najm Emptyالأحد 18 سبتمبر 2022, 10:43 pm


(51) Da Samũdãwa, sa'an nan bai rage su ba.

(52) Da mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sũ sun kasance mafi zãlunci kuma mafi girman kai.

(53) Da waɗanda aka birkice *ƙasarsu, Ya kãyar da su.
* Mutãnen Lũɗu da aka birkice ƙasarsu da su.

(54) Sa'an nan abin da ya rufe su, ya rufe su.

(55) To, da wace daga ni'imõmin Ubangijinka kake *yin shakka?
* Kamar abõkin magana kõ mai karãtu.

(56) wannan (Muhammadu) mai gargaɗi ne kamar irin mãsu gargaɗi na farko.

(57) Makusanciya* fa, tã yi kusa.
* Makusanciya ita ce Ƙiyãma.

(58) Bãbu wani rai, banda Allah, mai iya bãyani gare ta.

(59) Shin, kuma daga wannan *lãbãri kuke mãmãki?
* Al'ƙur'ãni.

(60) Kuma kunã yin dãriya, kuma bã ku yin kũka?

(61) Alhãli kunã mãsu wãsã?

(62) To, ku yi tawãli'u *ga Allah, kuma ku bauta (masa).
* Anã yin sujadar karatu a nan, amma bã ta a cikin sujadai na tĩlas.



53 - Suratu Al'najm 2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
 
53 - Suratu Al'najm
الرجوع الى أعلى الصفحة 
صفحة 1 من اصل 1
 مواضيع مماثلة
-
» 30 - Suratu Ar'rum
» 5 - Suratu Al'ma'ida
» 95 - Suratu At'tín
» 30 - Sûratu'r-Rûm
» 114 - Suratu Al'nas

صلاحيات هذا المنتدى:لاتستطيع الرد على المواضيع في هذا المنتدى
منتديات إنما المؤمنون إخوة (2024 - 2010) The Believers Are Brothers :: (English) :: The Holy Quran is translated :: Hausa-
انتقل الى: