|
| 43 - Suratu Al'zukhruf | |
| | كاتب الموضوع | رسالة |
---|
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn مؤسس ومدير المنتدى
عدد المساهمات : 52644 العمر : 72
| موضوع: 43 - Suratu Al'zukhruf الأحد 18 سبتمبر 2022, 10:15 pm | |
| 43 - Suratu Al'zukhruf Da sunan Allah Mai rahama (1) Ḥ. M̃.
(2) Ina rantsuwa da Littãfi Mabayyani.
(3) Lalle Mũ, Mun sanya shi abin karãtu na Lãrabci, tsammãninku, kunã hankalta.
(4) Kuma lalle, shĩ, a cikin uwar littãfi a wurin Mu, haƙĩƙa, maɗaukaki ne, bayyananne.
(5) Shin, zã Mu kau da kai daga saukar da hukunci daga gare ku ne dõmin kun kasance mutane mãsu ɓarna?
(6) Alhãli kuwa sau nawa Muka *aika wani Annabi a cikin mutãnen fãrko! * Tun da ba Mu bar mutãnen farko mãsu ɓarna ba, sai da Muka aika musu Manzanni, kuma kõwace ƙungiya daga cikin waɗanda aka aikawa wani Manzo sai da ta yi izgili game da Manzonsu, har abin ya kai ga halakar shũgabanninsu. To, haka mutãnenka, bã zã Mu bar su ba, sabõda ɓarnarsu, sai Mun aike ka zuwa gare su, su yi izgili game da kai, har a halaka shũgabanninsu, sa'an nan sauransu, su bi abin da aka umurce su da shi.
(7) Kuma wani Annabi bai je musu ba fãce sun kasance, game da shi, sunã mãsu yin izgili.
(8) Sai Muka halakar da waɗanda suke sũ ne mafiya ƙarfin damƙa daga gare su. Kuma abin misãlin mutãnen farkon ya shũɗe.
(9) Kuma lalle ne, idan ka tambaye su, "Wãne ne ya halitta sammai da ƙasa?" Lalle zã su ce, "Mabuwãyi Mai ilmi ne Ya halitta su."
(10) Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa kuma Ya sanya muku hanyõyi a cikinta, tsammãninku za ku nẽmi shiryuwa.'
(11) Kuma Wanda Ya saukar da ruwa daga sama, a kan wani gwargwado, sai Muka rãyar da gari matacce game da shi. Kamar haka nan ake fitar da ku (daga kabari).
(12) Kuma Wanda Ya halitta ma'aura dukansu, kuma Ya sanya muku, daga jirgi da dabbõbin ni'ima, abin da kuke hawa.
(13) Domin ku daidaitu a kan bãyansa, sa'an nan ku tuna ni'imar Ubangijinku a lõkacin da kuka daidaita a kansa kuma ku ce, "Tsarki ya tabbata ga Wanda Ya hõre mana wannan alhãli kuwa ba mu kasance mãsu iya rinjãya gare Shi ba.
(14) "Kuma lalle mũ haƙĩƙa mãsu* jũyãwa muke, zuwa ga Ubangijinmu." * Ku yi dalĩli da hõrewar abin hawa gare ku zuwa ga tabbatar tãshinku dõmin hisãbin Ƙiyãma, dõmin ku bi umurninsa a dũniya, kuma ku bar al'adunku.
(15) Kuma suka sanya *Masa juz'i daga bãyinsa. Lalle ne mutum, haƙĩƙa, mai yawan kãfirci ne, mai bayyanãwar kãfircin. * suka ce malã'iku 'ya'ya mãtane na Allah, sunã bauta musu ne dõmin su kusantar da su zuwa ga Allah, watau dõmin su cece su daga azãba. Sun yi wannan ƙarya ne dõmin su tabbatar da al'ãdarsu ta surkulle. Sabõda haka suka yi wa Allah ƙarya suka naƙasa shi da haka, kuma suka naƙasa malã'iku mãsu daraja a wurin Allah kuma suka kãfirce wa ni'imar da Allah Ya yi musu wajen aiko musu Manzo mai shiryar da su. Sa'an suka kafa hujja da ƙarya dõmin su danne gaskiya.
(16) Kõ zã Ya ɗauki 'ya'ya mãtã daga abin da Yake halittawa ne, kuma Ya zãɓe ku da ɗiya maza?
(17) Alhãli kuwa idan an bãyar da bushãra ga ɗayansu da abin da ya buga misãli da shi ga Mai rahama, sai fuskarsa ta yini tanã wadda aka baƙanta launinta, kuma yanã cike da baƙin ciki.
(18) Ashe, kuma (Allah zai zãɓi) wanda ake rẽno a cikin ƙawa alhãli kuwa gã shi a husũma bã mai iya bayyanawar magana ba?
(19) Kuma suka mayar da malã'iku ('yã'ya) mãtã, alhãli kuwa sũ, waɗanda suke bãyin (Allah) Mai rahama ne! Shin, sun halarci halittarsu ne? zã a rubũta shaidarsu kuma a tambaye su.
(20) Kuma suka ce: "Dã Mai rahama ya so, dã ba mu bauta musu ba." Bã su da wani ilmi game da wancan! Bãbu abin da suke yi fãce yanki-faɗi.
(21) Kõ Mun bã su wani littãfi ne a gabãninsa (Alƙur'ãni) sabõda haka da shĩ suke riƙe?
(22) Ã'a, sun ce dai, "Lalle mũ, mun sãmi ubanninmu a kan wani addini (na al'ãda) kuma lalle mũ, a kan gurãbansu muke mãsu nẽman shiryuwa."
(23) Kuma kamar haka, ba Mu aika wani mai gargaɗi ba a gabãninka, a cikin wata alƙarya, fãce mani'imtanta sun ce, "Lalle mũ, mun sãmi ubanninmu a kan wani addini kuma lalle mũ, mãsu kõyi nea kan gurãbansu."
(24) (Sai mai gargaɗin) ya ce: "Shin, ban zo muku da abin da ya fi zama shiriya daga abin da kuka sãmi ubanninku a kansa ba?" Suka ce, "Lalle mũ dai mãsu kafirta ne game da abin da aka aiko ku da shi."
(25) Sabõda haka Muka yi musu azãbar rãmuwa. To, ka dũbi yadda ãƙibar mãsu ƙaryatãwa take.
|
| | | أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn مؤسس ومدير المنتدى
عدد المساهمات : 52644 العمر : 72
| موضوع: رد: 43 - Suratu Al'zukhruf الأحد 18 سبتمبر 2022, 10:16 pm | |
| (26) Kuma (ka ambaci) lõkacin da Ibrãhĩm ya ce wa ubansada mutãnensa, "Lalle nĩ mai barranta ne daga abin da kuke bautãwa."
(27) "Fãce wannan *da Ya ƙãga halittata, to, lalle Shĩ ne zai shiryar da ni." * Bã ni bauta wa gumãka, amma inã bautawa Allah wanda Ya ƙãgi halittata.
(28) Kuma (Ibrãhĩm) ya sanya (ita wannan magana) kalma mai wanzuwa a cikin zuriyarsa, tsammãninsu su kõmo daga ɓata.
(29) Ã'a, Na jiyar da waɗannan mutãne dãɗi sũ da ubanninsu har gaskiya, da Manzo mai bayyanawar gaskiyar, ya zo musu.
(30) Kuma a lõkacin da gaskiyar ta jẽ musu sai suka ce: "Wannan sihiri ne kuma mũ mãsu kãfirta da shi ne."
(31) Kuma suka ce: "Don me ba a saukar da wannan Alƙur'ãni a kan wani mutum mai girma daga alƙaryun* nan biyu ba?" * Sunã nufin Makka da tã'ifa, kuma sunã nufi a saukar da Alƙur'ãni ga walĩdu ɗan Mugĩra na Makka kõ ga Urwatu ɗan Mas'ũdi As saƙafi a Ta'ifa. Watau sunã sũkar Muhammadu dõmin bã shi da dũkiya. A gare su mai dũkiya shĩ ne babban mutum, wanda ya cancanta Allah Ya aiko shi ga mutãne.
(32) Shin, sũ ne ke raba rahamar Ubangijinka? Mũ ne, Muka raba musu abincinsu a cikin rãyuwar dũniya, kuma Muka ɗaukaka waɗansunsu a kan waɗansu da darajõji dõmin waɗansunsu su riƙi waɗansu lẽburori kumarahamar Ubangijinka (ta Annabci*), ita ce mafificiya daga abin da suke tãrãwa. * Tun da ba Mu bar rabon abincin rãyuwarsu ta dũniya a hannunsu ba, to, ta yãya ne zã Mu bar babban abu kamar Annabci da shiryar da mutãne ga hannãyensu? Wãtau bã zai yiwu Mu yi ba sai yadda Muke so kawai, kõ su bi, kõ su kãfirta, duka daidai ne a gare Mu.
(33) Kuma bã dõmin mutane su kasance al'umma ɗaya ba, lalle ne, dã Mun sanya wa mãsu kãfircẽ wa Mai Rahama, a gidãjensu, rufi na azurfa, kuma da matãkalai, ya zama a kanta suke tãƙãwa.
(34) Kuma a gidãjensu, Mu sanya) ƙyamãre da gadãje, a kansu suke kishingiɗa.
(35) Da zĩnãriya. Kuma dukan wancan abu bai zama ba, sai jin dãɗin rãyuwar dũniya nekawai' alhãli kuwa Lãhira, a wurin Ubangijinka, ta mãsu taƙawa ce.
(36) Kuma wanda ya makanta daga barin hukuncin Mai rahama, to, zã Mu lulluɓe shi da shaiɗan, watau shĩ ne abõkinsa.
(37) Kuma lalle su haƙĩƙa sunã kange su daga hanya, kuma sunã Zaton cẽwa sũ mãsu shiryuwa ne.
(38) Har a lõkacin da (abõkin Shaiɗan) ya zo Mana (ya mutu) sai ya ce: (wa Shaiɗan) "Dã dai a tsakãnina da tsakãninka akwai nĩsan gabas da yamma, sabõda haka, tir da kai ga zama abõkin mutum!"
(39) Kuma (wannan magana) bã za ta amfãne ku ba, a yau, dõmin kun yi zãlunci, lalle ku mãsu tãrẽwa ne a cikin azãba.
(40) Shin to, kai kanã jiyar da kurma ne, ko kanã shiryar da makãho da wanda ke a cikin ɓata bayyananna?
(41) To, kõ dai Mu tafi *da kai to, lalle Mũ, mãsu yin azãbarrãmu, wa ne a kansu. * Mu tafi da kai, watau Mu karɓi ranka, ka mutu, to, dã Mun yi musu azãba ke nan, dõmin sun rasa mai shiryar da su.
(42) Kõ kuma Mu nũna maka abin da Muka yi musu wa'adi, to, lalle Mũ, Mãsu ĩkon tasarrufi a kansu ne.
(43) Sabõda haka, ka yi riƙo ga abin da aka yi wahayi da shi zuwa gaie ka. Lalle ne kai, kanã a kan hanya madaidaiciya.
(44) Kuma shi (abin wahayin) ambato (na ɗaukaka) ne a gare ka da kuma ga mutãnenka, kuma zã a tambaye ku.
(45) Kuma ka tambayi waɗanda Muka aika a gabãninka daga Manzannin Mu, "Shin, Mun sanya waɗansu gumãka, wasun (Allah), Mai rahama, anã bauta musu?"
(46) Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Mũsã, game da ãyõyin Mu, zuwa ga Fir'auna da mashãwartansa, sai ya ce: "Lalle nĩ, Manzo ne daga Ubangijin halittu."
(47) To, a lõkacin da ya jẽ musu da ãyõyin Mu, sai gã su sunã yi musu dãriya.
(48) Kuma ba Mu nũna musu wata ãyã ba, fãce ita ce mafi girma daga 'yar'uwarta. Kuma Muka kãma su da azãba, tsammãninsu kõ sunã kõmõwa.
(49) Kuma suka ce: "Yã kai mai sihiri! Ka rõƙa mana Ubangijinka da albarkacin abin da yi alkawari a wurinka, lalle mũ, haƙĩƙa, mãsu shiryuwa ne."
(50) To, a lõkacin da duk Muka kuranye musu azãba, sai gã su sunã warware alkawarinsu.
|
| | | أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn مؤسس ومدير المنتدى
عدد المساهمات : 52644 العمر : 72
| موضوع: رد: 43 - Suratu Al'zukhruf الأحد 18 سبتمبر 2022, 10:16 pm | |
| (51) Kuma Fir'auna ya yi kira a cikin mutãnensa, ya ce: "Ya mutãnẽna! Ashe mulkin Masar bã a gare ni yake ba, kuma waɗannan kõguna sunã gudãna daga ƙarƙashĩna? Ashe, ba ku gani ba?"
(52) "Kõ kuma bã nĩ ne mafĩfĩci ba daga wannan wanda yake shĩ wulakantacce ne kuma bã ya iya bayyanawar magana sai da ƙyar?
(53) "To, don me, ba a jẽfa mundãye na zĩnãriya a kansaba, kõ kuma malã'iku su taho tãre da shi haɗe?"
(54) Sai ya sassabce hankalin mutãnensa, sabõda haka suka bĩ shi. Lalle sũ, sun kasance waɗansu irin mutãne ne fãsiƙai.
(55) Sabõda haka a lõkacin da suka husãtar da Mu, Muka yi musu azãbar rãmuwa sai Muka nutsar da su gabã ɗaya.
(56) Sai Muka sanya su magabãta kuma abin misãli ga mutãnen ƙarshe.
(57) Kuma a lõkacin da aka buga misãli da ¦an Maryama, sai gã mutãnenka daga gare shi (shi misalin) sunã dãriya da izgili.
(58) Kuma suka ce: "Shin, gumãkanmu ne mafĩfĩta kõ shi (¦an Maryama)?" Ba su buga wannan misãli ba a gare ka fãce dõmin yin jidãli.* Ã'a, sũ mutãne nemãsu husũma. * Wãtau da aka ce gumãka damãsu bauta musu duka abincin wutar Jahannama ne kamar yadda yake a cikin sura ta 21 ãyã ta 98 da 99, sai suka ce sun yarda gumakansu su zama tãre da ɗan Maryama.
(59) Shi (¦an Maryama) bai zama ba fãce wani bãwa ne, Mun yi ni'ima a gare shi, kuma Muka sanya shi abin kõyi ga Banĩ Isrã'ĩla.
(60) Kuma dã Munã so lalle ne dã Mun sanya malã'iku, daga ci, kinku, a cikin ƙasa, sunã mayẽwa* * Dã Mun so dã Mun sanya ɗiyansu su zama malã'iku, su fi Ĩsa ɗan Maryama zama abin mãmãki ga halitta, sa'an nan su maye muku a cikin ƙasã maimakon ɗiya masu siffõfi irin na jikunkunanku. Zai fi zama abin mãmãki mutum yahaifi malã'ika bisa mace ta haifi ɗã bã da wani namiji yã kusance ta ba.
(61) Kuma lalle shĩ, haƙĩƙa, wani ilmi ne na Sa'a, sabõda haka, kada ku yi shakka a gare ta, kuma ku bĩ Ni. Wannan ita ce hanya madaidaiciya.
(62) Kuma kada Shaiɗan ya taushe ku (daga hanyar). Lalle shĩ maƙiyi ne a gare ku, mai bayyanãwar ƙiyayya.
(63) Kuma a lõkacin da Ĩsã ya jẽ da hujjõji bayyanannu, ya ce: "Lalle ne nã zo muku da hikima kuma dõmin in bayyana muku, sãshen abin da kuke sãɓã wa jũna acikinsa, sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'a."
(64) "Lalle ne, Allah Shĩ ne Ubangijina kuma Shi ne Ubangijinku sabõda haka ku bauta Masa. Wannan ita ce hanya madaidaiciya."
(65) Sai ƙungiyõyi *suka sãɓa a tsakãninsu. To, bone yã tabbata ga waɗanda suka yi zãlunci daga azãbar yini mai raɗaɗi! * Nasãra suka kasu a cikin ƙungiyõyi a bayan Ĩsã. Ya'akubiyya, mãsu cewa Ĩsã ɗan Allah ne, da Malakãniyya, mãsu cewa Ĩsa ɗayan uku ne. Waɗansu kuma suka ce bãwan Allah ne watau su ne Musulminsu, kuma waɗansu daga Musulmin suka kãfirta a bãyan zakuwar, Muhammadu tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, sabõda sun ƙi yarda da Annabcinsa. Yahũdu suka ce: "Ĩsã bã Annabi ba ne dan zina ne." Allah Ya la'ani kãfirai dukansu.
(66) Shin sunã jiran wani abu ne? sai dai Sa'a ta jẽ musu bisaga abke, alhãli kuwa ba su sani ba.
(67) Masõya a yinin nan, sãshensu zuwa ga sãshe maƙiya ne, fãce mãsu taƙawa (sũ kam mãsu son jũna ne).
(68) Ya bãyĩNa! Bãbu tsõro a kanku a yau, kuma bã zã ku yi baƙin ciki ba.
(69) Waɗanda suka yi ĩmãni da ãyõyin Mu, kuma suka kasance mãsu sallamawar al'amari (ga Allah).
(70) Ku shiga Aljanna, kũ da mãtan aurenku, anã girmama ku.
(71) Anã kẽwayãwa a kansu da akussa na zĩnãriya da kõfuna, alhãli kuwa a cikinsu akwai abin da rãyuka ke marmari kuma idãnu su ji dãɗi, kuma kũ, a cikinta (Aljannar), madawwama ne.
(72) Kuma waccan ita ce Aljannar, wannan da aka gãdar da ku ita sabõda abin da kuka kasance kunã aikatãwa.
(73) Kunã sãmu, a cikinta, 'yã'yan itãcen marmari mãsu yawa, daga cikinsu kuke ci.
(74) Lalle mãsu laifi madawwama ne a cikin azãbar Jahannama.
(75) Bã a sauƙaƙar da ita (azãbar) daga gare su, alhãli kuwa sũ, a cikinta, mãsu kãsa magana ne.
|
| | | أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn مؤسس ومدير المنتدى
عدد المساهمات : 52644 العمر : 72
| موضوع: رد: 43 - Suratu Al'zukhruf الأحد 18 سبتمبر 2022, 10:16 pm | |
| (76) Kuma ba Mu zãlunce su ba, amma sũ ne suka kasance azzãlumai.
(77) Kuma suka yi kira, "Ya Mãliku! Ubangijinka Ya kashe mu mana* " (Mãliku) ya ce: "Lalle kũ mazauna ne." * Watau sunã neman su mutu su huta da ɗaukar aZãba.
(78) Lalle ne, haƙĩƙa, Mun jẽ muku da gaskiya, kuma amma mafi yawanku mãsu ƙi ga gaskiyar ne.
(79) Kõ kuma sun tukka wani al'amari ne? To, lalle Mũ, Mãsu tukkãwa ne.
(80) Ko sunã zaton lalle Mũ, bã Mu jin asĩrinsu da gãnãwarsu? Na'am! Kuma manzannin Mu na tãre da su sunã rubũtãwa.
(81) Ka ce: "Idan har akwai ɗã ga Mai rahama, to, nĩ ne farkon mãsu bauta (wa ɗan)."
(82) Tsarkin Ubangijin sammai da ƙasa, Ubangijin Al'arshi, ya tabbata daga abin da suke sifantãwa.
(83) Sabõda haka, ka ƙyãlẽ su, su kũtsa kuma su yi wãsã har su haɗu da yininsu, wanda ake yi musu wa'adi da shi.
(84) Kuma Shĩ ne wanda ke abin bautãwa a sama kuma abin bautãwa a ƙasa, kuma, Shĩ ne Mai hikima, Masani.
(85) Kuma albarkar wanda ke da mulkin sammai da ƙasã abin da ke a tsakãninsu tã bayyana, kuma a wurin Sa ne ilmin Sa'a yake, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku.
(86) Kuma waɗanda suke kira baicin Sa ba su mallaki cẽto ba, fãce wanda ya yi shaida da gaskiya, kuma sũ, sunã sane* (da haka). * Su waɗanda suka yi shaida da gaskiya sun san bãbu mai mallakar ceto ga wani fãce Allah. Sabõda haka Allah nã yi musu izni su ceci wanda Yake son su cece shi, ba wanda su suke so ba. Ma'anar iznin da ceto ga bãyin Allah sãlihai ita ce dõmin Allah Ya bayyana darajar mai ceton ne kawai, bã don yanã da wani hakki ba, ga Allah. Allah Ya tsarkaka daga wata halittar Sa ta sãmi wani hakki a kan Sa. Kõwa bãwan Sa ne.
(87) Kuma lalle idan ka tambaye su: "Wãne ne ya halitta su?" Lalle ne zã su ce Allah ne. To, yãya ake jũyar da su?
(88) Kuma da (ilmin) maganar Sa (Annabi) "Ya Ubangijĩna! Lalle waɗannan mutãne ne waɗanda bã zã su yi ĩmãni ba."
(89) To, sai ka kau da kai daga gare su, kuma ka ce, "salãmã." Sa'an nan kuma zã su sani.
|
| | | | 43 - Suratu Al'zukhruf | |
|
مواضيع مماثلة | |
|
| صلاحيات هذا المنتدى: | لاتستطيع الرد على المواضيع في هذا المنتدى
| |
| |
| |