منتديات إنما المؤمنون إخوة (2024 - 2010) The Believers Are Brothers

(إسلامي.. ثقافي.. اجتماعي.. إعلامي.. علمي.. تاريخي.. دعوي.. تربوي.. طبي.. رياضي.. أدبي..)
 
الرئيسيةالأحداثأحدث الصورالتسجيل
(وما من كاتب إلا سيبلى ** ويبقى الدهر ما كتبت يداه) (فلا تكتب بكفك غير شيء ** يسرك في القيامة أن تراه)

IZHAR UL-HAQ

(Truth Revealed) By: Rahmatullah Kairanvi
قال الفيلسوف توماس كارليل في كتابه الأبطال عن رسول الله -صلى الله عليه وسلم-: "لقد أصبح من أكبر العار على أي فرد مُتمدين من أبناء هذا العصر؛ أن يُصْغِي إلى ما يظن من أنَّ دِينَ الإسلام كَذِبٌ، وأنَّ مُحَمَّداً -صلى الله عليه وسلم- خَدَّاعٌ مُزُوِّرٌ، وآنَ لنا أنْ نُحارب ما يُشَاعُ من مثل هذه الأقوال السَّخيفة المُخْجِلَةِ؛ فإنَّ الرِّسَالة التي أدَّاهَا ذلك الرَّسُولُ ما زالت السِّراج المُنير مُدَّةَ اثني عشر قرناً، لنحو مائتي مليون من الناس أمثالنا، خلقهم اللهُ الذي خلقنا، (وقت كتابة الفيلسوف توماس كارليل لهذا الكتاب)، إقرأ بقية كتاب الفيلسوف توماس كارليل عن سيدنا محمد -صلى الله عليه وسلم-، على هذا الرابط: محمد بن عبد الله -صلى الله عليه وسلم-.

يقول المستشرق الإسباني جان ليك في كتاب (العرب): "لا يمكن أن توصف حياة محمد بأحسن مما وصفها الله بقوله: (وَمَا أَرْسَلْنَاكَ إِلَّا رَحْمَةً لِّلْعَالَمِين) فكان محمدٌ رحمة حقيقية، وإني أصلي عليه بلهفة وشوق".
فَضَّلَ اللهُ مِصْرَ على سائر البُلدان، كما فَضَّلَ بعض الناس على بعض والأيام والليالي بعضها على بعض، والفضلُ على ضربين: في دِينٍ أو دُنْيَا، أو فيهما جميعاً، وقد فَضَّلَ اللهُ مِصْرَ وشَهِدَ لها في كتابهِ بالكَرَمِ وعِظَم المَنزلة وذَكَرَهَا باسمها وخَصَّهَا دُونَ غيرها، وكَرَّرَ ذِكْرَهَا، وأبَانَ فضلها في آياتٍ تُتْلَى من القرآن العظيم.
المهندس حسن فتحي فيلسوف العمارة ومهندس الفقراء: هو معماري مصري بارز، من مواليد مدينة الأسكندرية، وتخرَّجَ من المُهندس خانة بجامعة فؤاد الأول، اشْتُهِرَ بطرازهِ المعماري الفريد الذي استمَدَّ مَصَادِرَهُ مِنَ العِمَارَةِ الريفية النوبية المَبنية بالطوب اللبن، ومن البيوت والقصور بالقاهرة القديمة في العصرين المملوكي والعُثماني.
رُبَّ ضَارَّةٍ نَافِعَةٍ.. فوائدُ فيروس كورونا غير المتوقعة للبشرية أنَّه لم يكن يَخطرُ على بال أحَدِنَا منذ أن ظهر وباء فيروس كورونا المُستجد، أنْ يكونَ لهذه الجائحة فوائدُ وإيجابيات ملموسة أفادَت كوكب الأرض.. فكيف حدث ذلك؟!...
تخليص الإبريز في تلخيص باريز: هو الكتاب الذي ألّفَهُ الشيخ "رفاعة رافع الطهطاوي" رائد التنوير في العصر الحديث كما يُلَقَّب، ويُمَثِّلُ هذا الكتاب علامة بارزة من علامات التاريخ الثقافي المصري والعربي الحديث.
الشيخ علي الجرجاوي (رحمه الله) قَامَ برحلةٍ إلى اليابان العام 1906م لحُضُورِ مؤتمر الأديان بطوكيو، الذي دعا إليه الإمبراطور الياباني عُلَمَاءَ الأديان لعرض عقائد دينهم على الشعب الياباني، وقد أنفق على رحلته الشَّاقَّةِ من مَالِهِ الخاص، وكان رُكُوبُ البحر وسيلته؛ مِمَّا أتَاحَ لَهُ مُشَاهَدَةَ العَدِيدِ مِنَ المُدُنِ السَّاحِلِيَّةِ في أنحاء العالم، ويُعَدُّ أوَّلَ دَاعِيَةٍ للإسلام في بلاد اليابان في العصر الحديث.

أحْـلامٌ مِـنْ أبِـي (باراك أوباما) ***

 

 41 - Suratu Fussilat

اذهب الى الأسفل 
كاتب الموضوعرسالة
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 52644
العمر : 72

41 - Suratu Fussilat Empty
مُساهمةموضوع: 41 - Suratu Fussilat   41 - Suratu Fussilat Emptyالأحد 18 سبتمبر 2022, 10:11 pm

41 - Suratu Fussilat
Da sunan Allah Mai rahama
(1) Ḥ. M̃.

(2) Saukarwa (da Alƙur' ãni) dãga Mai rahama ne, Mai jin ƙai.

(3) Littãfi ne, an bayyana ãyõyinsa daki-daki, yanã abin karantãwa na Lãrabci, dõmin mutãnen dake sani

(4) Yanã mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi. Sai mafi yawansu suka bijire. Sabõda haka sũ, bã su saurãrãwa.

(5) Kuma suka ce: "Zukatanmu nã a cikin kwasfa daga abin da kake Kiran mu zuwa gare shi, kuma a cikin kunnuwanmu akwai wani nauyi, kuma daga tsakaninmu da tsakaninka akwai wani shãmaki. sahõda haka ka yi aiki, lalle mũ mãsu aiki ne."

(6) Ka ce: "Nĩ mutum kawai ne kamarku, ãnã yin wahayi zuwa gare ni cẽwa abin bautãwarku, abin bautãwa guda ne. Sai ku daidaitu zuwa gare Shi, kuma ku nẽmi gafararSa." Kuma bone ya tabbata ga mãsu yin shirki.

(7) Waɗanda bã su bãyar da zakka, kuma sũ a game da Lãhira su kafirai ne.

(8) Lalle wɗdanda suka yi ĩmãni, Kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da wani sakamako wanda bai yankẽwa.

(9) Ka ce: "Ashe lalle kũ, haƙĩƙa, kunã kafurta a game da wanda Ya halitta kasã a cikin kwanuka biyu, kuma kunã sanya Masa kĩshiyõyi? Wancan fa, shĩ ne Ubangijin halittu."

(10) Kuma Ya sanya, a cikinta, dũwatsu kafaffu daga samanta, kuma Ya sanya albarka a cikinta, kuma Ya ƙaddara abũbuwan cinta a cikinta a cikin kwanuka huɗu mãsu daidaita, dõmin matambaya.

(11) Sa'an nan Ya daidaita zuwa ga sama alhãli kuwa ita (a lõkacin) hayãƙi ce, sai Ya ce mata, ita da ƙasã "Ku zo, bisa ga yarda kõ a kan tĩlas." Suka ce: "Mun zo, munã mãsu ɗã'ã. "

(12) Sai Ya hukunta su sammai bakwai a cikin kwãnuka biyu. Kuma Ya yi wahayi, a cikin kõwace sama da al'amarinta, kuma Muka kãwata sama ta kusa da fitilu kuma don tsari. Wancan ƙaddarãwar Mabuwãyi ne, Masani.

(13) To, idan sun bijire sai ka ce: "Nã yi muku gargaɗi ga wata tsãwa kamar irin tsãwar Ãdãwa da samũdãwa."

(14) A lõkacin da Manzanninsu suka je musu daga gaba gare su kuma daga bãyansu, "Kada ku bauta wa kõwa fãce Allah." suka ce: "Dã UbangiJinmu Yã so, lalle dã Ya saukar da malã' iku, sabõda haka lalle mũ, mãsu kafirta ne a game da abin da aka aiko ku da shi."

(15) To, amma Ãdãwa, sai suka yi girman kai a cikin kasã, bã da wani hakki ba, suka ce: "Wãne ne mafi tsananin ƙarfi daga gare mu?" Ashe, kuma ba su gani ba cẽwa Allah, wanda Ya halitta su Shĩne Mafi ƙarfi daga gare su, kuma sun kasance a game da ãyõyin Mu suna yin musu?

(16) Sai Muka aika, a kansu, da iska mai tsananin sauti da sanyi, a cikin kwãnuka na shu'umci, dõmin Mu ɗanɗana musu azãbar wulãƙanci, a cikin rãyuwar dũniya, kuma lalle azãbar Lãhira ita ce mafi wulãƙantarwa, kuma sũ bã zã a taimake su ba.

(17) Kuma amma Samũdãwa, sai Muka shiryar da su, sai suka fi son makanta a kan shiriya, dõmin haka tsawar azãbar wulãkanci, ta kamã su sabõda abin da suka kasance sunã aikatãwa (dõmin nẽman wata fã'ida).

(18) Kuma Muka tsĩrar da waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka kasance sunã yin taƙawa.

(19) Kuma rãnar da ake tãra maƙiyan Allah zuwa wutã, to, sũ anã kakkange su.

(20) Har idan sun jẽ mata, sai jinsu da ganinsu da fãtunsu, su yi shaida a kansu a game da abin da suka kasance sunã aikatawa.

(21) Kuma suka ce wa fãtunsu, "Don me kuka yi shaida a kanmu?" Suka ce: "Allah, Wanda ke sanya kõwane abu ya yi furuci, Shĩ ne Ya sanya mu mu yi furuci, kuma Shĩ ne Ya halitta ku can da farko, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku."

(22) "Ba ku kasance kunã sani ba a ɓõye, cẽwa jinku zai yi shaida a kanku kuma ganinku zai yi, kuma fãtunku za su yi. Kuma amma kun yi zaton cẽwã Allah bai san abũbuwa mãsu yawa daga abin da kuke aikatãwa ba."

(23) "Kuma wancan zaton nãku wanda kuka yi zaton shi, game da Ubangijinku, ya halakar da ku, sai kuka wãyi gari a cikin mãsu hasãra."

(24) Sabõda haka idan sun yi hakuri, to, wutar, ita ce mazauni a gare su, kuma idan sun nẽmi yarda, to, ba su zama daga waɗanda ake yardwa ba.

(25) Kuma Muka sallaɗar da mabiya* a gare su, sai suka ƙawãta musu abin da ke a gabansu da abin da ke a bãyansu. Kuma kalmar azãba ta wajaba a kansu, a cikin wasu al'ummõmi da suka shũɗe a gabãninsu daga aljannu da mutãne. Lalle sũ, sun kasance mãsu hasãra.
* Mabiya, sũ ne aljannun kõ Shaiɗãnun da ke tãre da mutum.



41 - Suratu Fussilat 2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 52644
العمر : 72

41 - Suratu Fussilat Empty
مُساهمةموضوع: رد: 41 - Suratu Fussilat   41 - Suratu Fussilat Emptyالأحد 18 سبتمبر 2022, 10:11 pm


(26) Kuma waɗanda suka kafirta suka cc, "Kada ku saurãra ga wannan Alkur' ãni, kuma ku yi ta yin kuwwa a ckin (lõkacin karãtun) sa, tsammãninku zã ku rinjaya."

(27) Sabõda haka, lalle zã Mu ɗanɗana wa waɗanda suka kafirta wata azãba mai tsanani, kuma lalle zã Mu sãka musu da mafi mũnin abin da suka kasance sunã aikatãwa.

(28) Wancan shĩ ne sakamakon makiyan Allah, watau wuta. Sunã a gidan dawwama a cikinta, dõmin sakamako ga abin da suka kasance sunã yin musu game da ãyõyin Mu.

(29) Kuma waɗanda suka kafirta suka ce: "Yã Ubangijinmu! Ka nũnã mana wadannan biyun da suka batar da mu daga aljannu da mutãne, mu sanya su a karkashin, ƙafãfunmu, dõmin su kasance daga ƙaskantattu."

(30) Lalle waɗannan da suka ce: "Ubangjinmu, shĩ ne Allah," sa'an nan suka daidaitu, malã'iku na sassauka a kansu (a lõkacin saukar ajalinsu sunã ce musu) "Kada ku ji tsõro, kuma kada ku yi baƙin ciki, kuma ku yi bushãra da Aljanna, wadda kun kasance anã yi muku wa'adi da ita."

(31) "Mũ ne majibintanku a cikin rãyuwar dũniya da kuma a cikin Lãhira, kuma a cikinta kunã da abin da rãyukanku ke sha'awa, kuma kunã da abin da kuke kira (akawo muku) a cikinta.

(32) "A kan liyãfa daga Mai gafara, Mai jin ƙai."

(33) Kuma wãne ne mafi kyau ga magana daga wanda ya yi kira zuwa ga Allah, kuma ya aikata aiki na ƙwarai kuma ya ce: "Lalle nĩinã daga mãsu sallamãwar al'amari zuwa ga Allah?"

(34) Kuma kyautatãwa bã ta daidaita kuma haka mũnanãwa. Ka tunkuɗe cũta da abin da yake mafi kyau, sai ga shi wanda akwai ƙiyayya a tsakaninka da tsakaninsa, kamar dai shi majibinci ne, masoyi.

(35) Kuma bã za a cũsa wa kõwa wannan hãli ba fãce waɗanda suka yi haƙuri, kuma bã zã a cũsa shi ba fãce ga mai rabo mai gima.

(36) Kuma idan wata fizga ta fizge ka daga Shaiɗan, to ka nẽmi tsari ga Allah. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai ji, Masani.

(37) Kuma akwai daga ãyõyin Sa, dare da yini, da rãnã da watã. Kada ku yi sujada ga rãnã, kuma kada ku yi ga watã. Kuma ku yi sujada ga Allah wanda Ya halitta su, idan kun kasance Shĩ ne kuke bauta wa.

(38) To, idan sun yi girman kai, to, waɗanda ke a wurin Ubangijinka, sunã tasbĩhi a gare Shi, a dare da rana, alhãli kuwa sũ, bã su ƙõsãwa.

(39) Kuma akwai daga ãyõyinSa cẽwa lalle kai kanã ganin ƙasã ƙẽƙasasshiya, to, idan Mun saukar da ruwa a kanta, sai ta girgiza kuma ta kumbura. Lalle wannan da Ya rãya ta, haƙĩƙa, Mai rãyar da matattu ne. Lalle Shĩ Mai ĩkon yi ne a kan kõwane abu.

(40) Lalle waɗannan da ke karkacẽwa a cikin ãyõyinMu, bã su fakuwa a gare Mu. Ashe fa, wanda ake jẽfãwa a cikin Wutã ne mafĩfĩci kõ kuwa wanda zai je amintacce a Rãnar ¡iyãma? Ku aikata abin da kuke so! Lalle Shĩ Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa.

(41) Waɗannan da suka kãfirta game da Alkur'ãni a lõkacin da ya je musu, kuma lalle shi haƙĩƙa littãfi ne mabuwãyi.

(42) ¥arna bã zã ta je masa ba daga gaba gare shi. kuma bã zã ta zo ba daga bãya gare shi. Saukarwa ce daga Mai hikima, Gõdadde.

(43) Bã zã a fada maka ba fãce abin da aka riga aka faɗa ga Manzannin da suke a gabãninka. Lalle Ubangijinka, haƙĩƙa, Ma'abũcin gãfara ne, kuma Ma'abũcin azãba mai raɗaɗi ne.

(44) Kuma da Mun sanya shi abin karãtu na ajamanci, lalle dã sun ce, "Don me ba a bayyana ãyõyinsa ba? Ashe, zai yiwu a sãmi littãfi ba'ajame da Manzo Balãrabe?" Ka ce: "Shi, shiriya ne da warkewa ga waɗanda suka yi ĩmãni. Kuma wadanda ba su yi ĩmãni ba akwai wani nauyi a cikin kunnuwansu, kuma shi wata makanta ne a kansu. Waɗannan anã kiran su daga wuri mai nĩsa."

(45) Kuma lalle Mun bai wa Mũsã Littãfi, sai aka yi ɗãɓãni a cikinsa, Kuma ba dõmin wata kalma da tã gabata ba daga Ubangijinka, lalle dã an yi hukunci a tsakãninsu. Kuma lalle sũ, haƙĩƙa sunã a cikin shakka daga, gare shi, mai sanya kõkanto.

(46) Wanda ya aikata aiki na ƙwarai to sabõda kansa ne, kuma wanda ya mũnanã, to, yanã akansa. Kuma Ubangiwinka, bã Mai zãlunci ga bãyin Sa ne ba.

(47) Zuwa gare Shi ake mayar da sanin Sa'a. Kuma waɗansu 'yã'yan itãce bã su fita daga kwasfõfinsu, kuma wata mace bã ta yin ciki, kuma bã ta haihuwa, fãce da saninSa, kuma a rãnar da Yake kiran su (Ya ce): "Inã abõkan tãrayyaTa?" Sai su ce, "Mun sanar da Kai bãbu mai bãyar da shaida da haka nan daga gare mu."

(48) Kuma abin da suka kasance sunã kira a gabãnin haka ya ɓace musu, kuma suka yi zaton cẽwa bã su da wata mafakã.

(49) Mutum bã ya kõsãwa daga addu 'ar nẽman alhẽri kuma idan sharri ya shãfe shi, sai ya zama mai yanke kauna, Mai nũna kãsãwa.

(50) Kuma lalle idan Mun ɗanɗana masa wata rahama daga gareMu, daga bãyan wata cũta ta shãfe shi, lalle zai ce, "Wannan (ni'ima) tãwa ce kuma bã ni zaton Sã'a mai tsayuwa ce, kuma lalle idan aka mayar da ni zuwa ga Ubangijĩna, haƙĩƙa, inã da makõma mafi kyau, a wurin Sa." To, lalle zã Mu bã da lãbãri ga waɗanda suka kãfirta game da abin da suka aikata, kuma lalle Munã ɗanɗana musu daga azãba, Mai kauri.



41 - Suratu Fussilat 2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 52644
العمر : 72

41 - Suratu Fussilat Empty
مُساهمةموضوع: رد: 41 - Suratu Fussilat   41 - Suratu Fussilat Emptyالأحد 18 سبتمبر 2022, 10:11 pm


(51) Kuma idan Muka yi ni'ima ga mutum, sai ya bijire, kuma ya nĩsantar da gẽfensa, kuma idan sharri ya sãme shi, sai ya zama ma'abũcin addu'a mai fãɗi.

(52) Ka ce: "Ashe, kun gani! Idan (Alƙur'ãni) ya kasance daga Allah ne, sa'an nan kun kãfirta a game da Shi, wãne ne mafi ɓata daga wanda yake yanã a cikin sãɓani manisanci (daga gaskiya)?"

(53) Zã Mu nũna musu ãyõyin Mu a cikin sãsanni da kuma cikin rãyukansu, har ya bayyana a gare su cẽwã lalle (Alƙur'ãni), shi ne gaskiya. Ashe, kuma Ubangijinka bai isa ba, ga cẽwa lalle Shĩ halartacce ne a kan kowane abu ne?

(54) To lalle sũ, sunã a cikin shakka daga gamuwa da Ubangijinsu. To, lalle Shĩ, Mai kẽwayẽwane ga dukan kõme ne.



41 - Suratu Fussilat 2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
 
41 - Suratu Fussilat
الرجوع الى أعلى الصفحة 
صفحة 1 من اصل 1
 مواضيع مماثلة
-
» 41 - Suratu Fussilat
» Fussilat
» Fussilat
» Fussilat
» Fussilat

صلاحيات هذا المنتدى:لاتستطيع الرد على المواضيع في هذا المنتدى
منتديات إنما المؤمنون إخوة (2024 - 2010) The Believers Are Brothers :: (English) :: The Holy Quran is translated :: Hausa-
انتقل الى: