منتديات إنما المؤمنون إخوة (2024 - 2010) The Believers Are Brothers

(إسلامي.. ثقافي.. اجتماعي.. إعلامي.. علمي.. تاريخي.. دعوي.. تربوي.. طبي.. رياضي.. أدبي..)
 
الرئيسيةالأحداثأحدث الصورالتسجيل
(وما من كاتب إلا سيبلى ** ويبقى الدهر ما كتبت يداه) (فلا تكتب بكفك غير شيء ** يسرك في القيامة أن تراه)

IZHAR UL-HAQ

(Truth Revealed) By: Rahmatullah Kairanvi
قال الفيلسوف توماس كارليل في كتابه الأبطال عن رسول الله -صلى الله عليه وسلم-: "لقد أصبح من أكبر العار على أي فرد مُتمدين من أبناء هذا العصر؛ أن يُصْغِي إلى ما يظن من أنَّ دِينَ الإسلام كَذِبٌ، وأنَّ مُحَمَّداً -صلى الله عليه وسلم- خَدَّاعٌ مُزُوِّرٌ، وآنَ لنا أنْ نُحارب ما يُشَاعُ من مثل هذه الأقوال السَّخيفة المُخْجِلَةِ؛ فإنَّ الرِّسَالة التي أدَّاهَا ذلك الرَّسُولُ ما زالت السِّراج المُنير مُدَّةَ اثني عشر قرناً، لنحو مائتي مليون من الناس أمثالنا، خلقهم اللهُ الذي خلقنا، (وقت كتابة الفيلسوف توماس كارليل لهذا الكتاب)، إقرأ بقية كتاب الفيلسوف توماس كارليل عن سيدنا محمد -صلى الله عليه وسلم-، على هذا الرابط: محمد بن عبد الله -صلى الله عليه وسلم-.

يقول المستشرق الإسباني جان ليك في كتاب (العرب): "لا يمكن أن توصف حياة محمد بأحسن مما وصفها الله بقوله: (وَمَا أَرْسَلْنَاكَ إِلَّا رَحْمَةً لِّلْعَالَمِين) فكان محمدٌ رحمة حقيقية، وإني أصلي عليه بلهفة وشوق".
فَضَّلَ اللهُ مِصْرَ على سائر البُلدان، كما فَضَّلَ بعض الناس على بعض والأيام والليالي بعضها على بعض، والفضلُ على ضربين: في دِينٍ أو دُنْيَا، أو فيهما جميعاً، وقد فَضَّلَ اللهُ مِصْرَ وشَهِدَ لها في كتابهِ بالكَرَمِ وعِظَم المَنزلة وذَكَرَهَا باسمها وخَصَّهَا دُونَ غيرها، وكَرَّرَ ذِكْرَهَا، وأبَانَ فضلها في آياتٍ تُتْلَى من القرآن العظيم.
المهندس حسن فتحي فيلسوف العمارة ومهندس الفقراء: هو معماري مصري بارز، من مواليد مدينة الأسكندرية، وتخرَّجَ من المُهندس خانة بجامعة فؤاد الأول، اشْتُهِرَ بطرازهِ المعماري الفريد الذي استمَدَّ مَصَادِرَهُ مِنَ العِمَارَةِ الريفية النوبية المَبنية بالطوب اللبن، ومن البيوت والقصور بالقاهرة القديمة في العصرين المملوكي والعُثماني.
رُبَّ ضَارَّةٍ نَافِعَةٍ.. فوائدُ فيروس كورونا غير المتوقعة للبشرية أنَّه لم يكن يَخطرُ على بال أحَدِنَا منذ أن ظهر وباء فيروس كورونا المُستجد، أنْ يكونَ لهذه الجائحة فوائدُ وإيجابيات ملموسة أفادَت كوكب الأرض.. فكيف حدث ذلك؟!...
تخليص الإبريز في تلخيص باريز: هو الكتاب الذي ألّفَهُ الشيخ "رفاعة رافع الطهطاوي" رائد التنوير في العصر الحديث كما يُلَقَّب، ويُمَثِّلُ هذا الكتاب علامة بارزة من علامات التاريخ الثقافي المصري والعربي الحديث.
الشيخ علي الجرجاوي (رحمه الله) قَامَ برحلةٍ إلى اليابان العام 1906م لحُضُورِ مؤتمر الأديان بطوكيو، الذي دعا إليه الإمبراطور الياباني عُلَمَاءَ الأديان لعرض عقائد دينهم على الشعب الياباني، وقد أنفق على رحلته الشَّاقَّةِ من مَالِهِ الخاص، وكان رُكُوبُ البحر وسيلته؛ مِمَّا أتَاحَ لَهُ مُشَاهَدَةَ العَدِيدِ مِنَ المُدُنِ السَّاحِلِيَّةِ في أنحاء العالم، ويُعَدُّ أوَّلَ دَاعِيَةٍ للإسلام في بلاد اليابان في العصر الحديث.

أحْـلامٌ مِـنْ أبِـي (باراك أوباما) ***

 

 37 - Suratu Al'safat

اذهب الى الأسفل 
كاتب الموضوعرسالة
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 52644
العمر : 72

37 - Suratu Al'safat Empty
مُساهمةموضوع: 37 - Suratu Al'safat   37 - Suratu Al'safat Emptyالأحد 18 سبتمبر 2022, 7:55 am

37 - Suratu Al'safat
Da sunan Allah Mai rahama
(1) Inã rantsuwa da mãsu yin sahu-sahu (a cikin salla kõ yãƙi).

(2) Sa'an nan mãsu yin tsãwa* dõmin gargaɗi.
* Mãsu tsãwa, sũ ne Malamai mãsu sãmun ilmin wa'azi daga Annabãwa waɗanda ke karãtun abin tunãwa daga Allah Ubangijin sammai da ƙasa, Mai bãyar da haske ga rãnã, Mai haskaka taurari mãsu ƙãwãtar da samã kuma su tsare ta daga shaiɗanu. An siffanta rãnã da Annabãwa, Malamai da taurãri, ilmi da haske da sababin ƙawa da shiryarwa da kõrar mãsu ɓarna.

(3) Sa'an nan da mãsu karãtun abin tunãtarwa.

(4) Lalle Abin bautawarku haƙĩƙa ¦aya ne.

(5) Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke tsakãninsu, kuma Ubangijin wurãren fitar rãnã.

(6) Lalle Mũ, Mun ƙãwatãr da sama ta kusa da wata ƙawa, watau taurãri.

(7) Kuma sunã tsari daga dukan Shaiɗan mai tsaurin kai.

(8) Bã zã su iya saurãre zuwa ga jama'a mafi ɗaukaka (Malã'iku) ba, kuma anã jĩfar su daga kõwane gẽfe.

(9) Dõmin tunkuɗẽwa kuma sunã da wata azãba tabbatacciya.

(10) Fãce wanda ya fizgi wata kalma, sai yũla mai haske ta bĩ shi.

(11) Ka tambaye su: "Shin sũ ne mafi wuya ga halittawa, kõ, kuwa waɗanda Muka halitta?" Lalle Mũ, Mun halitta su daga lãkã mai ɗauri.

(12) Ã'a, kã yi mãmãki, alhãli kuwa sunã ta yin izgili.

(13) Kuma idan aka tunãtar da su, bã su tunãwa.

(14) Idan suka ga wata ãyã, sai su dinga yin izgili.

(15) Kuma su ce, "Wannnan bã kõme ba, fãce sihiri, ne bayyananne."

(16) "Shin, idan mun mutu, kuma muka kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle mũ tabbas waɗandaake tãyarwa ne?

(17) "Ashe kõ da ubanninmu na farko?"

(18) Ka ce: "Na'am alhãli kuwa kunã ƙasƙantattu."

(19) Tsãwa guda kawai ce, sai gã su, sunã dũbi.

(20) Kuma su ce: "Yã bonenmu! Wannan ita ce rãnar sakamako."

(21) Wannan ita ce rãnar rarrabẽwa wadda kuka kasance kuna ƙaryatãwa.

(22) Ku tãra waɗanda suka yi zãlunci, da abõkan haɗinsu, da abin da suka kasance sunã bautãwa.

(23) Wanin Allah, sabõda haka ku shiryar da su zuwa ga hanyar Jahĩm.

(24) Kuma ku tsayar da su, lalle su, waɗanda ake yi wa tambaya ne.

(25) Me ya sãme ku, bã ku taimakon jũna?



37 - Suratu Al'safat 2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 52644
العمر : 72

37 - Suratu Al'safat Empty
مُساهمةموضوع: رد: 37 - Suratu Al'safat   37 - Suratu Al'safat Emptyالأحد 18 سبتمبر 2022, 7:55 am


(26) Ã'a, sũ a yau, mãsu sallamãwa ne.

(27) Kuma sãshensu ya fuskanta ga sãshe, sunã tambayar jũna.

(28) Suka ce: "Lalle kũ, kun kasance kunã jẽ mana daga wajen dãma (inda muka amince)."

(29) Suka ce: "Ã'a, ba ku kasance mũminai ba.

(30) "Kuma wani dalĩli bai kasance ba gare mu a kanku. Ã'a, kun kasance mutãne ne mãsu kẽtare iyãka."

(31) "Sabõda haka maganar Ubangijinmu ta wajaba a kanmu. Lalle mũ, mãsu ɗanɗanãwa ne."

(32) "Sabõda haka muka ɓatar da ku. Lalle mũ, mun kasance ɓatattu."

(33) To lalle sũ a rãnar nan, mãsu tãrayya ne a cikin azãbar.

(34) Lalle Mũ, kamar haka Muke aikatãwa game, da mãsu laifi.

(35) Lalle sũ, sun kasance idan an ce musu: "Bãbu abin bautãwa, fãce Allah," sai su dõra girman kai.

(36) Kuma sunã cẽwa, "Shin, mũ lalle mãsu barin gumãkanmu ne, sabõda maganar wani mawãƙi mahaukaci?

(37) Ã'a, yã zo da gaskiya kuma ya gaskata Manzanni.

(38) Lalle kũ, haƙĩƙa mãsu ɗanɗana azãba mai raɗaɗi ne.

(39) Kuma bã zã a sãka muku ba fãce da abin da kuka kasance kunã aikatãwa.

(40) Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.

(41) Waɗannan sunã da abinci sananne.

(42) Ya'yan itãcen marmari, kuma sunã waɗanda ake girmamãwa.

(43) A cikin gidãjen Aljannar ni'ima.

(44) A kan karagu, sunã mãsu fuskantar jũna.

(45) Anã kẽwayãwa a kansu da hinjãlan giya, ta daga waɗansu marẽmari.

(46) Farã mai dãɗi ga mashãyan.

(47) A cikinta bãbu jirĩ kuma ba su zama mãsu mãye daga gare ta ba,

(48) Kuma a wurinsu, akwai mãtan aure mãsu taƙaita kallonsu, mãsu manyan idãnu.

(49) Kamar dai su ƙwai ne ɓõyayye.

(50) Sai sãshensu ya fuskanta a kan sãshe, sunã tambayar jũna.



37 - Suratu Al'safat 2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 52644
العمر : 72

37 - Suratu Al'safat Empty
مُساهمةموضوع: رد: 37 - Suratu Al'safat   37 - Suratu Al'safat Emptyالأحد 18 سبتمبر 2022, 7:56 am


(51) Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Lalle ni wani abõki ya kasance a gare ni (a dũniya)."

(52) Yanã cewa, "Shin, kai lalle, kanã daga mãsu gaskatãwa ne?"

(53) "Ashe, idan muka mutu, kuma muka, kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle, mũ tabbas waɗanda ake sãka wa ne?"

(54) (Mai maganar) ya ce: "Shin, kõ ku, mãsu tsinkãya ne (mu gan shi)?"

(55) Sai ya tsinkãya, sai ya gan shi a cikin tsakar Jahim.

(56) Ya ce (masa), "Wallahi, lalle, kã yi kusa, haƙĩƙã, ka halakãni."

(57) "Kuma bã dõmin ni'imar Ubangijĩna ba, lalle, dã na kasance daga waɗanda ake halartarwa (tãre da kai a cikin wutã)."

(58) "Shin fa, ba mu zama mãsu mutuwa ba."

(59) "Sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake azabtarwa ba?"

(60) Lalle, wannan shĩ ne babban rabo mai girma.

(61) Sabõda irin wannan, sai mãsu aiki su yi ta aikatãwa.

(62) Shin wancan shĩ ne mafi zama alhẽri ga liyafa kõ itãciyar zaƙƙũm?

(63) Lalle, Mũ, Mun sanya ta fitina ga. azzãlumai.

(64) Lalle ita wata itãciya ce wadda take fita daga asalin Jahĩm.

(65) Gundarta, kamar dai shi kãnun Shaiɗan ne.

(66) To, lalle sũ haƙĩƙa mãsu ci ne daga gare ta. Sa'an nan mãsu cika cikuna ne daga gare ta.

(67) Sa'an nan lalle sunã da wani garwaye a kanta, daga ruwan zãfi.

(68) Sa'an nan lalle makomarsu, haƙĩƙa, zuwa ga Jãhĩm take.

(69) Lalle sũ, sun iske ubanninsu batattu.

(70) Sabõda haka sũ, a kan gurãbunsu, suke gaggãwa.

(71) Kuma tabbas haƙĩƙa mafi yawan mutãnen farko sun ɓace a gabãninsu.

(72) Kuma tabbas haƙĩƙa, Mun aika mãsu gargaɗi a cikinsu.

(73) Sai ka dũba yadda ãƙibar waɗanda aka yi wa gargaɗi ta kasance.

(74) Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.

(75) Kuma lalle, haƙĩƙa' Nũhu ya kira Mu. To, madalla da mãsu karɓãwa, Mu.



37 - Suratu Al'safat 2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 52644
العمر : 72

37 - Suratu Al'safat Empty
مُساهمةموضوع: رد: 37 - Suratu Al'safat   37 - Suratu Al'safat Emptyالأحد 18 سبتمبر 2022, 7:56 am


(76) Kuma Mun tsĩrar da shi da mutãnensa daga bakin ciki babba.

(77) Muka sanya zurriyarsa sunã mãsu wanzuwa.

(78) Kuma Muka bar masa (yabo) a cikin jama'ar ƙarshe.

(79) Aminci ya tabbata ga Nũhu, a cikin halittu.

(80) Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.

(81) Lalle shi, yanã daga bãyin Mu mũminai.

(82) Sã'an nan Muka nutsar da waɗansunsu.

(83) Kuma lalle daga ƙungiyarsa, haƙĩƙa, Ibrahĩm yake.

(84) A lõkacin da ya je wa ubangijinsa da zũciya kuɓutacciya.

(85) A lõkacin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bautãwa?"

(86) "Shin, ƙiren ƙarya (wãtau) gumãka, wanin Allah, kuke bautãwa?"

(87) "To, mẽne ne zatonku game da Ubangijin halittu?"

(88) Sai ya yi dũbi, dũba ta sõsai, a cikin taurãri.

(89) Sã'an nan ya ce: "Nĩ mai rashin lãfiya ne."

(90) Sai suka jũya ga barinsa, sunã mãsu jũyãwa da bãya.

(91) Sai ya karkata zuwa ga gumãkansu, sa'an nan ya ce: "Ashe bã zã ku ci ba?

(92) "Me ya sãme ku, bã ku magana?"

(93) Sai ya zuba dũka a kansu da hannun dãma.

(94) Sai suka fuskanto zuwa gare shi, sunã gaggãwa.

(95) Ya ce, "Kunã bauta wa abin da kuke sassaƙawa,

(96) "Alhãli, Allah ne Ya halitta ku game da abin da kuke aikatãwa?"

(97) Suka ce: "Ku gina wani gini sabõda shi, sa'an nan ku jẽfa shi a cikin Jahĩm."

(98) Sabõda haka suka yi nufin makĩda game da shi. Sai Muka sanya su, sũ ne mafi ƙasƙanci.

(99) Kuma (Ibrahĩm] ya ce: "Lalle, nĩ mai tafiya ne zuwa ga Ubangijĩna, zai shiryar da ni."

(100) "Ya Ubangijĩna! Ka bã ni (abõkin zama) daga sãlihan mutãne."



37 - Suratu Al'safat 2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 52644
العمر : 72

37 - Suratu Al'safat Empty
مُساهمةموضوع: رد: 37 - Suratu Al'safat   37 - Suratu Al'safat Emptyالأحد 18 سبتمبر 2022, 7:57 am


(101) Sai Muka yi masa bushãra da wani yãro *mai haƙuri.
* Yãron da aka yi bushãra da shi a nan, shĩ ne Ismã'ĩla' sabõda abin da yake tafe a gaba wanda ya shãfi Is'hãƙa da sũnansa a bayyane yã nũna a nan bã shi ba ne. Watau Ismã'ĩla kawai ne.

(102) To, a lõkacin da ya isa aiki tãre da shi, ya ce: "Ya ƙaramin ɗãna! Lalle ne inã gani, a ciki barci, lalle inã yanka ka. To, ka dũba mẽ ka gani?" (Yãron) ya ce: "Ya, Bãbãna! Ka aikata abin da aka umurce ka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga mãsu haƙuri."

(103) Yayin da suka mika wuya sai muka fansheshi da Rago

(104) Kuma Muka kira shi cẽwa "Ya Ibrahĩm!"

(105) "Haƙĩƙa kã gaskata mafarkin." Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.

(106) Lalle wannan ita ce jarrabãwa bayyananna.

(107) Kuma Muka yi fansar yãron da wani abin yanka, mai girma.

(108) Kuma Muka bar (yabo) a kansa a cikin mutãnen ƙarshe.

(109) Aminci ya tabbata ga Ibrãhĩm.

(110) Kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.

(111) Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai.

(112) Kuma Muka yi masa bushãra* Da Is'hãƙa ya zama Annabi daga sãlihan mutãne.
* Wannan sãbuwar bushãra da Is'hãƙa tanã nũna cewa bã shĩ ne wanda kissar yankã ta shãfa ba sabõda haka Isma'ĩla dai ne tabbas, mai ƙissar yankã. Sabõda haka Allah Ya sanya shi wata al'umma dabam' dõmin a sãka masa, sa'an nan aka sãkawa Ibrãhĩm da Is'hãƙa dõmin ya zama wata al'umma ta dabam,.

(113) Kuma Muka yi albarka a gare shi, kuma ga Is'hãka. Kuma daga cikin zurriyarsu akwai mai kyautatãwa da kuma maizãlunci dõmin kansa, mai bayyanãwa (ga zãluncin).

(114) Kuma lalle, Mun yi ni'ima ga Mũsã da Hãrũna.

(115) Kuma Muka tsĩrar da su da mutãnensu daga bakin ciki mai girma.

(116) Kuma Muka taimake su, sabõda haka suka kasance mãsu rinjãya.

(117) Kuma Muka ba su Littãfi mai iyãkar bayãni.

(118) Kuma Muka shiryar da su ga hanya mĩƙaƙƙiya.

(119) Kuma Muka bar (yabo) a gare su a cikin mutãnen karshe.

(120) Aminci ya tabbata ga Mũsã da Hãruna.

(121) Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.

(122) Lalle, sunã daga bãyin Mu mũminai.

(123) Kuma lalle Ilyãs, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.

(124) A lõkacin da yake ce wa mutãnensa, "Ashe, bã zã ku yi taƙawa ba?"

(125) "Shin, kunã bauta wa Ba'al ne, kuma kunã barin Mafi kyautatãwar mãsu halitta?"



37 - Suratu Al'safat 2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 52644
العمر : 72

37 - Suratu Al'safat Empty
مُساهمةموضوع: رد: 37 - Suratu Al'safat   37 - Suratu Al'safat Emptyالأحد 18 سبتمبر 2022, 7:57 am


(126) "Allah Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku farko?"

(127) Sai suka ƙaryata shi. Sabõda haka sũ lalle waɗanda zã a halartãwa ne (a wutã).

(128) Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.

(129) Kuma Muka bar (yabo) a gare shi, a cikin mutãnen ƙarshe.

(130) Aminci ya tabbata ga Ilyãs.

(131) Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.

(132) Lalle shĩ, yanã daga bãyin Mu mũminai.

(133) Kuma lalle Lũdu, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.

(134) A lõkacin da Muka tsĩrar da shi, da mutãnensa gabã ɗaya.

(135) Sai wata tsõhuwa tanã a cikin mãsu wanzuwa (a cikin azãba).

(136) Sã'an nan Muka darkãke waɗansu mutãnen.

(137) Kuma lalle kũ, haƙĩƙa, kunã shũɗewa a kansu, kunã mãsu asubanci.

(138) Kuma da dare. Shin fa, bã zã ku hankalta ba?

(139) Kuma lalle Yũnusa, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.

(140) A lõkacin da ya gudu zuwa ga jirgin ruwa wanda aka yi wa lõdi.

(141) Sã'an nan ya yi ƙuri'a, sai ya kasance a cikin waɗanda aka rinjaya.

(142) Sai kĩfi ya yi lõma da shi, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi.

(143) To, ba dõmin lalle shi ya kasance daga mãsu tasbĩhi ba,

(144) Lalle dã ya zauna a cikin cikinsa har ya zuwa rãnar da zã a tãyar da su.

(145) Sai Muka jẽfa shi ga wani fĩli alhãli kuwa yanã mai raunin rashin lãfiya.

(146) Kuma Muka tsirar da wata itãciya ta kankana a kusa da shi.

(147) Kuma Muka aika shi zuwa ga waɗansu mutãne dubuɗari, kõ sunã ƙaruwa (a kan haka).

(148) Sai suka yi ĩmãni sabõda haka Muka jiyar da su dãdi har wani lõkaci.

(149) Sabõda haka, ka tambaye su, "Shin, Ubangijinka ne da 'ya'ya mãtã, kuma su da ɗiya maza?"

(150) Kõ kuma Mun halitta malã'iku mãtã ne, alhãli kuwa sũ sunãhalarce?



37 - Suratu Al'safat 2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 52644
العمر : 72

37 - Suratu Al'safat Empty
مُساهمةموضوع: رد: 37 - Suratu Al'safat   37 - Suratu Al'safat Emptyالأحد 18 سبتمبر 2022, 7:58 am


(151) To! Lalle sũ, daga ƙiren ƙaryarsu sunã cẽwa.

(152) "Allah Yã haihu," alhãli kuwa lalle sũ, haƙĩƙa maƙaryata ne.

(153) Shin, Yã zãɓi 'yã'ya mãtã ne a kan ɗiya maza?

(154) Mẽ ya same ku? Yãya kuke hukuntãwa (wannan hukunci)?

(155) Shin, bã ku tunãni?

(156) Ko kuma kunã da wani dalĩli bayyananne ne?

(157) To, ku zo da littãfinku idan kun kasance mãsu gaskiya.

(158) Kuma suka sanya nasaba a tsakãnin Sa da tsakãnin aljannu. Alhãli kuwa Lalle aljannu sun sani, "Lalle sũ, haƙĩƙa waɗanda ake halartarwa ne (a cikin wutã.)"

(159) Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke siffantãwa.

(160) Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.

(161) To, lalle, ku da abin da kuke bautãwa,

(162) Ba ku zama mãsu buwãya ba a gare Shi.

(163) Sai wanda yake mai shiga babbar wutã Jahĩm.

(164) "Kuma bãbu kõwa daga cikinmu,* fãce yanã da matsayi sananne."
* Malã'iku da sauran halitta duka kõwa yã san matsayinsa na bauta ga Allah wanda ba Ya da dã ko diya, kuma ba Ya da dangantaka da kõwa.

(165) "Kuma lalle mu, haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin sahu-sahu (dõmin ibãda)."

(166) "Kuma lalle mũ haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin tasbĩhi."

(167) Kuma lalle sũ, sun kasance sunã cẽwa,

(168) "Dã lalle munã da wani littãfi irin na mutãnen farko."

(169) "Lalle dã mun kasance bãyin Allah waɗanda aka tsarkake."

(170) Sai suka kãfirta da shi. Sabõda haka zã su sani.

(171) Kuma lalle, haƙĩƙa kalmar Mu ta gabãta ga bãyinMu, Manzanni.

(172) Lalle sũ, haƙĩƙa, sũ ne waɗanda ake taimako.

(173) Kuma lalle rundunarMu, haƙĩƙa, sũ ne marinjaya.

(174) Sabõda haka juya daga barinsu, har a wani lõkaci.

(175) Ka nũna musu (gaskiya), da haka zã su dinga gani.*
* Wannan ƙãrin bayãni ne ga abin da sũrar ke karantarwa na cewa Annabãwa sũ ne kamar rãna mai haske na asali. Mãlamai kamar taurãri suke mãsu sãmun haske daga rana su wãtsa ga dũniya kuma su kõre ɓarna. Aya ta l79 da ke tafe karfafawa ce ga ma'anar wannan.



37 - Suratu Al'safat 2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 52644
العمر : 72

37 - Suratu Al'safat Empty
مُساهمةموضوع: رد: 37 - Suratu Al'safat   37 - Suratu Al'safat Emptyالأحد 18 سبتمبر 2022, 7:58 am


(176) Shin fa, da azabarMu suke nẽman gaggãwa?

(177) To, idan ta sauka ga farfãjiyarsu, to, sãfiyar wadanda ake yi wa gargaɗi ta mũnana.

(178) Kuma ka jũya daga barinsu har a wani lõkaci.

(179) Ka nũna (musu gaskiya), da haka zã su dinga nũnãwa.

(180) Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka, Ubangijin rinjãye, daga barin abin da suke siffantãwa.

(181) Kuma aminci ya tabbata ga Manzanni.

(182) Kuma gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu.



37 - Suratu Al'safat 2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
 
37 - Suratu Al'safat
الرجوع الى أعلى الصفحة 
صفحة 1 من اصل 1
 مواضيع مماثلة
-
» 30 - Suratu Ar'rum
» 5 - Suratu Al'ma'ida
» 95 - Suratu At'tín
» 30 - Sûratu'r-Rûm
» 114 - Suratu Al'nas

صلاحيات هذا المنتدى:لاتستطيع الرد على المواضيع في هذا المنتدى
منتديات إنما المؤمنون إخوة (2024 - 2010) The Believers Are Brothers :: (English) :: The Holy Quran is translated :: Hausa-
انتقل الى: