منتديات إنما المؤمنون إخوة (2024 - 2010) The Believers Are Brothers

(إسلامي.. ثقافي.. اجتماعي.. إعلامي.. علمي.. تاريخي.. دعوي.. تربوي.. طبي.. رياضي.. أدبي..)
 
الرئيسيةالأحداثأحدث الصورالتسجيل
(وما من كاتب إلا سيبلى ** ويبقى الدهر ما كتبت يداه) (فلا تكتب بكفك غير شيء ** يسرك في القيامة أن تراه)

IZHAR UL-HAQ

(Truth Revealed) By: Rahmatullah Kairanvi
قال الفيلسوف توماس كارليل في كتابه الأبطال عن رسول الله -صلى الله عليه وسلم-: "لقد أصبح من أكبر العار على أي فرد مُتمدين من أبناء هذا العصر؛ أن يُصْغِي إلى ما يظن من أنَّ دِينَ الإسلام كَذِبٌ، وأنَّ مُحَمَّداً -صلى الله عليه وسلم- خَدَّاعٌ مُزُوِّرٌ، وآنَ لنا أنْ نُحارب ما يُشَاعُ من مثل هذه الأقوال السَّخيفة المُخْجِلَةِ؛ فإنَّ الرِّسَالة التي أدَّاهَا ذلك الرَّسُولُ ما زالت السِّراج المُنير مُدَّةَ اثني عشر قرناً، لنحو مائتي مليون من الناس أمثالنا، خلقهم اللهُ الذي خلقنا، (وقت كتابة الفيلسوف توماس كارليل لهذا الكتاب)، إقرأ بقية كتاب الفيلسوف توماس كارليل عن سيدنا محمد -صلى الله عليه وسلم-، على هذا الرابط: محمد بن عبد الله -صلى الله عليه وسلم-.

يقول المستشرق الإسباني جان ليك في كتاب (العرب): "لا يمكن أن توصف حياة محمد بأحسن مما وصفها الله بقوله: (وَمَا أَرْسَلْنَاكَ إِلَّا رَحْمَةً لِّلْعَالَمِين) فكان محمدٌ رحمة حقيقية، وإني أصلي عليه بلهفة وشوق".
فَضَّلَ اللهُ مِصْرَ على سائر البُلدان، كما فَضَّلَ بعض الناس على بعض والأيام والليالي بعضها على بعض، والفضلُ على ضربين: في دِينٍ أو دُنْيَا، أو فيهما جميعاً، وقد فَضَّلَ اللهُ مِصْرَ وشَهِدَ لها في كتابهِ بالكَرَمِ وعِظَم المَنزلة وذَكَرَهَا باسمها وخَصَّهَا دُونَ غيرها، وكَرَّرَ ذِكْرَهَا، وأبَانَ فضلها في آياتٍ تُتْلَى من القرآن العظيم.
المهندس حسن فتحي فيلسوف العمارة ومهندس الفقراء: هو معماري مصري بارز، من مواليد مدينة الأسكندرية، وتخرَّجَ من المُهندس خانة بجامعة فؤاد الأول، اشْتُهِرَ بطرازهِ المعماري الفريد الذي استمَدَّ مَصَادِرَهُ مِنَ العِمَارَةِ الريفية النوبية المَبنية بالطوب اللبن، ومن البيوت والقصور بالقاهرة القديمة في العصرين المملوكي والعُثماني.
رُبَّ ضَارَّةٍ نَافِعَةٍ.. فوائدُ فيروس كورونا غير المتوقعة للبشرية أنَّه لم يكن يَخطرُ على بال أحَدِنَا منذ أن ظهر وباء فيروس كورونا المُستجد، أنْ يكونَ لهذه الجائحة فوائدُ وإيجابيات ملموسة أفادَت كوكب الأرض.. فكيف حدث ذلك؟!...
تخليص الإبريز في تلخيص باريز: هو الكتاب الذي ألّفَهُ الشيخ "رفاعة رافع الطهطاوي" رائد التنوير في العصر الحديث كما يُلَقَّب، ويُمَثِّلُ هذا الكتاب علامة بارزة من علامات التاريخ الثقافي المصري والعربي الحديث.
الشيخ علي الجرجاوي (رحمه الله) قَامَ برحلةٍ إلى اليابان العام 1906م لحُضُورِ مؤتمر الأديان بطوكيو، الذي دعا إليه الإمبراطور الياباني عُلَمَاءَ الأديان لعرض عقائد دينهم على الشعب الياباني، وقد أنفق على رحلته الشَّاقَّةِ من مَالِهِ الخاص، وكان رُكُوبُ البحر وسيلته؛ مِمَّا أتَاحَ لَهُ مُشَاهَدَةَ العَدِيدِ مِنَ المُدُنِ السَّاحِلِيَّةِ في أنحاء العالم، ويُعَدُّ أوَّلَ دَاعِيَةٍ للإسلام في بلاد اليابان في العصر الحديث.

أحْـلامٌ مِـنْ أبِـي (باراك أوباما) ***

 

 25 - Suratu Al'furqan

اذهب الى الأسفل 
كاتب الموضوعرسالة
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 52644
العمر : 72

25 - Suratu Al'furqan Empty
مُساهمةموضوع: 25 - Suratu Al'furqan   25 - Suratu Al'furqan Emptyالخميس 15 سبتمبر 2022, 6:12 pm

25 - Suratu Al'furqan
Da sunan Allah Mai rahama
(1) Albarka ta tabbata ga wanda Ya saukar da (Littãfi) mai rarrabẽwa a kan bãwanSa, dõmin ya kasance mai gargaɗi ga halitta.

(2) wanda Yake da mulkin sammai da ƙasa kuma bai riƙi abin haihuwa ba, kuma abõkin tãrayya bai kasance a gare Shi ba a cikin mulkin Sa kuma Ya halitta dukan kowane abu, sa'an nan Ya ƙaddara shi ƙaddarãwa.

(3) Kuma suka riƙi abũbuwan bautawa, baicin Shi, bã su yin halittar kõme alhãli sũ ne ake halittãwa kuma bã su mallakar wa kansu wata cũta ko wani amfãni, kuma bã su mallakar mutuwa kuma bã su mallakar rãyarwa, kuma bã su mallakar tãyarwa.

(4) Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Wannan bã kõme ba ne fãce ƙiron ƙarya da (Muhammadu) ya ƙirƙira shi, kuma waɗansu mutãne na dabam suka taimake shi a kansa." To, lalle ne sun jẽ wa zãlunci da karkacẽwar magana.

(5) Kuma suka ce: "Tatsũniyõyi ne na farko ya rurrbũta, sai sũ ake shibtarsu a gare shi sãfe da yamma."

(6) Ka ce: "wanda Yake sanin asĩri a cikin, sammai da ƙasane Ya saukar da shi. Lalle ne shĩ Ya kasance Mai gãfara, Mai, jin ƙai."

(7) Kuma suka ce: "Mẽne ne ga wannan Manzo, yanã cin abinci, kuma yanã tafiya a cikin kãsuwanni! Don me ba a saukar da malã'ika zuwa gare shi ba, dõmin ya kasance mai gargaɗi tãre da shi?

(8) "Kõ kuwa a jẽfo wata taska zuwa gare shi, kõ kuwa wata gõna ta kasance a gare shi, yanã ci daga gare ta?" Kuma azzãlumai suka ce: "Bã ku bin kõwa, fãce mutum sihirtacce:"

(9) Ka dũba yadda suka buga maka misãlai sai suka ɓace, dõmin haka bã su iya bin tafarki.

(10) Albarka ta tabbata ga wanda idan Ya so, Yã sanya maka mafi alhẽri daga wannan (abu): gõnaki, ƙõramu na gudãna daga ƙarƙashinsu, kuma Ya sanya maka manyan gidãje.

(11) Ã'a, sun ƙaryata game da Sã'a, alhãli kuwa Mun yi tattalin wuta mai tsanani ga wanda ya ƙaryata (manzanni) game da Sa'a.

(12) Idan ta gan su daga wani wuri mai nĩsa, sai su ji sautin fushi da wani rũri nãta.

(13) Kuma idan an jẽfa su a wani wuri mai ƙunci daga gare ta, sunã waɗanda aka ɗaure ciki daidai, sai su kirãyi halaka a can.

(14) Kada ku kirãyi halaka guda, kuma ku kirãyi halaka mai yawa.

(15) Ka ce: "Shin, wancan ne mafi alhẽri, kõ kuwa Aljannar dawwama wadda aka yi wa'adi ga mãsu taƙawa? Tã zama, a gare su, sakamako da makõma."

(16) "Sunã da abin da suke so, a cikinta sunã madawwama. Wannan ya kasance wa'adi abin tambaya a kan Ubangijinka."

(17) Kuma rãnar da Yake tãra su da abin da suke bauta wa, baicin Allah sai Ya ce: "Shin kũ nekuka ɓatar, da bãyiNa, waɗannan, ko kuwa su ne suka ɓata daga hanya?"

(18) suka ce: "Tsarki ya tabbata a gare Ka, bã ya kasancẽwa agare mu, mu riƙi waɗansu majiɓinta, baicin Kai, kuma amma Kã jiyar da su dãɗi sũ da ubanninsu har suka manta da Tunãtarwa, kuma sun kasance mutãne ne halakakku."

(19) To, lalle ne, sun ƙaryata game da abin da kuke cẽwa, sabõda haka bã ku iya karkatarwa ga (maganarsu), kuma ba ku iya taimako (ga hana azãba), kuma wanda ya yi zãlunci a cikinku zã Mu ɗanɗana masa azãba mai girma.

(20) Kuma ba Mu aika ba, a gabãninka daga Manzanni, fãce lalle sũ haƙĩƙa sunã cin abinci kuma sunã tafiya a cikin kasuwõyi. Kuma Mun sanya sãshen mutãne fitina ga sãshe. Shin kunã yin haƙuri? Kuma Ubangijia Ya kasance Mai gani.

(21) Kuma waɗanda bã su fatan haɗuwa da Mu suka ce: "Don me ba a saukar da malã'ĩku ba a kanmu, kõ kuwa mu ga Ubangijinmu?" Lalle ne sun kangara a cikin rãyukansu, kuma suka yi tsaurin kai, tsaurin kai mai girma.

(22) A rãnar da suke ganin malã'iku bãbu bushãra a yinin nan ga mãsu laifi kuma sunã cẽwa,"Allah Ya kiyãshe* mu!"
* Asalin maganar shĩ ne "Tsari tsararre," wãtau muna neman tsari daga Allah, tsari tabbatacce.

(23) Kuma Muka gabãta zuwa ga abin da suka aikata daga aiki, sai Muka sanya shi ƙũra wãtsattsiya.

(24) Ma'abũta Aljanna a rãnar nan sũ ne mafi alhẽri ga matabbata kuma mafi kyaun wurin ƙailũla.

(25) Kuma a rãnar da sama take tsattsãgewa tãre da gizãgizai, kuma a saukar da malã'iku, saukarwa.



25 - Suratu Al'furqan 2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 52644
العمر : 72

25 - Suratu Al'furqan Empty
مُساهمةموضوع: رد: 25 - Suratu Al'furqan   25 - Suratu Al'furqan Emptyالخميس 15 سبتمبر 2022, 11:10 pm

(26) Mulki a rãnar nan, na gaskiya, yanã ga Mai rahama, kuma ya zama yini, a kan kãfirai, mai tsanani.

(27) Kuma rãnar da azzãlumi yake cĩzo a kan hannayensa, yanã cẽwa "Ya kaitõna! (A ce dai) na riƙi hanya tãre da Manzo!

(28) "Ya kaitõna! (A ce dai) ban riƙi wãne masõyi ba!

(29) "Lalle ne, haƙĩƙa ya ɓatar da ni daga Tunãwa a bãyan (Tunãwar) ta je mini."Kuma Shaiɗan ya zama mai zumɓulẽwa ga mutum.

(30) Kuma Manzo ya ce: "Ya Ubangijĩna! Lalle mutãnena sun riƙi wannan Alƙur'ãni abin ƙauracẽwa!"

(31) Kuma kamar haka ne, Muka sanya maƙiyi daga mãsu laifi ga kõwane Annabi. Kuma Ubangijinka Ya isa ga zama Mai Shiryarwa, kuma Mai taimako.

(32) Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Don me ba a saukar da Alƙur'ãni a kansa ba, jimla guda?" kamar wancan! Dõmin Mu ƙarfafa zũciyarka game da shi, kuma Mun jẽranta karanta shi da hankali jẽrantawa.

(33) Kuma bã zã su zo maka da wani misãli ba, fãce Mun je maka da gaskiya da mafi kyau ga fassara.

(34) Waɗanda ake tãyarwa a kan fuskõkinsu, zuwa ga Jahannama, waɗancan sũ ne mafi sharri ga wuri, kuma mafi ɓacẽwa ga hanya.

(35) Kuma lalle ne, Mun bai wa Mũsã Littãfi, kuma Mun sanya ɗan'uwansa, Hãrũna, mataimaki tãre da shi.

(36) Sai Muka ce: "Ku tafi, kũ biyu, zuwa ga mutãnen nan waɗanda suka ƙaryata game da ãyõ yin Mu." sai Muka darkãke su, darkãkewa.

(37) Kuma mutãnen Nũhu, a lõkacin da suka ƙaryata Manzanni, Muka nutsar da su, kuma Muka sanya su wata ãya ga mutãne, kuma Muka yi tattalin azãba mai raɗaɗi ga azzãlumai.

(38) Da Ãdãwa da Samũdãwa, da mutanen Rassi, da waɗansu al'ummomi, a tsakãnin wannan, mãsu yawa.

(39) Kuma kõwannensu Mun buga masa misãlai, kuma kõwanne Mun halakar da (shi), halakarwa.

(40) Kuma lalle ne, haƙĩƙa, (¡uraishi) sun jẽ a kan alƙaryar nan wadda aka yi wa ruwa, ruwan azãba. Shin, ba su kasance sun gan ta ba? Ã'a, sun kasance bã su ƙaunar tãyarwa (a ¡iyãma).

(41) Kuma idan sun gan ka, bã su rikon ka fãce da izgili, (sunã cẽwa) "Shin, wannan ne wanda Allah Ya aiko, Manzo?

(42) "Lalle ne, yã yi kusa ya ɓatar da mu daga Ubangijinmu, in bã dõmin da muka yi haƙuri a kansu ba."Kuma zã su sani a lõkacin da suke ganin azãba, wãne ne mafi ɓacẽwa ga hanya!

(43) Shin, kã ga wanda ya riƙi UbangiJinsa son zuciyarsa? shin, to, kai ne ke kasancẽwa mai tsaro a kansa?

(44) Ko kanã zaton cẽwa mafi yawansu sunã ji, kõ kuwa sunã hankali? sũ ba su zama ba fãce dabbõbin gida* suke. Ã'a, sũ ne mafi ɓacẽwa ga hanya.
* Dabbõbin gida sun fi rashin hankali bisa ga na dãji, dõmin na dãji na gudun abin da zai cũce sũ su kuma dabbõbin gida sunã zamã tãre da mãsu cin su, su shã nõnonsu kuma su kashe 'ya'yansu.

(45) Ashe, ba ka dũba ba zuwa ga Ubangijinka, yadda Ya miƙe inuwa? Kuma dã Yã so dã Yã bar ta tsaye cif, sa'an nan Muka sanya rãnã mai nũni a kanta.

(46) Sa'an nan Muka karɓe ta (inuwa) zuwa gare Mu, karɓa mai sauƙi.

(47) Kuma shĩ ne wanda Ya sanya muku dare ya zama tũfa da barci ya zama hũtãwa, dã yini ya zama lokacin tãshi (kamar Tashin ¡iyãma).

(48) Kuma Shi ne Ya aika iskõkin bushãra gaba ga rahamar Sa, kuma Muka saukar da ruwa mai tsarkakẽwa daga sama.

(49) Dõmin Mu rãyar, game da shi, gari matacce, kuma Mu shayar da shi dabbõbi da mutãne mãsu yawa daga abin da Muka halitta.

(50) Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun sarrafa* shi (Alƙur'ãni) a tsakãninsu, dõmin su yi tunãni, sai dai mafi yawan mutãnen sun ƙi fãce kãfirci.
* Sarrafa Alƙur'ãni watau Munsanya shi a cikin misãlai dabam-dabam dõmin su gani kõ su ji, su yi tunãni, amma sai suka ƙi saurãren, sai dai kãfirci.



25 - Suratu Al'furqan 2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 52644
العمر : 72

25 - Suratu Al'furqan Empty
مُساهمةموضوع: رد: 25 - Suratu Al'furqan   25 - Suratu Al'furqan Emptyالخميس 15 سبتمبر 2022, 11:11 pm


(51) Kuma da Mun so, haƙĩƙa dã Mun aika da mai gargaɗi* a ciƙin kõwace alƙarya.
* Dã Muna so dã Mun aika wa kõwane gari da Annabinsa mai yi musu gargaɗi, amma ba Mu so haka ba, sai Muka aika ka kai ɗaya zuwa ga dukan dũniya dõmin Mu ɗaukaka darajarka.

(52) Sabõda haka kada ka yi ɗã'ã ga kãfirai, ka yãke su, da shi, yãƙi mai girma.

(53) Kuma shĩ ne Ya gauwaya tẽkuna biyu, wannan mai dãdi, mai sauƙin haɗiya, kuma wannan gishiri gurbatacce, kuma Ya sanya wani shãmaki a tsakãninsu da kãriya mai shãmakacẽwa.

(54) Kuma Shi ne Ya halitta mutum daga ruwa, sai Ya sanya shi nasaba da surukuta, kuma Ubangijinka Ya kasance Mai ĩkon yi.

(55) Kuma sunã bauta wa, baicin Allah, abin da bã ya amfãnin su, kuma bã ya cũtar su, kuma kãfiri ya kasance mai taimakon (Shaiɗan) a kan Ubangijinsa.

(56) Ba Mu aika ka ba sai kana mai bãyar da bushãra, kuma mai gargaɗi.

(57) Ka ce: "Bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa fãce wanda ya so ya riƙi wata hanya* zuwa ga Ubangijinsa."
* Bã na neman wata ijãra sabõda inã karanta muku Alƙur'ãni, ko, sabõda inã shiryar da ku, amma wanda ya so ya ciyar da dũkiyarsa dõmin Allah, to, shĩ kam bã ni hana shi, sai ya ciyar. Kuma mun sani Annabi ba ya cin sadaka. A kan haka ne waɗansu Malamai suka hana karɓar ijãraa kan karantar da Alƙur'ãni. Abin da yake Mu'utamadi ya halatta sabõda Hadĩsi, kumada sauƙaƙewa ga aikin yãɗa addĩnin Musulunci. Hukumci yanã canzawa da canzãwar hãli.

(58) kuma ka dõgara a kan Rãyayye wanda bã Ya mutuwa, kuma ka yi tasbĩhi game da gõde Masa. Kuma Yã isa zama Mai ƙididdigewa ga laifuffukan bãyinSa.

(59) Wanda Ya halitta sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, a cikin kwãnuka shida sa'an nan Yã daidaitu a kan Al'arshi Mai rahama, sai ka tambayi mai bãyar da lãbãri game da Shi.
* Idan kanã son sanin siffofin Allah, sai ka tambayi Allah, dõmin bãbu wanda ya san shi, sani na gani balle ya iya gaya maka yadda Yake, sabõda haka siffõfin Allah da sũnãyenSa duka bã a yin shisshigi a gare su, sai yadda aka ji su daga Manzon Allah.Tauƙifiyyai ne.

(60) Idan aka ce musu, "Ku yi sujada ga Mai rahama." Sai su ce: "Mene ne Mai rahama? Ashe zã mu yi sujada ga abin da kuke umurnin mu?"Kuma wannan (magana* ta ƙãra musu gudu.
* Kõ sun san gaskiyar abin daaka kira su zuwa gare shi, bã zã su yi ɗã'ã ba, dõmin wai sunã jin nauyi su karɓi umurni daga wani mutum.

(61) Albarka ta tabbata ga Wanda Ya sanya masaukai* (na tafiyar wata) a cikin sama kuma Ya sanya fitila da watã mai haskakewa a cikinta.
* Taurãri bakwai waɗandaake cewa matafa su ne Mirrikh da Zahra da Uɗãrid da Ƙamar, wãtau Watã, da Rãnã, da Mushtari, da Zuhal; Kuma burjõji sũ gõma sha biyu ne, su ne Himlu, da Saur, da jauzã'a, da Sirtãn, da Asad, da Sunbula da Mĩzãn da Aƙrab, da Ƙausu, da Jadyu,da Dalwu da Hũt.

(62) Kuma Shĩ ne wanda Ya sanya dare da yini a kan mayẽwa, ga wanda yake son ya yi tunãni, kõ kuwa ya yi nufin ya gõde.

(63) Kuma bãyin Mai rahama* su ne waɗanda ke yin tafiya a kan ƙasa da sauƙi, kuma idan jãhilai sun yi musu magana, sai su ce: "Salãma" (a zama lafiya).
* Bãyan da ya ambaci masu ƙin su yi sujada ga Mai rahama sabõda kangararsu sai kumaya fãra ambaton siffofin mãsu son yin sujada gare shi, Yãyi musu sunã Bãyin Mai rahama.

(64) Kuma waɗanda suke kwãna sunã mãsu sujada da tsayi a wurin Ubangijinsu.

(65) Kuma waɗanda suke cẽwa "Ya Ubangijinmu! Ka karkatar da azãbar Jahannama daga gare mu. Lalle ne, azãbarta tã zama tãra*
* Garama, ita ce uƙũba da dũkiya mai lazimtar wanda aka aza wa ita. Da Hausa anã cewa tãra. Watau azãba da zã tafi ƙarfin jiki har tanã neman wani abu wanda ya danganci jiki. Kõ mene ne, kamar dũkiya.

(66) "Lalle ne ita ta mũnana ta zama wurin tabbata da mazauni."

(67) Kuma waɗanda suke idan sun ciyar, bã su yin ɓarna, kuma bã su yin ƙwauro, kuma (ciyarwarsu) sai ta kasance a tsakãnin wancan da tsakaitãwa.

(68) Kuma waɗanda bã su kiran wani ubangiji tãre da Allah, kuma bã su kashe rai wanda Allah Ya haramta fãce da hakki kuma bã su yin zina. Kuma wanda ya aikata wancan, zai gamu da laifuffuka,

(69) A riɓanya masa azãba a Rãnar ¡iyãma. Kuma ya tabbata a cikinta yanã wulakantacce.

(70) Sai wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aiki na ƙwarai to, waɗancan Allah Yanã musanya miyãgun ayyukansu da mãsu kyau. Allah Ya kasance Mai gãfara Mai jin ƙai.

(71) Kuma wanda ya tũba,* kuma ya aikata aiki mai kyau, to, lalle ne sai ya tũba zuwa gaAllah.
* Wanda ya tũba daga kõwane irin zunubi, waɗanda aka ambata da waɗanda ba a ambata ba, kõ dã laifinsa kãfirci ne, to, sai ya tũba zuwa ga Allah kawai, tũba ta gaskiya, lalle ne Allah zai karɓi tũbarsa matuƙar ajalin mutuwa bai sauka a kansa ba.

(72) Kuma waɗanda suke bã su yin shaidar zur, kuma idan sun shũɗe ga yasassar magana sai su shũɗe suna mãsu mutumci.

(73) Kuma waɗanda suke idan an tunãtar da su da ãyõyin Allah, bã su saukar da kai, sunã kurame* da makãfi.
* Idan an yi musu wa'azi zã su saurãre shi, kuma su yi aiki da shi. Bã zã su zama kurãme ba ga karɓar gaskiya, kuma bã zã su zama makãfi ba gaganin hanyar shiryawa.

(74) Kuma waɗanda suke cẽwa "Yã Ubangijinmu! Ka bã mu sanyin idãnu daga mãtanmu da zũriyarmu, kuma Ka sanya* mu shũgabanni ga mãsu taƙawa."
* Anã son mutum ya rõƙi Allah Ya ɗaukaka shi, shi da zuriyarsa, ɗaukakar addini, kamar yadda Annabi Ibrãhĩm ya yi rõƙon haka. Kuma wannan yanã cikin sifõfin Bãyin Mai rahama.

(75) Waɗannan anã sãka musu da bẽne, sabõda haƙurin da suka yi, kuma a haɗa su, a cikinsa, da gaisuwa da aminci.



(76) Suna madawwama a cikinsa. Ya yi kyau ga zama matabbaci da mazauni.

(77) Ka ce: "Ubangijĩna ba Ya kula da ku in bã dõmin addu'arku* ba. To, lalle ne, kun ƙaryata, sabõda haka al'amarin zã ya zama malizimci."
* Wannan yanã nũna cewa Allah Yanã son bãyinSa mãsu rõƙonsa. Kuma Yanã son a rõkeShi ƙwarai.



25 - Suratu Al'furqan 2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
 
25 - Suratu Al'furqan
الرجوع الى أعلى الصفحة 
صفحة 1 من اصل 1
 مواضيع مماثلة
-
» Interpretation of Surat: ALFURQAN
» 114 - Suratu Al'nas
» 6 - Suratu Al'an'am
» 5 - Suratu Al'ma'ida
» 103 - Suratu Al'asr

صلاحيات هذا المنتدى:لاتستطيع الرد على المواضيع في هذا المنتدى
منتديات إنما المؤمنون إخوة (2024 - 2010) The Believers Are Brothers :: (English) :: The Holy Quran is translated :: Hausa-
انتقل الى: