منتديات إنما المؤمنون إخوة (2024 - 2010) The Believers Are Brothers

(إسلامي.. ثقافي.. اجتماعي.. إعلامي.. علمي.. تاريخي.. دعوي.. تربوي.. طبي.. رياضي.. أدبي..)
 
الرئيسيةالأحداثأحدث الصورالتسجيل
(وما من كاتب إلا سيبلى ** ويبقى الدهر ما كتبت يداه) (فلا تكتب بكفك غير شيء ** يسرك في القيامة أن تراه)

IZHAR UL-HAQ

(Truth Revealed) By: Rahmatullah Kairanvi
قال الفيلسوف توماس كارليل في كتابه الأبطال عن رسول الله -صلى الله عليه وسلم-: "لقد أصبح من أكبر العار على أي فرد مُتمدين من أبناء هذا العصر؛ أن يُصْغِي إلى ما يظن من أنَّ دِينَ الإسلام كَذِبٌ، وأنَّ مُحَمَّداً -صلى الله عليه وسلم- خَدَّاعٌ مُزُوِّرٌ، وآنَ لنا أنْ نُحارب ما يُشَاعُ من مثل هذه الأقوال السَّخيفة المُخْجِلَةِ؛ فإنَّ الرِّسَالة التي أدَّاهَا ذلك الرَّسُولُ ما زالت السِّراج المُنير مُدَّةَ اثني عشر قرناً، لنحو مائتي مليون من الناس أمثالنا، خلقهم اللهُ الذي خلقنا، (وقت كتابة الفيلسوف توماس كارليل لهذا الكتاب)، إقرأ بقية كتاب الفيلسوف توماس كارليل عن سيدنا محمد -صلى الله عليه وسلم-، على هذا الرابط: محمد بن عبد الله -صلى الله عليه وسلم-.

يقول المستشرق الإسباني جان ليك في كتاب (العرب): "لا يمكن أن توصف حياة محمد بأحسن مما وصفها الله بقوله: (وَمَا أَرْسَلْنَاكَ إِلَّا رَحْمَةً لِّلْعَالَمِين) فكان محمدٌ رحمة حقيقية، وإني أصلي عليه بلهفة وشوق".
فَضَّلَ اللهُ مِصْرَ على سائر البُلدان، كما فَضَّلَ بعض الناس على بعض والأيام والليالي بعضها على بعض، والفضلُ على ضربين: في دِينٍ أو دُنْيَا، أو فيهما جميعاً، وقد فَضَّلَ اللهُ مِصْرَ وشَهِدَ لها في كتابهِ بالكَرَمِ وعِظَم المَنزلة وذَكَرَهَا باسمها وخَصَّهَا دُونَ غيرها، وكَرَّرَ ذِكْرَهَا، وأبَانَ فضلها في آياتٍ تُتْلَى من القرآن العظيم.
المهندس حسن فتحي فيلسوف العمارة ومهندس الفقراء: هو معماري مصري بارز، من مواليد مدينة الأسكندرية، وتخرَّجَ من المُهندس خانة بجامعة فؤاد الأول، اشْتُهِرَ بطرازهِ المعماري الفريد الذي استمَدَّ مَصَادِرَهُ مِنَ العِمَارَةِ الريفية النوبية المَبنية بالطوب اللبن، ومن البيوت والقصور بالقاهرة القديمة في العصرين المملوكي والعُثماني.
رُبَّ ضَارَّةٍ نَافِعَةٍ.. فوائدُ فيروس كورونا غير المتوقعة للبشرية أنَّه لم يكن يَخطرُ على بال أحَدِنَا منذ أن ظهر وباء فيروس كورونا المُستجد، أنْ يكونَ لهذه الجائحة فوائدُ وإيجابيات ملموسة أفادَت كوكب الأرض.. فكيف حدث ذلك؟!...
تخليص الإبريز في تلخيص باريز: هو الكتاب الذي ألّفَهُ الشيخ "رفاعة رافع الطهطاوي" رائد التنوير في العصر الحديث كما يُلَقَّب، ويُمَثِّلُ هذا الكتاب علامة بارزة من علامات التاريخ الثقافي المصري والعربي الحديث.
الشيخ علي الجرجاوي (رحمه الله) قَامَ برحلةٍ إلى اليابان العام 1906م لحُضُورِ مؤتمر الأديان بطوكيو، الذي دعا إليه الإمبراطور الياباني عُلَمَاءَ الأديان لعرض عقائد دينهم على الشعب الياباني، وقد أنفق على رحلته الشَّاقَّةِ من مَالِهِ الخاص، وكان رُكُوبُ البحر وسيلته؛ مِمَّا أتَاحَ لَهُ مُشَاهَدَةَ العَدِيدِ مِنَ المُدُنِ السَّاحِلِيَّةِ في أنحاء العالم، ويُعَدُّ أوَّلَ دَاعِيَةٍ للإسلام في بلاد اليابان في العصر الحديث.

أحْـلامٌ مِـنْ أبِـي (باراك أوباما) ***

 

 17 - Suratu Al'israa

اذهب الى الأسفل 
كاتب الموضوعرسالة
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 52644
العمر : 72

17 - Suratu Al'israa  Empty
مُساهمةموضوع: 17 - Suratu Al'israa    17 - Suratu Al'israa  Emptyالخميس 15 سبتمبر 2022, 5:12 pm

17 - Suratu Al'israa
Da sunan Allah Mai rahama
(1) Tsarki ya tabbata ga wanda Ya yi tafiyar dare* da bãwanSa da dare daga Masallaci mai alfarma zuwa ga Masallaci mafi nĩsa** wanda Muka sanya albarka a gefensa dõmin Mu nũna masa daga ãyõyinMu. Lalle ne Shi shĩ ne Mai ji, Mai gani.
* Isrã'i, shi ne tafiyar dare da Allah Ya yi da Annabi daga Makka zuwa Baitil Maƙadis. Sa'an nan Mi'iraji zuwa sama inda aka ba shi sallõli. ** Muƙarana a tsakãnin Masjidil Harãm watau tsararre daga a yãki mutãnensa da Masjidil Aƙsã wanda ba tsararre ba. Isrã'i da Mi'irãji sun fi Miƙãtin Mũsã da gãnãwarsa da Ubangiji a Ɗũr-Sĩna'a.

(2) Kuma Mun bai wa Mũsã* littafi, kuma Mun sanya shi shiriya ga Banĩ Isrã'ila, cẽwa kada ku riƙi wani wakĩli baici Na.
* Tsakãnin Bãwan Allah Muhammadu da Mũsã, kuma an aiko Mũsã ga Banĩ Isrã'ila kawai, kuma Nũhu an ce masa bãwa amma ba a jingina shi kamar yadda aka jingina bawanSa ba. Sa'an nan kuma Jingina Yahũdu ga Nũhu ya daidaita su da sauran mutãne wajen da'awar ɗaukaka da nasaba.

(3) Zuriyar waɗanda Muka ɗauka tãre da Nũhu. Lalle ne shi ya kasance wani bãwa mai gõdiya.

(4) Kuma Mun hukunta zuwa ga Bani Isrã'ĩla a cikin Littãfi, cewa lalle ne, kunã yin ɓarna a cikin ƙasa sau biyu, kuma lalle ne kunã zãlunci, zãlunci mai girma.

(5) To idan wa'adin na farkonsu yajẽ, za Mu aika, a kanku waɗansu bãyi* Nãmu, ma'abũta yãƙi mafĩ tsanani, har su yi yãwo a tsakãnin gidãjenku, kuma yã zama wa'adi abin aikatawa.
* Sun yi fasãdi da barin aiki da Taurãti, sabõda haka aka aika Jãlũta a kansu. Ya kashe su kuma ya kãma zuriyarsu.

(6) Sa'an nan kuma Mu nwayar da ɗauki a gare ku a kansu, kuma Mu taimake ku da dũkiyõyi da ɗiya kuma Mu sanya ku mafiya yawan mãsu fita yãƙi.

(7) Idan kun kyautata, kun kyautata dõmin kanku, kuma idan kun mũnana to dõmĩnsu. Sa'an nan idan wa'adin na ƙarshe* ya jẽ, (za su je) dõmin su baƙanta fuskokinku, kuma su shiga masallaci kamar yadda suka shige shi a farkon lõkaci, kuma dõmin su halakar da abin da suka rinjaya a kansa, halakarwa.
* Suka yi fasãdi marra ta biyu da kashe Zakariyya da Yahaya, sai aka aika musu da Bukht Nasar daga Bãbila ya karkashe su, kuma ya kãma zuriyarsu, kuma ya rũshe Baitil Maƙadis. Waɗannan lãbaru biyu na ɓarnar Banĩ Isrã'ila sunã cikin bãyar da lãbaru ga gaibi. Idan an daidaita su da lãbarun gaibi waɗanda Alƙur'ãni ya faɗã, waɗansu suka auku kuma waɗansu sunã ta aukuwa zã a san falalar Alƙur'ãni a kan Taurãti kamar yadda ya bayyana cewa Attaura ta yi kira zuwa ga tauhidi da shiriya, sa'an nan ya bayyana abũbuwan da Alƙur'ãnĩ yake karantarwa daga ãyã ta 9 zuwa ga ãyã ta 38 inda ya tãra hãlãyen ƙwarai kuma ya kõre mũnãna.

(8) Akwai tsammãnin Ubangijinku Ya yi muku rahama. Kuma idan kun sãke Mu sãke. Kuma Mun sanya Jahannama matsara ga kãfirai.

(9) Lalle ne wannan Alƙur'ãni yanã shiryarwa ga (hãlayen) waɗanda suke mafi daidaita* kuma yanã bãyar da bushãra ga mũminai waɗanda suke aikata ayyuka na ƙwarai (cẽwa) "Lalle ne sunã da wata ijãra. mai girma."
* Bãyan ya faɗi abũbuwan da Attaura ta karantar, ya ce: "Alƙur'ãni yanã shiryarwa zuwa ga hãlãyen da suka fi daidaita daga abin da Attaura ta karantar." Sa'an nan ya ci gaba da bayãnin abũbuwan da Alƙur'ãni yake karantarwa.

(10) Kuma lalle ne, waɗanda ba su yin ĩmãni da Lãhira, Mun yimusu tattalin wata azãba mai raɗaɗi.

(11) Kuma mutum yanã* yin addu'a da sharri kamar addu'arsa da alhẽri, kuma mutum ya kasance mai gaggãwa.
* Alƙur'ani yanã shiryar da mutum har ga yadda yake yin addu'a dõmin kada ya yi wa kansa addu'a ta sharri alhãli kuwa yanã nufin ya yi alhħri dõmin an halicci mutum da son gaggãwa.

(12) Kuma Mun sanya dare da rãna, ãyõyi biyu, sa'an nan Muka shãfe ãyar dare, kuma Muka sanya ãyar rãna mai sanyãwa a yi gani, dõmin ku nẽmi falala daga Ubangijinku, kuma dõmin ku san ƙidãyar shẽkara da lissafi. Kuma dukan kõme Mun bayyana shi daki-dakin bayyanãwa.

(13) Kuma kõwane mutum Mun lazimta masa abin rekõdinsa a cikin wuyansa, kuma Mu fitar masa a Rãnar ¡iyãma da littãfi wanda zai haɗu da shi buɗaɗɗe.

(14) "Karanta Littãfinka. Ranka ya isa ya zama mai hisãbi a kanka a yau."

(15) Wanda ya nẽmi shiryuwa, to, ya nẽmi shiryuwa ne dõminkansa kawai kuma wanda ya ɓace, to, ya ɓace ne a kansa kawai kuma rai mai ɗaukar nauyi bã ya ɗaukar nauyin wani ran, kuma ba Mu zama mãsu yin azãba ba, sai Mun aika wani Manzo.

(16) Kuma idan Mun yi nufin Mu halakar da wata alƙarya, sai Mu umurci mawadãtanta, har su yi fasadi a cikinta, sa'an nan maganar azãba ta wajaba a kanta, sa'an nan Mu darkãke ta, darkãkẽwa.

(17) Kuma da yawa Muka halakar da al'ummomi a bãyan Nũhu. Kuma Ubangijinka Ya isa ya zama Mai ƙididdigewa ga zunubban bãyinSa, Mai gani.

(18) Wanda ya kasance yanã nufin mai gaggãwa, sai Mu gaggauta masa a cikinta, abin da Muke so ga wanda Muke nufi, sa'an nan kuma Mu sanya masa Jahannama, ya ƙõnu da ita, yanã abin zargi kuma abin tunkuɗewa.

(19) Kuma wanda ya nufi Lãhira, kuma ya yi aiki sabõda ita irin aikinta alhãli kuwa yanã mũmĩni, to, waɗannan aikinsu ya kasance gõdadde.

(20) Dukkansu Munã taimakon waɗannan da waɗancan daga kyautar Ubangijinka, kuma kyautar Ubangijinka ba ta kasance hananna ba.

(21) Ka duba yadda Muka fĩfĩtar da sãshensu a kan sãshe! Kuma lalle ne Lãhira ce mafi girman darajõji, kuma mafi girman fĩfĩtãwa.

(22) Kada ka sanya wani abin bautawa na daban tãre da Allah har ka zauna kana abin zargi, yarɓaɓɓe.

(23) Kuma Ubangijinka Ya hukunta kada ku bauta wa kõwa fãce Shi, kum game da mahaifa biyu ku kyautata kyautatawa, ko dai ɗayansu ya kai ga tsũfa a wurinka ko dukansu biyu, to, kada ka ce musu 'tir' kuma kada ka tsãwace su kuma ka faɗa musu magana mai karimci.

(24) Kuma ka sassauta musu fikãfikan tausasãwa na rahama. Kuma ka ce: "Ya Ubangijina! Ka yi musu rahama, kamar yadda suka yi rẽnõna, ina ƙarami."

(25) Ubangijin ku ne Mafi sani ga abin da yake a cikin rãyukanku. Idan kun kasan ce sãlihai to lalle ne shĩ Ya kasance ga mãsu kõmawa gare Shi, Mai gãfara.



17 - Suratu Al'israa  2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 52644
العمر : 72

17 - Suratu Al'israa  Empty
مُساهمةموضوع: رد: 17 - Suratu Al'israa    17 - Suratu Al'israa  Emptyالخميس 15 سبتمبر 2022, 5:12 pm


(26) Kuma ka bai wa ma'abũcin zumunta hakkinsa* da miskĩna da ɗan hanya. Kuma kada ka bazzara dũkiyar ka, bazzarãwa.
* Hakkin zumunta shi ne alheri da sãdar da zumunta. Hakkin miskini da ɗan hanya zakka da sadakar taɗawwa'i da liyãfar kwana uku ga bãƙo bisa al'ada da alheri, bã bisa ɓarna da kallafãwa ba.

(27) Lalle ne mubazzarai sun kasance 'yan'uwan shaiɗanu. Kuma Shaiɗan ya kasance ga Ubangijinsa, mai yawan kãfirci.

(28) Ko dai ka kau da kai daga gare su dõmin nẽman rahama daga Ubangijinka, wadda kake fãtanta, to sai ka gaya musu magana mai laushi.

(29) Kuma kada ka sanya hannunka ƙuƙuntacce zuwa ga wuyanka, kuma kada ka shimfiɗa shi dukan shimfiɗãwa har ka zama abin zargi, wanda ake yanke wa.*
* Kada ka zama marõwaci a zarge ka, kuma kada ka zama almubazzari ka rasa mutãne, su yanke daga gare ka.

(30) Lalle ne Ubangijinka Yanã shimfiɗa arzĩki ga wanda Yake so, kuma Yanã ƙuƙuntãwa. Lalle Shi, Yã kasance Mai sani ga bãyinSa, Mai gani.

(31) Kuma kada ku kashe 'yã'yanku dõmin tsõron talauci. Mu ne ke arzũta su, su da ku. Lalle ne kashe su yã kasance kuskure babba.

(32) Kuma kada ku kusanci zina. Lalle ne ita ta kasance alfãsha ce kuma tã mũnãna ga zama hanya.

(33) Kuma kada ku kashe rai wanda Allah Ya haramta fãce da haƙƙi, kuma wanda aka kashe, yanã wanda aka zãlunta to, haƙĩƙa Mun sanya hujja ga waliyyinsa, sai dai kada ya ƙẽtare haddi a cikin kashẽwar. Lalle shĩ ya kasance wanda ake taimako.

(34) Kuma kada ku kusanci dũkiyar marãya fãce dai da sifa wadda take ita ce mafi kyau, har ya isa ga mafi ƙarfinsa. Kuma ku cika alkawari. Lalle alkawari yã kasance abin tambayãwa ne.

(35) Kuma ku cika mũdu idan kun yi awo, kuma ku auna nauyi da sikẽli madaidaici. Wancan ne mafi alhẽri, kuma mafi kyau ga fassara.

(36) Kuma kada ka bi abin da bã ka da ilmi game da shi. Lalle ne jĩ da gani da zũciya, dukan waɗancan (mutum) yã kasance daga gare shi wanda ake tambaya.

(37) Kuma kada ka yi tafiya a cikin ƙasa da alfahari. Lalle kai bã zã ka hũda ƙasa ba kuma bã zã ka kai a duwãtsu ba ga tsawo.

(38) Dukan wancan mli mũninsa yã kasance abin ƙyãma a wurin Ubangijin ka.

(39) Wancan yãnã daga abin da Ubangijinka Ya yi wahayi zuwa gare ka na hikima. Kuma kada ka sanya wani abin bautãwa na daban tãre da Allah har a jẽfa ka a cikin Jahannama kanã wanda ake zargi, wanda ake tunkuɗẽwa*
* Wannan shĩ ne ƙarshen muƙãrana tsakãnin shiryarwar da Alƙur'ãni ya kãwo wa dũniya da abin da Attaura ta kãwo wa Banĩ Isrã'ĩla. Kuma akwai daidatãwa a cikinsu a tsakãnin hãlãye mãsu kyau da kĩshiyõyinsu, watau hãlãye mãsu mũni.

(40) Shin fa, Ubangijinku Ya zãɓe ku da ɗiya maza ne, kuma Ya riƙi 'ya'ya mãta daga malã'iku?* Lalle ne kũ, haƙĩƙa, kunã faɗar magana mai girma!
* Farkon muƙãrana a tsakãnin al'ãdun mushirikai da shiryarwar Alƙur'ãni dõmin gyãra tunãninsu ga karɓar ĩmãnin tauhĩdi.

(41) Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun sarrafa bayãni a cikin wannan Alƙur'ãni dõmin su yi tunãni, kuma bã ya ƙãra musu kõme fãce gudu.

(42) Ka ce: "Dã akwai waɗansu abũbuwan bautãwa tãre da shi, kamar yadda suka faɗa, a lõkacin, dã (abũbuwan bautãwar) sun nẽmi wata hanya* zuwa ga Ma'abũcin Al'arshi."
* Dã su abõkan tãrayyar sun nemi hanya zuwa ga Allah dõmin su yãƙe shi sabõda Ya ce Al'arshi Tãsa ce, Shi kaɗai, dõmin su sãmi nãsu rabon, sabõda Al'arshi tã haɗiye kõme, har da su.

(43) TsarkinSa yã tabbata kuma Ya ɗaukaka daga abin da suke faɗã, ɗaukaka mai girma.

(44) Sammai bakwai da ƙasa da wanda yake a cikinsu sunã yi Masa tasbĩhi. Kuma bãbu wani abu fãce yanã tasbĩhi game da gõde Masa, kuma amma ba ku fahimtar tasbĩhinsu. Lalle ne shĩ, Ya kasance Mai haƙuri ne, Mai gãfara.

(45) Kuma idan ka karanta Alƙur'ani,* sai Mu sanya a tsakãninka da tsakanin waɗanda bã su yin ĩmãni da Lãhira wani shãmaki mai suturcẽwa.
* Mushirikai jahilai ne, ba su iya ɗaukar jãyayyar magana, sabõda sun fi kusanta zuwa ga dabbõbi ga tunãninsu, bisa gare su zuwa ga mutãne, kõ da yake sauran jikinsu na mutãne ne. Sabõda haka a kõ yaushe sunã kusa ga faɗan tãyar da hankali da dõke-dõke. Sabõda haka Allah Ya sanya tsari ga AnnabinSa da wanda ya bi hanyar Annabin, wajen shiryar da mutãne game da karanta Alƙur'ãni. Bã zã su iya fãɗa mai karanta Alƙur'ãni da dũka ba, kuma tsõronsa suke ji dõmin kwarjinin Alƙur'ãni.

(46) Kuma Mu sanya marufai a kan zukãtansu dõmin kada su fahimce shi, da, wani nauyi a cikin kunnuwansu, kuma idan ka ambaci Ubangijinka, a cikin Alƙur'ãni shĩ kaɗai, sai su jũya a kan bayayyakinsu dõmin gudu.

(47) Mũ ne Mafi sani game da abin da suke saurãre da shi a lõkacin da suke yin saurãren zuwa gare ka, kuma a lõkacin da suke mãsu gãnãwa a tsakãninsu a lõkacin da azzãlumai suke cẽwa, "Bã ku biyar kõwa fãce wani namiji sihirtacce."

(48) Ka dũba yadda suka buga maka misãlai, sai suka ɓace bã su iya sãmun hanya.

(49) Kuma suka ce: "Shin, idan mun kasance ƙasũsuwa da, niƙaƙƙun gaɓãɓuwa ashe, lalle ne mũ haƙĩƙa, waɗanda ake tãyarwa ne a wata halitta sãbuwa?"

(50) Ka ce: "Ku kasance duwãtsu ko kuwa baƙin ƙarfe."



17 - Suratu Al'israa  2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 52644
العمر : 72

17 - Suratu Al'israa  Empty
مُساهمةموضوع: رد: 17 - Suratu Al'israa    17 - Suratu Al'israa  Emptyالخميس 15 سبتمبر 2022, 5:13 pm


(51) "Kõ kuwa wata halitta daga abin da yake da girma a cikin ƙirazanku." To zã su ce "Wãne ne zai mayar da mu?" Ka ce: "Wanda Ya ƙaga halittarku a fabkon lõkaci." To, zã su gyaɗa kansu zuwa gare ka, kuma sunã cẽwa, "A yaushene shi?" Ka ce: "Akwai tsammãninsa ya kasance kusa."

(52) "A rãnar da Yake kiran ku, sa'an nan ku riƙa karɓãwa game dã gõde Masa, kuma kunã zaton ba ku zauna ba fãce kaɗan."

(53) Kuma ka cẽ wa bãyiNa, su faɗi kalma* wadda take mafi kyau. Lalle ne Shaiɗan yanã sanya ɓarna a tsakãninsu. Lalle ne Shaiɗan ya kasance ga mutum, maƙiyi bayyanan ne.
* Ka ce wa bãyĩNa, mutãne, idan sunã magana su auna kalmõmin da suke zance da su, sa'an nan su riƙa amfãni da kalma mafi kyãwo dõmin kada shaiɗan ya sãmi mashiga daga maganarsu zuwa ga zukãtansu, ya sanya ɓarna a tsakãninsu.

(54) Ubangijinku ne Mafi sani game da ku. Idan Ya so, zai yi muku rahama, kõ kuwa idan Yã so zai azabtãku. Kuma ba Mu aika ka kanã wakĩli a kansu ba.

(55) Kuma Ubangijinka ne Mafi sani game da wanda yake a cikin sammai da ƙasa. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun fĩfĩta sãshen Annabãwa a kan sãshe kuma Mun bai wa Dãwũda zabũra.*
* Muƙãrana a tsakãnin Annabãwa. Allah Yã fĩfĩta waɗansu a kan waɗansu. Falalar Dãwũda a kan waɗansu Annabãwa da Zabũra ne to inã fĩfĩkon wanda aka bai wa Alƙur'ãni mafĩfĩcin littafi da sauran Annabãwa?.

(56) Ka ce: "Ku kirãyi waɗanda kuka riya, baicinSa." To, ba su mallakar kuranyẽwar cũta daga gare ku, kuma haka jũyarwa."*
* Bã zã su iya jũyar da cũta daga gare ku zuwa ga wani ko kuwa daga wani zuwa gare ku ba.

(57) Waɗancan, waɗanda suke kiran*, sunã nẽman tsãni zuwa ga Ubangijinsu. Waɗanne ne suke mafĩfĩta a kusanta? Kuma sunã fãtan sãmun rahamarSa, kuma sunã tsõron azãbarSa. Lalle ne azãbar Ubangijinka ta kasance abar tsõro ce.
* Waɗanda kãfirai ke neman tawassuli da su zuwa ga Allah, sũ ma sunã neman abin da zai sãdar da su zuwa ga Allah, sabõda haka bãbu bambanci a tsakãnin mai tawassuli da wanda ake tawassulin da shi ga kusanta zuwa ga Allah. Bãbu mai kusanta zuwa ga Allah sai da taƙawa ga ibãdarSa kawai.

(58) Kuma bãbu wata alƙarya fãce, Mu ne mãsu halaka ta a gabãnin Rãnar ¡iyãma kõ kuwa Mũ mãsu azãbta ta ne da azãba mai tsanani. Wancan ya kasance a cikin littãfi rubũtacce.

(59) Kuma bãbu abin da ya hana Mu, Mu aika da ãyõyi fãce sabõda mutãnen farko sun ƙaryata game da su. Kuma Mun bai wa Samũdãwa tãguwa, ãyã bayyananna, sai suka yi zãlunci game da ita. Kuma bã Mu aikãwa da ãyõyi fãce dõmin tsõratarwa.

(60) Kuma a lõkacin da Muka ce maka, "Lalle ne Ubangijinka Yã kẽwaye mutãne." Kuma ba Mu sanya abin da ya gani wanda* Muka nũna maka ba, fãce dõmin fitina ga mutãne, da itãciya wadda aka la'anta a cikin Alƙur'ani. Kuma Munã tsõratar da su, sa'an nan (tsõratarwar) bã ta ƙãra su fãce da kangara mai girma.
* Abũbuwan da Annabi ya gani a daren Isrã'i da Mi'irãji, watau tafiyarsa zuwa sama wadda aka yi ishãrã da ita a farkon sũrar. Itãciyar da aka la'anta ita ce Zaƙƙũm abincin mutãnen Wuta. Akwai muƙãrana, a cikin wannan,cħwa ãyõyin da aka bai wa wani Annabi sun fi waɗanda aka bai wa wasu Annabãwa girma.

(61) Kuma a lõkacin* da Muka cẽ wa malã'iku, "Ku yi sujada ga Ãdamu," sai suka yi sujada, fãce Ibilĩsa, ya ce: "shin, zan yi sujada ga wanda ka** halitta shi yanã lãka?"
* Muƙãrana a tsakãnin jinsin mutum da malã'iku da aljannu. An fĩfĩtar da jinsin mutum da sanya wa sauran jinsõshi biyu su yi masa sujada, sa'an nan aka ɗaukaka jinsin malã'ika sabõda ɗã'a, kuma aka la'anci jinsin Iblĩsa da sãɓo. ** Rubũta "ka" da ƙaramin "ka" ne kõ da yake lamĩrin Allah ne, dõmin ya nuna hãlin maganar Shaiɗan zuwa ga Allah Mai girma. Yanã yin maganar da hushi, ba da girmamawa ba.

(62) Ya ce: "Shin, kã gan ka*! Wannan wanda ka girmama a kaina, lalle ne idan ka jinkirtã mini zuwa ga Rãnar ¡iyãma lalle ne, zan tumɓuke zuriyarsa, fãce kaɗan."
* Mai sãɓõ sabõda hassada bã ya ganin girman Ubangijinsa. A cikin maganar Iblĩs akwai rashin ladabi da nũna ƙiyayya ga Ãdamu, har zuwa ga zuriyarsa, wadda ba a haifã ba tukuna.

(63) Ya ce: "Ka tafi. Sa'an nan wanda ya bĩ ka daga gare su, to, Jahannama ce sakamakonku, (Mu ba ku shi) sakamako cikakke."

(64) "Kuma ka rikitar da wanda ka sãmi ĩko a kansa, daga gare su, da sautinka, kuma ka yi hari a kansu da dawãkinka da dãkãrunka kuma ka yi tãrẽwa da su a cikin dũkiyõyi da ɗiyã, kumaka yi musu wa'adi. Alhãli kuwa Shaiɗan bã ya yi musu wa'adin kõme fãce da ruɗi."

(65) "Lalle ne bãyiNa, bã ka da wani ƙarfi a kansu. Kuma Ubangijinka Ya isa Ya zama wakĩli."

(66) Ubangijinku ne Yake gudãnar da jirgi a cikin tẽku, dõmin ku nema daga falalarSa. Lalle ne Shĩ, Yã kasance a gare ku Mai jin ƙai.

(67) Kuma idan cũta ta shãfe ku, a cikin tẽku, sai wanda kuke kira ya ɓace fãce Shi. To, a lõkacin da Ya tsira da ku zuwa, ga tudu sai kuka bijire. Kuma mutum ya kasance mai yawan butulci.

(68) Shin fa kun amince cẽwa (Allah) bã Ya shãfe gẽfen ƙasa game da ku kõ kuwa Ya aika da iska mai tsakuwa a kanku, sa'an nan kuma bã zã ku sãmi wani wakĩli ba dõminku?

(69) Ko kun amince ga Ya mayar da ku a cikin tẽkun a wani lõkaci na dabam, sa'an na Ya aika wata gũguwa mai karya abũbuwa daga iska, har ya nutsar da ku sabõda abin da kuka yi na kãfirci? Sa'an nan kuma bã ku sãmun mai bin hakki sabõda ku, a kanMu, game da Shi.

(70) Kuma lalle ne Mun girmama 'yan Adam*, kuma Muka ɗauke su a cikin ƙasa da tẽku kuma Muka azurta su daga abũbuwa mãsu dãɗi kuma Muka fĩfĩta su a kan mãsu yawa daga waɗanda Muka halitta, fĩfĩtãwa.
* Muƙãrana a tsakãnin jinsin mutum da sauran halittar Allah.

(71) A rãnar da Muke kiran* kõwane mutãne da lĩmãminsu to, wanda aka bai wa littafinsa a dã, mansa, to, waɗannan sunã karãtun littãfinsu, kuma bã a zãluntar su da zaren bãkin gurtsin dabĩno.
* Muƙãrana a Lãhira a tsakãnin al'ummõmi kuma da tsakãnin mũminai da kãfirai,.

(72) Kuma wanda ya kasance makãho* a cikin wannan sabõda haka shi a Lãhira makãho ne kuma mafi ɓata ga hanya.
* Muƙarana a tsakãnin makantar basĩra da makantar ganin ido.

(73) Kuma lalle ne sun yi kusa haƙĩƙa, su fitinẽ ka daga abin da Muka yi wahayi zuwa gare ka, dõmin ka ƙirƙira waninsa a gare Mu, a lõkacin, haƙĩƙa, dã sun riƙe ka masoyi.

(74) Kuma bã dõmin* Mun tabbatar da kai ba, lalle ne, haƙĩƙa, dã kã yi kusa ka karkata zuwa gare su ta wani abu kaɗan.
* Muƙãrana a tsakãnin sarauta da Manzancin Allah. Sarkin dũniya yanã canja manufarsa dõmin neman yardar mutãnensa. Amman Manzon Allah bã ya sãke abin da Allah Ya umurce shi da shi dõmin neman yardar Mutãne.

(75) A lõkacin, lalle ne, dã Mun ɗanɗana maka ninkin azãbar rãyuwa da ninkin azãbar mutuwa, sa'an nan kuma bã zã ka sãmi mataimaki ba a kanMu.



17 - Suratu Al'israa  2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 52644
العمر : 72

17 - Suratu Al'israa  Empty
مُساهمةموضوع: رد: 17 - Suratu Al'israa    17 - Suratu Al'israa  Emptyالخميس 15 سبتمبر 2022, 5:13 pm


(76) Kuma lalle ne, sun* yi kusa, haƙĩƙa, su tãyar da hankalinka daga ƙasar, dõmin su fitar da kai daga gare ta. Kuma a lõkacin, bã zã su zauna ba a kan sãɓãninka fãce kaɗan.
* Muƙãrana a tsakãnin mai aiki dõmin Allah, bã a iya jũyar da shi daga aikinsa dõmin neman wata kamãla, amma mai aikin dũniya anã iya canja shi dõmin haka. Kuma bambancin hijira da kõra waɗanda suka kõri Annabinsu sai a halaka su, amma waɗanda Annabinsu ya yi hijira gabãnin azãba, to, bã zã a halaka su ba.

(77) Hanyar waɗanda, haƙĩƙa, Muka aika a gabãninka, daga ManzanninMu, kuma bã zã ka sãmi jũyarwa ba ga hanyar Mu.

(78) Ka tsayar da salla* a karkatar rãnã zuwa ga duhun dare da lõkacin fitar alfijir** lalle ne karãtun fitar alfijir ya kasance wanda ake halarta.
* Tsayar da salla a cikin lõkutanta, shi ne yake hana a yaudari mutum da magana har a sanya shi ya yi abin da bai kamãta ba, ko kuma ya yi abin da sharĩ'a ta hana. ** Karãtun fitar alfijir, ana nufin sallar asuba. Sabõda haka anã son dõgon karãtu a cikinta, gwargwadon fãrã ta a duhun dare a bayan fitar Alfijir.

(79) Kuma da dare, sai ka yi hĩra* da shi (Alƙur'ãni) akan ƙãri gare ka. Akwai tsammãnin Ubangijin ka Ya tãyar da kai a wani matsayi gõdadde.
* Hĩra da Alƙur'ãni, watau a yi sallõlin nãfila na dare, shafa'i bibbiyu, a ƙãre da wutri. Ga Annabi tahajjudi da wutrin wãjibi ne ƙãri a kan abin da aka ɗõra wa sauran mutãne, a lõkacin da yake zaune a gida. Ga sauran mutãne wutri sunna ce, kamar sallõlin ĩdi da rõkon ruwa da husũfin rãnã da na wata. A nan akwai bambanci a tsakãnin Annabi da jama'arsa a wajen wutri.

(80) Kuma ka ce: "Yã Ubangijĩna*! Ka shigar, da ni shigar gaskiya, kuma Ka fitar da ni fitar gaskiya. Kuma Ka sanya mini, daga gun Ka, wani ƙarfi mai taimako."
* Kuma ka yi addu'a a cikin sallarka da bãyanta da wannan addu'a dõmin ta nũna sallamãwarka ga Ubangijinka Allah.

(81) Kuma ka ce: "Gaskiya tã zo, kuma ƙarya ta lãlãce. Lalle ne ƙarya ta kasance lãlãtacciya."

(82) Kuma Munã sassaukarwa daga Alƙur'ãni, abin da yake waraka ne da rahama ga mũminai. Kuma bã ya ƙãra wa azzãlumai (kõme) fãce hasãra.

(83) Kuma idan Muka yi ni'ima a kan mutum,* sai ya hinjire, kuma ya nĩsanta da gefensa, kuma idan sharri ya shãfe shi, sai ya kasance mai yanke ƙauna.
* Muƙãrana a tsakãnin hãlãye biyu na mutum, hãlin tsanani da hãlin cũta.

(84) Ka ce: "Kõwa ya yi aiki a kan hanyarsa. Sa'an nan Ubangijinka ne Mafi sani ga wanda yake mafi shiryuwa ga Hanya."

(85) Sunã tambayar ka ga rũhi. Ka ce: "Rũhi daga al'amarin Ubangijina ne, kuma ba a bã ku (kõme) ba daga ilmi fãce kaɗan."

(86) Kuma lalle ne idan Mun so, haƙĩƙa, Munã tafiya da abinda Muka yi wahayi zuwa gare ka. Sa'an nan kuma bã za ka sãmi wani wakĩli ba dõminka game da shi a kanMu.

(87) Fãce da rahama daga Ubangijinka. Lalle ne falalarSa ta kasance mai girma a kanka.

(88) Ka ce: "Lalle ne idan mutãne da aljannu sun tãru a kan su zo da misãlin wannan Alƙur'ãni bã zã su zo da misãlinsa ba, kuma kõ dã sãshinsu yã kasance, mataimaki ga sãshi."

(89) Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun caccanza dõmin mutãne, a cikin wannan Alƙur'ãni, daga kõwane misãli sai mafi yawan mutãne suka ƙi (kõme) fãce kãfirci,

(90) Kuma suka ce: "Bã zã mu yi ĩmãni ba dõminka sai kã ɓuɓɓugar* da idan ruwa daga ƙasa.
* Kãfiri bã ya iya hangen abinda bã a iya taɓa shi da gaɓoɓin ji na jiki, dõmin haka suka nemi ɗayan waɗannan abũbuwa ya auku kãmin su yi ĩmãni. Mũmini yanã kange da ganin basĩra, dõmin haka ya wadãtu da zaman Alƙur'ani ãyã mai isa ga ya yi ĩmãni da shi.

(91) "Kõ kuma wata gõna daga dabĩnai da inabi ta kasance a gare ka. Sa'an nan ka ɓuɓɓugar da ƙõramu a tsakãninta ɓuɓɓugarwa."

(92) "Kõ kuwa ka kãyar da sama a kanmu kaɓukka kõ kuwa ka zo da Allah, da malã'iku banga-banga."

(93) "Kõ kuwa wani gida na zĩnãriya ya kasance a gare ka, kõ kuwa ka tãka a cikin sama. Kuma bã zã mu yi ĩmãni ba ga tãkawarka, sai ka sassaukõ da wani littãfi a kanmu, munã karantã shi." Ka ce: "Tsarki ya tabbata ga Ubangijĩna! Ban kasance ba fãce mutum, Manzo."

(94) Kuma bãbu abin da ya hana mutãne su yi ĩmãni, a lõkacin da shiriya ta jẽ musu, fãce sunce, "Shin, Allah zai aiko mutum ya zamo yana Manzo."

(95) Ka ce: "Dã malã'iku sun kasance a cikin ƙasa, kuma sunã tafiya, sunã masu natsuwa, lalle ne dã mun saukar da malã'ika daga sama ya zama manzo a kansu."

(96) Ka ce: "Allah Yã isa zama shaida a tsakãnina da ku. Lalle Shi Ya kasance ga bãyinsa, mai ƙididdigewa ne Mai gani."

(97) Kuma wanda Allah Ya shiryar, to, shĩ ne shiryayye, kuma wanda Ya ɓatar to bã zã ka sãmi waɗansu masõya gare su ba baicinSa. Kuma Munã tãra su a Rãnar ¡iyãma a kan fuskõkinsu, sunã makãfi, kuma bẽbãye da kurãme. Matattararsu Jahannama ce, kõ da yaushe ta bice, sai Mu ƙãra musu wata wuta mai tsanani.

(98) Wancan ne sãkamakonsu sabõda lalle sũ, sun kãfirta da ãyõ yinMu, kuma suka ce: "Shin idan muka kasance ƙasũsuwa da nĩƙaƙƙun gaɓũɓuwa, shin lalle mũ, haƙĩ ka, waɗanda ake tãyarwa ne a cikin wata halitta sãbuwa?"

(99) Shin, kuma ba su ganĩ* ba (cẽwa) lalle ne Allah, wandaYa halicci sammai da ƙasa, Mai ikon yi ne a kan Ya halicci misãlinsu? Kuma Ya sanya wani ajali wanda bãbu kõkwanto a cikinsa? Sai azzãlumai suka ƙi fãce kãfirci.
* Muƙãrana a tsakãnin farkon halitta da mayarwa da ita, idan fãrãwa ba ta buwãya ba, mayarwa bã zã ta buwãya ba.

(100) Ka ce: "Dã dai kũ, kunã mallakar* taskõkin rahamar Ubangijĩna, a lõkacin, haƙĩƙa dã kun kãme dõmin tsõron ƙãrẽwar taskõkin. Kuma mutum yã kasance mai ƙwauro ne."
* Muƙãrana a tsakãnin kyautar mutum da rõwarsa ga dũkiyar da ya mallaka.



17 - Suratu Al'israa  2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 52644
العمر : 72

17 - Suratu Al'israa  Empty
مُساهمةموضوع: رد: 17 - Suratu Al'israa    17 - Suratu Al'israa  Emptyالخميس 15 سبتمبر 2022, 5:13 pm


(101) Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun bai wa Mũsã ãyõyi* guda tara bayyanannu, sai ka tambayi Banĩ Isrã'ila, a lõkacin da ya jẽ musu, sai Fir'auna ya ce masa, "Lalle nĩ, inã zaton ka, ya Mũsã, sihirtacce."
* Muƙãrana a tsakãnin maganar makangari Fir'auna da Manzon Allah, Mũsã dõmin nũna ãyar Annabãwa ba su tsõron kõwa wajen iyar da Manzancin Allah, kuma bã su ganin wani ƙarfi a gabansu fãce na Allah.

(102) Ya ce: "lalle ne haƙĩƙa ka sani bãbu wanda ya saukar da waɗannan, fãce Ubangijin sammai da ƙasa dõmĩn su zama abũbuwan lũra. Kuma lalle ne ni, haƙĩƙa, ina zaton ka, yã Fir'auna, halakakke."

(103) Sai ya yi nufin fitar da su daga ƙasar, sai Muka nutsar da shi, shi da wanda yake tãre da shi gabã ɗaya.

(104) Kuma Muka ce: daga bãyansa ga Banĩ Isrã'ĩla, "Ku zauni ƙasar. Sa'an nan idan wa'adin ƙarshe ya zo, zã Mu jẽ da ku jama'a-jama'a."*
* Wannan magana tanã kamã da da'awar Yahũdu cewa yanã rubuce a cikin littãfinsu za su kõma haɗuwa bãyan rarraba a nan dũniya kuma Hadĩsin kõmawar Yahũdu a Falasɗĩnu, har Musulmi su yi yãƙi da su, sunã a kan gãɓar gabas kuma su Yahũdãwa suna a kan gãɓar yamma daga Kõgin Urdun yanã ƙarfafa wannan ra'ayi. Kuma an ruwaito cewa daga cikin alãmõmin Tãshin Ƙiyãma akwai kõmãwar Yahũdu a Falasɗinu. Allah ne Mafi sani.

(105) Kuma da gaskiya Muka saukar da shi, kuma da gaskiya ya sauka. Kuma ba Mu aike ka ba fãce kanã mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi.

(106) Kuma yanã abin karãtu Mun rarraba shi dõmin ka karanta shi ga mutane a kan jinkiri kuma Mun sassaukar da shi sassaukarwa.*
* Saukar da Alƙur'ãni a cikin shekaru ashirin ko ashirin da uku ya yi kama da saukar ãyõyin Mũsã tãre a lõkacin da yake kiran Fir'auna zuwa ga addini.

(107) Ka ce: "Ku yi ĩmãni* da Shi, ko kuwa kada ku yi ĩmãni, lalle ne waɗanda aka bai wa ilmi daga gabãninsa, idan anã karãtunsa a kansu, sunã fãɗuwa ga haɓõɓinsu, sunã mãsu sujada."
* Muƙãranar yin ĩmãni da rashin ĩmãnin mutãne ga Alƙur'ãni ba zai rage gaskiyarsa da kõme ba, sai dai waɗanda suka ƙi ĩmãnin ne zã su cũtu, sa'an nan da bambanci a tsakãnin mai ilmi da jãhili. Mai ilmi yanã da sauƙin jãwuwa zuwa ga gaskiya har ya rasa abin da zai aikata fãce ya fãɗi rikice, a kan haɓarsa, yanã mayar da al'amari ga Allah kuma yanã tawali'u.

(108) "Kuma sunã cẽwa: Tsarki ya tabbata ga Ubangijinmu! Lalle ne wa'adin Ubangijinmu ya kasance, haƙĩƙa, abin aikatãwa."

(109) Kuma sunã fãɗuwa ga haɓõɓinsu sunã kũka, kuma yanã ƙara musu tsõro.

(110) Ka ce: "Ku kirayi Allah* kõ kuwa ku kirãyi Mai rahama. Kõwane kuka kira to Yanã da sũnãye mafi kyau. Kuma, kada ka bayyana** ga sallarka, kuma kada ka ɓõye ta. Ka nẽmi hanya a tsakãnin wancan."
* Muƙarana a tsakãnin sũnayen Allah waɗanda ake kiran sa da su wajen rõƙo da waɗanda bã a yin roko da su. Sũnãyen mafiya kyau da ake kiran Allah da su Hadĩsi ya kãwo su sai a nħma daga Jalãlaini.** Kuma tsakaitãwa wajen karãtun salla ko addu'a kamar yadda aikin Annabi ya nũna yadda ake yi, kada a bayyana kada a ɓõye. Sai dai tsaka.

(111) Kuma ka ce: "Gõdiyã* ta tabbata ga Allah wanda bai riƙi ɗã ba kuma abõkin tãrayya bai kasance a gare Shi ba a cikin mulkinSa, kuma wani masõyi sabõda wulãkancin bai kasance a gare Shi ba." Kuma ka girmama Shi, girmamãwa.
* Ka ce: "Allah ba Shi da abõkin muƙãrana a kõwace jiha. Shi kaɗai Ya cancanci girmamãwa." Sabõda haka ka girmama Shi, girmãmãwar da ta dãce da Shi.



17 - Suratu Al'israa  2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
 
17 - Suratu Al'israa
الرجوع الى أعلى الصفحة 
صفحة 1 من اصل 1
 مواضيع مماثلة
-
» 6 - Suratu Al'an'am
» 5 - Suratu Al'ma'ida
» 103 - Suratu Al'asr
» 7 - Suratu Al'a'raf
» 52 - Suratu At'tur

صلاحيات هذا المنتدى:لاتستطيع الرد على المواضيع في هذا المنتدى
منتديات إنما المؤمنون إخوة (2024 - 2010) The Believers Are Brothers :: (English) :: The Holy Quran is translated :: Hausa-
انتقل الى: