منتديات إنما المؤمنون إخوة (2024 - 2010) The Believers Are Brothers

(إسلامي.. ثقافي.. اجتماعي.. إعلامي.. علمي.. تاريخي.. دعوي.. تربوي.. طبي.. رياضي.. أدبي..)
 
الرئيسيةالأحداثأحدث الصورالتسجيل
(وما من كاتب إلا سيبلى ** ويبقى الدهر ما كتبت يداه) (فلا تكتب بكفك غير شيء ** يسرك في القيامة أن تراه)

IZHAR UL-HAQ

(Truth Revealed) By: Rahmatullah Kairanvi
قال الفيلسوف توماس كارليل في كتابه الأبطال عن رسول الله -صلى الله عليه وسلم-: "لقد أصبح من أكبر العار على أي فرد مُتمدين من أبناء هذا العصر؛ أن يُصْغِي إلى ما يظن من أنَّ دِينَ الإسلام كَذِبٌ، وأنَّ مُحَمَّداً -صلى الله عليه وسلم- خَدَّاعٌ مُزُوِّرٌ، وآنَ لنا أنْ نُحارب ما يُشَاعُ من مثل هذه الأقوال السَّخيفة المُخْجِلَةِ؛ فإنَّ الرِّسَالة التي أدَّاهَا ذلك الرَّسُولُ ما زالت السِّراج المُنير مُدَّةَ اثني عشر قرناً، لنحو مائتي مليون من الناس أمثالنا، خلقهم اللهُ الذي خلقنا، (وقت كتابة الفيلسوف توماس كارليل لهذا الكتاب)، إقرأ بقية كتاب الفيلسوف توماس كارليل عن سيدنا محمد -صلى الله عليه وسلم-، على هذا الرابط: محمد بن عبد الله -صلى الله عليه وسلم-.

يقول المستشرق الإسباني جان ليك في كتاب (العرب): "لا يمكن أن توصف حياة محمد بأحسن مما وصفها الله بقوله: (وَمَا أَرْسَلْنَاكَ إِلَّا رَحْمَةً لِّلْعَالَمِين) فكان محمدٌ رحمة حقيقية، وإني أصلي عليه بلهفة وشوق".
فَضَّلَ اللهُ مِصْرَ على سائر البُلدان، كما فَضَّلَ بعض الناس على بعض والأيام والليالي بعضها على بعض، والفضلُ على ضربين: في دِينٍ أو دُنْيَا، أو فيهما جميعاً، وقد فَضَّلَ اللهُ مِصْرَ وشَهِدَ لها في كتابهِ بالكَرَمِ وعِظَم المَنزلة وذَكَرَهَا باسمها وخَصَّهَا دُونَ غيرها، وكَرَّرَ ذِكْرَهَا، وأبَانَ فضلها في آياتٍ تُتْلَى من القرآن العظيم.
المهندس حسن فتحي فيلسوف العمارة ومهندس الفقراء: هو معماري مصري بارز، من مواليد مدينة الأسكندرية، وتخرَّجَ من المُهندس خانة بجامعة فؤاد الأول، اشْتُهِرَ بطرازهِ المعماري الفريد الذي استمَدَّ مَصَادِرَهُ مِنَ العِمَارَةِ الريفية النوبية المَبنية بالطوب اللبن، ومن البيوت والقصور بالقاهرة القديمة في العصرين المملوكي والعُثماني.
رُبَّ ضَارَّةٍ نَافِعَةٍ.. فوائدُ فيروس كورونا غير المتوقعة للبشرية أنَّه لم يكن يَخطرُ على بال أحَدِنَا منذ أن ظهر وباء فيروس كورونا المُستجد، أنْ يكونَ لهذه الجائحة فوائدُ وإيجابيات ملموسة أفادَت كوكب الأرض.. فكيف حدث ذلك؟!...
تخليص الإبريز في تلخيص باريز: هو الكتاب الذي ألّفَهُ الشيخ "رفاعة رافع الطهطاوي" رائد التنوير في العصر الحديث كما يُلَقَّب، ويُمَثِّلُ هذا الكتاب علامة بارزة من علامات التاريخ الثقافي المصري والعربي الحديث.
الشيخ علي الجرجاوي (رحمه الله) قَامَ برحلةٍ إلى اليابان العام 1906م لحُضُورِ مؤتمر الأديان بطوكيو، الذي دعا إليه الإمبراطور الياباني عُلَمَاءَ الأديان لعرض عقائد دينهم على الشعب الياباني، وقد أنفق على رحلته الشَّاقَّةِ من مَالِهِ الخاص، وكان رُكُوبُ البحر وسيلته؛ مِمَّا أتَاحَ لَهُ مُشَاهَدَةَ العَدِيدِ مِنَ المُدُنِ السَّاحِلِيَّةِ في أنحاء العالم، ويُعَدُّ أوَّلَ دَاعِيَةٍ للإسلام في بلاد اليابان في العصر الحديث.

أحْـلامٌ مِـنْ أبِـي (باراك أوباما) ***

 

 9 - Suratu Al'taubah

اذهب الى الأسفل 
كاتب الموضوعرسالة
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 52644
العمر : 72

9 - Suratu Al'taubah  Empty
مُساهمةموضوع: 9 - Suratu Al'taubah    9 - Suratu Al'taubah  Emptyالخميس 15 سبتمبر 2022, 4:39 pm

9 - Suratu Al'taubah
(1) Barranta daga Allah da Manzon Sa zuwa ga waɗan da kuka yi wa Alkawari daga mãsu shirki*
* Kãfirai iri uku ne: mãsu addinin al'ãda kamar Lãrabãwa sũ ne mãsu shirki, sa'an nan mãsu bin Littãfi shãfaffe watau Yahudu da Nasãra sa'an nan da munãfukan wannan al'umma. Ya fãra da mãsu shirki da bayãnin irin ayubansu, sa'an nan ya yi bayãnin sauran kamar haka.

(2) Sabõda haka ku yi tafiya a cikin ƙasa watã huɗu,* kuma ku sani lalle kũ, bã mãsu buwãyar Allah ba ne, kuma lalle Allah ne Mai kunyatar da kãfirai.
* Bãyan yanke sulhu, Allah Yabai wa kãfirai watã huɗu na amãna, dõmin su ƙãre harkõkinsu da wasu ma'amalõli da suka ƙulla tãre da Musulmi, sa'an nan yãƙi ya tãshi. Anã nufin mãsu addinin al'ãda na shirki a nan.

(3) Kuma da yẽkuwa daga Allah da ManzonSa zuwa ga mutãne, a Rãnar Haji Babba cẽwa lallene Allah Barrantacce ne daga mãsu shirki, kuma ManzonSa (haka). To, idan kun tũba to shi ne mafi alhẽri a gare ku, kuma idan kun jũya, to, ku sani lalle ne kũ, bã mãsu buwãyar Allah ba ne. Kuma ka bãyar da bishãra ga waɗanda suka kãfirta, da azãba mai raɗaɗi.

(4) Sai waɗanda kuka yi wani alkawari daga mãsu shirki, sa'an nan kuma ba su rage ku da kõme ba, kuma ba su taimaki kõwa a kanku ba, to, ku cika alkawarin, zuwa gare su, har ga iyakar yarjẽjẽyarsu. Lalle ne Allah Yanã son mãsu taƙawa.

(5) Kuma idan watanni, mãsu alfarma suka shige, to, ku yãki mushirikai inda kuka sãmẽ su, kuma ku kãmã su, kuma ku tsare su, kuma ku zaune musu dukkan madãkata. To, idan sun tũba, kuma suka tsayar da salla, kuma suka bãyar da zakka to ku sakar musu da hanyarsu. Lalle Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.

(6) Idan wani daga mushirikai ya nemi maƙwabtakarka to, ka ba shi maƙwabtakar har ya ji, maganar Allah, sa'an nan ka isar da shi ga wurin amincewar sa. Wan can fa domin lalle ne su, mutãne ne waɗan da ba su sani ba.

(7) Yãya wani alkawari a wurin Allah a wurin ManzonSa yake kasancẽwa ga mushirikai, fãce ga waɗanda kuka yi wa alkawari wurin Masallaci Mai alfarma? To matuƙar sun tsaya sõsai gare ku, sai ku tsayu sõsai gare su. Lalle ne Allah Yanã son mãsu taƙawa.

(8) Yãya, alhãli idan sun ci nasara a kanku, bã zã su tsare wata zumun ta ba a cikinku, kuma haka wata amãna, sunã yardar da ku da bãkunansu kuma zukãtansu sunã ƙi? Kuma mafi yawansu fãsiƙai ne.

(9) Sun saya da ãyõyin Allah, 'yan kuɗi kaɗan, sa'an nan suka kange daga hanyar Allah. Lalle ne sũ, abin da suka kasance sunã aikatãwa yã mũnana.

(10) Bã su tsaron wata zumunta a cikin mũminai, kuma haka bãsu tsaron wata amãna. Kuma waɗannan ne mãsu ta'adi.

(11) Sa'an nan idan sun tũba* kuma suka tsayar da salla, kuma suka bãyar da zakka, to, 'yan'uwanku ne a cikin addini, kuma Munã rarrabe ãyõyi daki-daki, ga mutãne waɗanda suke sani.
* Rukunõnin Musulunci biyar ne: Kalmar shahãda da salla da azumi da zakka da hajji ga Ɗãkin Allah. Ana yãƙar mutum sabõda barin uku daga cikinsu, watau kalmar shahãda da salla da zakka kawai. Kuma uku sunã lazimtar mawãdaci da matalauci. Su ne kalmar shahãda da salla da azumi kawai. Amma zakka da hajji sai ga mai hãlin yi da wadãta.

(12) Kuma idan suka warware rantsuwõyin amãna daga bãyan alkawarinsu, kuma suka yi sũka a cikin addininku, to, ku yaki shũgabannin kãfirci. Lalle ne sũ, bãbu rantsuwõyin amãna a gare su. Tsammãnin su sunã hanuwa.

(13) Shin, bã ku yaƙin mutãne, waɗanda suka warware rantsuwõyinsu, kuma suka yi niyya ga fitar da Manzo, kuma sũ ne suka fãra muku, tun a farkon lõkaci? Shin kunã tsõron su ne? To, Allah ne marfi cancantar ku ji tsõron Sa, idan kun kasance mũminai!

(14) Ku yãƙe su, Allah Ya yi musu azabã da hannãyenku, kuma Ya kunyatar da su, kuma Ya taimake ku, kuma Ya warkar da ƙirãzan mutãne mũminai.

(15) Kuma Ya tafĩ da fushin zukãtansu, kuma Ya karɓi tũba a kan wanda Ya so. Kuma Allah ne Masani, Mai hikima.

(16) Kõ kunã zaton* a bar ku, tun Allah bai bayyana waɗanda suka yi jihãdi ba daga gare ku, kuma sũ ba su riƙi wani shigeba, baicin Allah da ManzonSa da mũminai? Kuma Allah ne Mai jarrabãwa ga abin da kuke aikatãwa.
* Watau kunã zaton ku shiga Aljanna sabõda cewarku, "Mun yi ĩmãni," kawai? Ã'aha! Sai Allah Yã bayyanar da mai gaskiyar ĩmãni game da jihãdi, kuma gaskiyar ĩmãni itace ce rashin sõyayya da wanin Allah da ManzonSa da mũminai, duka wanda ya so wani abu baicinsu, to, bã mũmini ba ne, bã zai shiga Aljanna ba dõmin wai yã yi ĩmãni kawai. Ma'anar son Allah da son Annabi shi ne rashin sãɓa wa umurninSa. Ma'anar son wanin Allah da wanin Annabi, shi ne ka yi abin da wanin nan yake so, alhãli kuwa a wajen yinsa akwai sãɓa wa Allah da Manzon Sa.

(17) Bã ya kasancewa ga mãsu shirki su rãya masallatan Allah, alhãli kuwa sunã mãsu bãyar da shaida a kan rãyukansu da kafirci, waɗannan ayyukansu sun ɓãci, kuma a cikin wutã sũ madawwama

(18) Abin sani kawai, mai rãya masallãtan Allah, shĩ ne wanda ya yi ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira, kuma ya tsayar da salla kuma ya bãyar da zakka, kuma bai ji tsõron kõwa ba fãce Allah. To, akwai tsammãnin waɗannan su kasance daga shiryayyu.

(19) Shin, kun sanya shãyar da mahajjata da rãyar da Masallaci Mai alfarma kamar wanda ya yi ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira, kuma ya yi jihãɗi a cikin hanyar Allah? Bã su daidaita a wurin Allah. Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne Azzãlumai.

(20) Waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi hijira, kuma suka yi jihãdi, a cikin hanyar Allah, da dũkiyõyinsu, da rãyukansu, sũ ne mafi girma ga daraja, a wurin Allah, kuma waɗannan sũ ne mãsu babban rabo.

(21) Ubangijinsu Yanã yi musu bishãra da wata rahama daga gare shi, da yarda, da gidãjen Aljanna. sunã da, a cikin su, ni'ima zaunanniya.

(22) Sunã madawwamã a cikinsu, har abada. Lalle ne Allah a wurinSa akwai lãda mai girma.

(23) Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku riƙi ubanninku da 'yan'uwanku masõya, idan sun nũna son kãfirci a kan ĩmãni*. Kuma wanda ya jiɓince su daga gare ku, to, waɗan nan sũ ne Azzãlumai.
* Idan an umurci mutum ya rabu da ubansa da 'yan'uwansa kãfirai, sabõda shĩ yanã Musulmi, to, ga waninsu abin yã fi ƙarfi.

(24) Ka ce: "Idan ubanninku da ɗiyanku da 'yan'uwanku da mãtanku da danginku da dũkiyõyi, waɗanda kuka yi tsiwirwirinsu, da fatauci wanda kuke tsõron tasgaronsa, da gidaje waɗanda kuke yarda da su, sun kasance mafiya sõyuwa a gare ku daga Allah da ManzonSa, da yin jihãdi ga hanyarSa, to, ku yi jira har Allah Ya zo da umurninSa! Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne fãsiƙai."

(25) Lalle ne, haƙĩƙa, Allah Yã taimake ku a cikin wurãre mãsu yawa, da Rãnar Hunainu,* a lõkacin da yawanku ya bã ku sha'awa, sai bai amfãnar da ku da kõme ba, kuma ƙasa ta yi ƙunci a kanku da yalwarta, sa'an nan kuma kuka jũya kunã mãsu bãyar da bãya.
* Hunainu wani wãdi ne a tsakãnin Makka da Ɗã'ifa inda Musulmi suka yi yãƙi da Hawãzinãwa, a cikin Shawwal shekara ta takwas. Yawan Musulmi ya rũɗe su har suka ce: "Yau bã zã a rinjãye mu ba, sabõda ƙaranci." Yawansu yã kasance dubũ gõma sha biyu, kuma kãfirai dubũ huɗu, sai suka ji tsõro, suka gudu, suka bar Annabi a kan alfadararsa Baidã'a, bãbu kõwa tãre da shĩ fãce Abbas da Abu Sufyãna wanda yake riƙe da likkãfar Annabi. Annabi ya sanya Abbas ya yi ta kiran su,"Yã Ansãr! Ya Mũhajirũn!" Har suka kõmo aka ci Nasara.



9 - Suratu Al'taubah  2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 52644
العمر : 72

9 - Suratu Al'taubah  Empty
مُساهمةموضوع: رد: 9 - Suratu Al'taubah    9 - Suratu Al'taubah  Emptyالخميس 15 سبتمبر 2022, 4:39 pm


(26) Sa'an nan kuma Allah Ya saukar da natsuwarSa a kan ManzonSa kuma a kan mũminai, kuma Ya saukar da rundunõni waɗanda ba ku gan su ba, kuma Ya azabtar da waɗan da suka kãfirta: Wancan ne sakamakon kãfirai.

(27) Sa'an nan kuma Allah Ya karɓi tũba daga bãyan wancanan ka wanda Ya so. Kuma Allah ne Mai gãfara, Mai rahama.

(28) Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Abin sani kawai, mushirikai najasa ne, sabõda haka kada su kusanci Masallaci Mai Alfarma a bãyan shẽkarar su wannan. Kuma idan kun ji tsõron talauci* to, da sannu Allah zai wadãta ku daga falalar Sa, idan Ya so. Lalle Allah ne Masani, mai hikima.
* Idan kun ji tsõron talauci sabõda hanã mushirikai zuwa hajji sabõda fataucinku da su zai rage, to, bãbu kõme, arziki ga Allah yake, Yanã bãyar da shi ga wanda Yake so.

(29) Ku yãƙi waɗan da* bã su yin ĩmãni da Allah kuma bã su ĩmãni da Rãnar Lãhira kumabã su haramta abin da Allah da Manzon Sa suka haramta, kuma bã su yin addini, addinin gaskiya, daga waɗan da aka bai wa Littãfi, har sai sun bãyar da jizya daga, hannu, kuma sunã ƙasƙantattu.
* Bãyan gama hukuncin alãƙar Musulmi da kãfiran farko, watau mãsu shirkin, Lãrabãwa, sai kuma ya fãra bayãnin alãƙar Musulmi kãfirai na biyu; watau Yahũdu da Nasãra.

(30) Kuma Yahũdãwa suka ce: "Uzairu ɗan Allah ne."Kuma Nasãra suka ce: "Masĩhu ɗan Allah ne." Wancan zancensu ne da bãkunansu. Sunã kamã da maganar waɗanda suka kãfirta daga gabãni. Allah Yã la'ance su! Yãya aka karkatar da su?

(31) Sun riƙi mãlamansu* (Yahũdu) da ruhubãnãwansu (Nasãra) Ubannangiji, baicin Allah, kuma sun riƙi Masĩhu ɗan Maryama (haka). Kuma ba a umurce su ba fãce da su bautã wa Ubangiji Guda. Bãbu abin bautãwa fãce Shi. TsarkinSa ya tabbata daga barin abin da suke yin shirki da shi.
* Hibru shi ne mãlamin Yahũdãwa, Ruhubãni mai ibãda wanda ya yanke jin dãɗin dũniya daga kansa sabõda ibãda, daga cikin Nasãra, mabiyan,gefen biyu sun riƙi shũgabanninsu ubanningiji sunã bauta musu, watau sunã yanka musu dõkoki waɗanda ba na Allah ba, sũ kuma sunã bin su a kan haka. Bautar da suke yi wa Uzairu kõ Masĩhu, Ĩsaɗan Maryama dõmin sun ce sũ ɗiyan Allah ne, watau sun zama juz'inSa ke nan. Tsarki ya tabbata ga Allah daga waɗannan siffõfi duka.

(32) Sunã nufin su bice hasken Allah da bãkunãnsu. Kuma Allah Yanã ki, fãce dai Ya cika haskenSa, kuma kõ da kãfirai sun ƙi.

(33) Shi ne wanda Ya aiko manzonSa da shiriya da addinin gaskiya, dõmin ya bayyanl shi a kan addini dukansa, kuma kõ dã mushirikai sun ƙi.

(34) Yã waɗanda suka yi ĩmãni! Lalle ne mãsu yawa daga Ahbãr* da Ruhbãnãwa haƙĩƙa sunã cin dũkiyar mutãne da ƙarya, kuma sunã kangẽwa daga hanyar Allah. Kuma waɗanda suke taskacẽwar zĩnãriya da azurfa, kuma bã su ciyar da ita a cikin hanyar Allah, to, ka yi musu bushãra da azãba mai raɗaɗi.
* Jam'in Hibru watan malamin Yahũdãwa.

(35) A Rãnar da ake ƙõna shi a kanta a cikin wutar Jahannama, sai a yi lalas da ita ga gõshinansu da sãshinansu da bãyayyakinsu, (a ce musu): "Wannan ne abin da kuka taskace dõmin rãyukanku. To, ku ɗanɗani abin da kuka kasance kunã sanyãwa a taska."

(36) Lallai ne ƙidãyayyun watanni a wurin Allah watã gõma shã biyu ne a cikin Littãfin* Allah, a Rãnar da Ya halicci sammai da ƙasa daga cikinsu akwai huɗu mãsu alfarma. Wannan ne addini madaidaici. Sabõda haka kada ku zãlunci kanku a cikinsu. Kuma ku yãƙi mushirikai gabã ɗaya, kamar yadda suke yãƙar ku gabã ɗaya. Kuma ku sani cẽwa lallai ne Allah Yanã tãre da mãsu taƙawa.
* Kõ dã, a cikin waɗannan watanni akwai mãsu alfarma, kõ da yake sũ kãfirai ba sa kiyaye alfarmarsu ba, sun shigar da wani wãyonsu a ciki wanda suke cewa Nasĩ'u (watau jinkiri); Idan sunã son su yi yãƙi a cikin ɗayan watannin, sai su halattar da shi, sa'an nan su haramta wani watã a matsayinsa, su ƙãra kãfirci a kan kafircinsu, da yin haka. Sabõda haka Allah Ya halattar da yãƙi a cikin kõwanne watã dõmin kada a mãmayi Musulmi. Kuma yin jihãdi Yanã cikin ayyukan ibãda wadda Allah Yake riɓanya lãdarta a cikin watannin, mãsu alfarma.

(37) Abin sani kawai, "Jinkirtãwa" ƙãri ne a cikin kãfirci, anã ɓatar da waɗanda suka kãfirta game da shi. Sunã halattar da watã a wata shẽkara kuma su haramtar da shi a wata shẽkara dõmin su dãce da adadin abin da Allah Ya haramta. Sabõda haka sunã halattar da abin da Allah Ya haramtar. An ƙawãce musu mũnanan ayyukansu. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutãne kãfirai.

(38) Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Mẽne ne a gare ku, idan ance muku, "Ku fita da yãƙi a cikin hanyar Allah," sai ku yi nauyi* zuwa ga ƙasa. Shin, kun yarda da rãyuwar dũniya ne daga ta Lãhira? To jin dãɗin rãyuwar dũniya bai zama ba a cikin Lãhira, fãce kaɗan.
* Nauyi zuwa ga ƙasa, watau ku ƙãsa tãshi tsaye balle mã ku fita zuwa yãƙin da aka neme ku da shi (sabõda shi). fita da yãƙi a nan, anã nufin yãƙin Tabũka a cikin lõkacin bazara, kuma bãbu abinci dõmin Allah Ya jarrabi Musulmi, Ya fitar da mũminai da kuma munãfukai, dõmin a san yadda zã a yi ma'ãmala da su. Haka kuma a kõwane lõkaci Allah Yakan sanya wani abin jarraba na wahala a cikin Musulmi dõmin Ya bambanta mũminai daga munãfukai.

(39) Idan ba ku fita da yãƙi ba, Allah zai azabta ku da azãba mai raɗaɗi, kuma Ya musanya wasu mutãne, wasunku (a maimakonku). Kuma bã zã ku cũtar da Shida kõme ba. Kuma Allah a kan dukan kõme Mai ĩkon yi ne.

(40) Idan ba ku taimake shi ba, to, lalle ne Allah Yã taimake shi, a lõkacin da waɗanda suka kãfirta suka fitar da shi, Yanã na biyun biyu, a lõkacin da suke cikin kõgon dũtse, a lõkacin da yake cẽwa da sãhibinsa: "Kada ka yi baƙin ciki, lalle ne Allah Yanã tãre da mu." Sai Allah Ya saukar da natsuwarSa a kansa, kuma Ya taimake shi da waɗansu rundunõni, ba ku gan su ba, kuma Ya sanya kalmar waɗanda suka kãfirta maƙasƙanciya, kuma kalmar Allah ita ce maɗaukakiya. Kuma Allah ne Mabuwãyi, Mai hikima.

(41) Ku fita da yãƙi kunã mãsu sauƙãƙan kãyã da mãsu nauyi, kuma ku yi jihãdi da dũkiyõyinku da kuma rãyukanku a cikin hanyar Allah. Wancan ne mafi alhẽri a gare ku, idan kun kasance kunã sani.

(42) Dã yã kasance* wata siffar dũniya ce: makusanciya, da tafiya matsakaiciya, dã sun bĩ ka, kuma amma fagen yã yi musu nĩsa. Kuma zã su yi ta yin rantsuwa da Allah, "Dã mun sãmi dãma, dã mun tafi tare da ku." Sunã halakar da kansu (da rantsuwar ƙarya) ne, kuma Allah Yanã sanin lalle, haƙĩƙa, sumaƙaryata ne.'
* Ya Shiga bayãnin siffõfin munãfukai waɗanda suka ƙi fita da waɗanda suka fita zuwa Tabũka, da waɗanda suka nemi wani uzuri, a cikin siffõfi dabam-dabam da zã a iya gane munãfukai da su acikin kõwane zãmani na rãyuwar Musulmi a Dũniya.

(43) Allah Ya yãfe maka laifi. Dõmin me ka yi musu izinin zama? Sai waɗanda suka yi gaskiya ssun bayyana a gare ka, kuma ka san maƙaryata.

(44) Waɗanda suke yin ĩmãnida Allah da Rãnar Lãhira, bã zã su nẽmi izininka ga yin, jihãdida dũkiyõyinsu da rãyukansu ba. Kuma Allah ne Masani ga mãsu taƙawa.

(45) Abin sani kawai, waɗanda bã sa ĩmãni da Allah, da Rãnar Lãhira, kuma zukãtansu suka yi shakka, sũ ne ke nẽman izininka, sa'an nan a cikin shakkarsu sunã ta yin kai kãwo.

(46) Kuma dã sun yi nufin fita, dã sun yi wani tattali sabõda shi, kuma amma Allah Ya ƙi zãburarsu, sai Ya nauyayar da zamansu. Kuma aka ce ku zauna tãre da mãsu* zama.
* Watau mãtã da yãra da gajiyayyu.

(47) Dã sun fita a cikinku bã zã su ƙãre ku da kõme ba fãce da ɓarna, kuma lalle dã sun yi gaggãwar sanya annamĩmanci a tsakãninku, sunã nẽma muku fitina. Kuma a cikinku akwai 'yan rahõto sabõda su. Kuma Allah ne Masani ga azzãlumai,

(48) Kuma lalle ne, haƙĩƙa sun nẽmi fitina daga gabãni, kuma, suka jũya maka al'amari, har gaskiya ta zo,* kuma umurnin Allah Ya bayyana, alhãli sunã mãsu ƙyãma,
* Tun farkon zuwan Annabi a Madĩna mũnafukai sun yi ta yin kaidi dõmin su ɓãta al'amarin Annabi da Musulunci, suka kãsa, har gaskiya ta bayyana, suka kãma bakinsu dõmin rashin abin da zã su iya faɗã a yarda da shi.

(49) Kuma daga cikinsu* akwai mai cẽwa, "Ka yi mini izinin zama, kuma kada ka fitine ni." To, a cikin fitinar suka fãɗa. Kuma lalle ne Jahannama, haƙĩƙa, mai ƙẽwayẽwa ce ga kãfirai.
* Kuma a yanzu ga yãƙin Tabũka (munafukai) sun bayyana da irin uzurran da suke kãwowa dõmin kada su fita kamar mai cewa" To, Allah Ya hana zina, idan na fita nã gã mãtan Rũmãwa, bã zan iya yin haƙuri daga barinsu ba' sabõdahaka inã son a karbi uzurina kada a jefa ni a cikin fitina." Bai sani ba. da wannan rashin fitar ya jefa kansa a cikin fitinar. Dõmin zã a bar shi tãre da mãtã, sũ da shi kawai.

(50) Idan wani alhẽri ya sãme ka, zai ɓãta musu rai, kuma idan wata masifa ta sãme ka sai su ce: "Haƙĩƙa, mun riƙe al'amarinmu daga gabãni."Kuma sujũya, alhãli kuwa sunã mãsu farin ciki.



9 - Suratu Al'taubah  2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 52644
العمر : 72

9 - Suratu Al'taubah  Empty
مُساهمةموضوع: رد: 9 - Suratu Al'taubah    9 - Suratu Al'taubah  Emptyالخميس 15 سبتمبر 2022, 4:40 pm


(51) Ka ce: "Bãbu abin da yake sãmun mu fãce abin da Allah Ya rubũta sahõda mu. Shĩ ne Majiɓincinmu. Kuma ga Allah, sai mũminai su dõgara."

(52) Ka ce: "Shin, kunã dãko ne da mu? Fãce dai da ɗayan abũbuwan biyu* mãsu kyau, alhãli kuwa mũ, munã dãko da ku, AllahYa sãme ku da wata azãba daga gare Shi, kõ kuwa da hannayenmu. To, ku yi dãko. Lalle ne mũ, tãre da ku mãsu dãkon ne."
* Ɗayan abũbuwa biyu mãsu kyau, sũ ne mutuwa a kan shahãda kõ rinjaya da sãmun ganĩma da izza.

(53) Ka ce: "Ku ciyar a kan yarda kõ kuwa a kan tĩlas. Bã zã a karɓa daga gare ku ba. Lalle ne kũ, kun kasance mutãne fãsiƙai."

(54) Kuma bãbu abin da ya hana a karɓi ciyarwarsu daga gare su fãce dõmin sũ, sun kãfirta da Allah da ManzonSa, kuma bã su zuwa ga salla fãce Luma sunã mãsu kasãla, kuma bã su ciyarwa fãce sunã mãsu ƙyãma.

(55) Sabõda haka, kada dũkiyõyinsu su bã ka sha'awa, kuma haka 'ya'yansu. Abin sani kawai, Allah Yanã nufin Ya yi musu azãba, da su a cikin rãyuwar dũniya, kuma rãyukansu su fita alhãli kuwa sunã kãfirai.

(56) Kuma sunã rantsuwa da Allah cẽwa, lalle ne sũ, haƙĩƙa, daga gare ku suke, alhãli kuwa ba su zamo daga gare ku ba. Kuma amma sũ mutãne ne mãsu tsõro.

(57) Dã sunã sãmun mafaka kõ kuwa waɗansu ɓulõli, kõ kuwa wani mashigi, da sun, jũya zuwa gare shi, kuma suna gaggawar shiga.

(58) Kuma daga cikinsu akwai wanda yake zunɗen ka a kan sha'anin dũkiyõyin sadaka, sai idan an bã su daga cikinta, su yarda, kuma idan ba a bã su ba daga cikinta sai su zamo sunã mãsu fushi.

(59) Kuma dã dai su lalle sun yarda da abin da Allah Ya bã su, da ManzonSa kuma suka ce: "Ma'ishinmu Allah ne, zai kãwo mana daga falalarSa kuma ManzõnSa (zai bã mu). Lalle ne mũ, zuwa ga Allah mãsu kwaɗayi ne."

(60) Abin sani kawai, dũkiyõyin sadaka na faƙĩrai ne da miskinai da mãsu aiki a kansu, da waɗanda ake lallãshin zukãtansu, kuma a cikin fansar wuyõyi, da mabarta, da a cikin hanyar Allah da ɗan hanya (matafiyi). Farilla daga Allah. Kuma Allah ne Masani, Mai hikima.

(61) Kuma daga cikinsu akwai waɗanda suke cũtar Annabi, kuma sunã cẽwa "Shi kunne* ne." Ka ce: "Kunnen alhẽri gare ku, Yanã ĩmãni da Allah, kuma Yanã yarda da mũminai, kuma rahama ne ga waɗanda suka yi ĩmãni daga gare ku."Kuma waɗanda suke cũtar Manzon Allah sunã da Azãba mai raɗaɗi.
* Shi kunne ne, ma'anarsa, kome ka gaya masa Yanã gaskatawa, watau wai ba shi da wãyon gãne gaskiyã da ƙaryã. Sabõda haka Allah Ya ce: Kunnen alheri, watau ya san gaskiya kuma yana gaskata ta, kuma ya san ƙarya, ba ya aiki da ita.

(62) Sunã rantsuwa da Allah sabõda ku, dõmin su yardar da ku. Kuma Allah da ManzonSa ne mafi cancantar su yardar da Shi, idan sun kasance mũminai.

(63) Shin, ba su sani ba cẽwa "Lalle ne wanda ya sãɓa wa Allah da ManzonSa, haƙĩƙa Yanã da wutar Jahannama, Yanã madawwami a cikinta? Waccan ita ce wulãkantãwa babba!"

(64) Munãfukai sunã tsõron a saukar da wata sũra a kansu, wadda take bã su lãbãri ga abin da yake cikin zukãtansu. Ka ce: "Ku yi izgili. Lalle ne, Allah ne Mai fitai da abin da kuke tsõro."

(65) Kuma lalle ne, idan ka tambaye,* su haƙĩƙa, sunã cẽwa, "Abin sani kawai, mun kasance munã hĩra kuma munã wãsã. Ka ce: "Shin da Allah, da kuma ãyõyinSa da ManzonSa kuka kasance kunã izgili?"
* Ana a cikin tafiya zuwa Tabũka sai wasu mutãne daga cikin munãfukai suka ce wa junansu, "Wannan Yana zaton ya ci gidajen Rumawa da Biranensu? faufau." Sai Allah Ya sanar da AnnabinSa (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) abin da suka faɗa. Sai ya ce: "Ku zo mani da waɗannan mutãne." Da suka je masa ya ce musu 'Kun ce kaza da kaza.' Sai suka yi rantsuwa da cewa: ba mu kasance ba sai muna hĩra muna wãsã.

(66) "Kada ku kãwo wani uzuri, haƙĩƙa, kun kãfirta a bãyanĩmãninku. Idan Mun yãfe laifi ga wata ƙungiya daga gare ku, zã Mu azabta wata ƙungiya sabõda, lalle, sun kasance mãsu laifi."

(67) Munãfukai maza da munãfukai mãtã, sãshensu* daga sãshe, sunã umurni da abin ƙi kuma sunã hani daga alhẽri. Kuma sunã damƙẽwar hannayensu. Sun mance Allah, sai Ya mantã da su. Lalle ne munãfukai sũ ne fãsiƙai.
* sũ duka daidai suke ga hãlinsu na sharri. Damƙe hannu shi ne rõwa.

(68) Allah yã yi wa'adi ga munãfukai maza da munãfukai mãtã da kãfirai da wutar Jahannama, sunã madawwama a cikinta. Ita ce ma'ishiyarsu. Kuma Allah Yã la'ance su, kuma sunã da azãba zaunanniya.

(69) Kamar waɗanda suke a gabãninku, sun kasance mafi tsananin ƙarfi daga gare ku, kuma mafi yawan dũkiyõyi da ɗiya. Sai suka ji daɗi da rabonsu, sai kuka ji daɗi da rabonku kamar yadda waɗanda suke a gabãninku suka ji dãɗi, da rabonsu, kuma kuka kũtsa kamar kũtsãwarsu. Waɗancan ayyukansu sun ɓãci a dũniya da Lãhira, kuma waɗannan sũ ne mãsu hasãra.

(70) Shin lãbarin waɗanda suke a gabãninsu bai je musu ba, mutãnen Nũhu da Ãdãwa da Samũdãwa da mutãnen Ibrãhĩm da Ma'abũta Madyana da waɗanda aka birkice? Manzanninsu sun jẽ musu da ãyõyayi bayanannu. To, Allah bai kasance Yanã zãluntar su ba, amma sun kasance rãyukansu suke zãlunta.

(71) Kuma mummunai maza da mummunai mãtã sãshensu majiɓincin sãshe ne, sunã umurni da alhẽri* kuma sunã hani daga abin da bã a so, kuma sunã tsayar da salla, kuma sunã bãyar da zakka, kuma sunãɗã'a ga Allah da ManzonSa. Waɗannan Allah zai yi musu rahama. Lalle Allah ne Mabuwãyi, Mai hikima.
* Abin da aka sani ga sharĩ'a shĩ ne alheri, kuma abin da da ba a sani ba ga sharĩ'a shĩ ne abin ƙi wanda bã a so.

(72) Kuma Allah Yã yi wa'adi ga mummunai maza da mummunai mãtã da gidãjen Aljanna ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwamã a cikinsu, da wurãren zama mãsu dãɗi a cikin gidãjen Aljannar. Kuma yarda daga Allah ce mafi girma. Wancan shi ne babban rabo, mai girma.

(73) Ya kai Annabi! Ka yãƙi kãfirai da munãfukai kuma ka tsaurara a kansu. Kuma matattararsu Jahannama ce. Tir da ta zama makõmar!

(74) Sunã rantsuwa da Allah, ba su faɗa ba, alhãli kuwa lalle ne, haƙĩƙa, sun faɗi kalmar kãfirci, kuma; sun kãfirta a bãyan musuluntarsu, kuma sun yi himma ga abin da ba su sãmu ba. Kuma ba su zargi kõme ba fãce dõmin Allah da ManzonSa Ya wadãtar da su daga falalarSa. To, idan sun tũba zai kasance mafi alhẽri gare su, kuma idan sun jũya bãya, Allah zaiazabtã su da azãba mai raɗaɗi a cikin dũniya da Lãhira, kuma bã su da wani masõyi kõ wani mataimaki a cikin kasa.

(75) Kuma daga cikinsu akwai wadɗanda suka yi wa Allah alkawari, "Lalle ne idan ya kãwo mana daga falalarSa, haƙĩƙa, munãbãyar da sadaka, kuma lalle ne munã kasancẽwa, daga sãlihai."



9 - Suratu Al'taubah  2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 52644
العمر : 72

9 - Suratu Al'taubah  Empty
مُساهمةموضوع: رد: 9 - Suratu Al'taubah    9 - Suratu Al'taubah  Emptyالخميس 15 سبتمبر 2022, 4:40 pm


(76) To, a lõkacin da Ya bã su daga falalarSa, sai suka yi rõwa da shi, kuma suka jũya bãya sunã mãsu bijirẽwa,

(77) Sai Ya biyar musu da munãfunci a cikin zukatan su har zuwa ga Rãnar da suke haɗuwa da Shi sabõda sãɓã wa Allah a abin da suka yi Masa alkawari, kuma sabõda abin da suka kasance sunã yi na ƙarya.

(78) Shin, ba su sani ba cẽwa lalle ne Allah Yanã sanin asĩrinsuda gãnawarsu, kuma lalle Allah ne Masanin abũbuwan fake?

(79) Waɗanda suke aibanta mãsu yin alhẽri daga mummunaia cikin dũkiyõyin sadaka, da waɗanda ba su sãmu fãce iyãkar ƙõƙarinsu, sai sanã yi musu izgili. Allah Yanã yin izgili gare su. Kuma sunã da azãba mai raɗaɗi.

(80) Kõ kã nẽma musu gãfara ko ba ka nẽma musu ba, idan ka nẽma musu gãfara sau saba'in, to, Allah bã zai gãfarta musu ba. Sabõda sũ, sun kãfirta da Allah da ManzonSa. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutãne fãsiƙai.

(81) Waɗanda aka bari sun yi farin ciki da zamansu a bãyan Manzon Allah, kuma suka ƙi su yi jihãdi da dũkiyõyinsu da rãyukansu a cikin hanyar Allah, kuma suka ce: "Kada ku fita zuwa yãƙi a cikin zãfi."Ka ce: "Wutar Jahannama ce mafi tsanlnin zãfi." Dã sun kasance sunã fahimta!

(82) Sabõda haka su yi dãriya kaɗan, kuma su yi kũkada yawa a kan sãkamako ga abin da suka kasance sunã tsirfatãwa.

(83) To, idan Allah Ya mayar da kai zuwa ga wata ƙungiyã daga gare su sa'an nan suka nẽme ka izni dõmin su fita, to, ka ce: "Bã zã ku fita tãre da nĩ ba har abada, kuma bã zã ku yi yãƙi tãre da nĩ ba a kan wani maƙiyi. Lalle ne kũ, kun yarda da zama a farkon lõkaci, sai ku zauna tãre da mãtã mãsu zaman gida."

(84) Kuma kada ka yi salla a kan kõwa daga cikinsu wanda ya mutu, har abada, kuma kada ka tsaya a kan kabarinsa. Lalle ne sũ, sun kãfirta da Allah da ManzonSa, kuma sun mutu alhãli kuwa sunã fãsiƙai.

(85) Kuma kada dũkiyõyinsu da ɗiyansu su bã ka sha'awa. Abin sani kawai, Allah Yanã nufin Ya yi musu azãba da su a cikin dũniya, kuma rãyukansu su fita alhãli kuwa sunã kãfirai.

(86) Kuma idan aka saukar da wata sũra cẽwa; Ku yi ĩmãni da Allah kuma ku yi jihãdi tãre da ManzionSa. Sai mawadãta daga gare su su nẽmi izninka, kuma su ce: Ka bar mu mu kasance tãre da mazauna.

(87) Sun yarda da su kasance tãre da mãtã mãsu zama (a cikin gidãje). Kuma aka rufe a kan zukãtansu, sabõda haka, sũ, bã su fahimta.

(88) Amma Manzon Allah da waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi, sun yi jihãdi da dũkiyõyinsu da rãyukansu. Kuma waɗannan sunã da ayyukan alhẽri, kuma waɗan nan sũ ne mãsu cin nasara.

(89) Allah yã yi musu tattalin gidãjen Aljanna, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwamã a cikinsu. Wancan ne babban rabo mai girma.

(90) Kuma mãsu uzuri daga ƙauyãwa zuka zo dõmin a yi musu izini, kuma waɗanda suka yi wa Allah da ManzonSa ƙarya, suka yi zamansu. wata azãba mai raɗaɗi zã ta sãmi waɗanda suka kãfirta daga gare su.

(91) Bãbu laifi a kan maraunana kuma haka majinyata, kuma bãbu laifi a kan waɗanda bã su sãmun abin da suke ciyarwa idan sun yi nasĩha* ga Allah da ManzonSa. Kuma bãbu wani laifi a kan mãsu kyautatãwa. Kuma Allah ne Mai gãfara, Mai tausayi.
* Nasĩha ita ce su faɗi maganar ƙwarai; kyautatãwa itace a yi aiki dõmin Allah, ba dõmin neman dũniya ba.

(92) Kuma bãbu (laifi) a kan waɗanda idan sun je maka dõmin ka ɗauke su ka ce: "Bã ni da abin da nake ɗaukar ku a kansa," suka jũya alhãli kuwa idãnunsu sunã zubar da hawãye dõmin baƙin ciki cẽwa ba su sãmi abin da suke ciyarwa ba.

(93) Abin sani kawai, laifi Yanã a kan waɗanda suke nẽman izininka alhãli kuwa sũ mawadãta ne. Sun yarda su kasance tãre da mãtã mamaya (gidãje), kuma Allah Yã danne a kan zukãtansu, dõmin haka sũ, bã su gãnẽwa.

(94) Sunã kãwo uzurinsu zuwa gare ku idan kun kõma zuwa gare su Ka ce: "Kada ku kãwo wani uzuri, bã zã mu amince muku ba. Haƙĩƙa, Allah Yã bã mu lãbãri daga lãbãrunku, Allah zai ga aikinku kuma ManzonSa (zai gani). Sa'an nan kuma a mayar da ku zuwa ga Masanin gaibi da bayyane, sai Ya bã ku lãbarin abin da kuka kasance kunã aikatãwa."

(95) Zã su yi rantsuwa da Allah a gare ku idan kun jũya zuwa gare su, dõmin ku kau da kai daga gare su. To, ku kau da kai daga gare su don kõ sũ ƙarantã ne, kuma Jahannama ce matattararsu bisa ga sãkamakon abin da suka kasance sunã tsirfatãwa.

(96) Sunã rantsuwã gare ku dõmin ku yarda da su. To, idan kun yarda da su, to, lalle ne Allah bã shi yarda da mutãne fãsiƙai.

(97) ¡auyãwã ne mafi tsananin* kãfirci da munãfinci, kuma sũne mafi kamanta ga, rashin sanin haddõjin abin da Allah Ya saukar a kan ManzonSa. Kuma Allah ne Masani, Mai hikima.
* Ƙauyãwã ne mafi tsananin kãfirci dõmin nĩsansu daga sanin hãlãyen girmamãwã da na zamantakewa, sa'an nan da nĩsansu daga Annabi har su saurari abin da ya zo da shi.

(98) Kuma daga ƙauyãwã akwai waɗanda* suke riƙon abin da suke ciyarwa a kan tãra ce, kuma sunã saurãron aukuwar masĩfa a gare ku, aukuwar mummunar masĩfa ta tabbata a kansu. Kuma Allah ne Mai ji, Masani.
* Ƙauyãwã kashi biyu ne: Akwai wãwãye munãfukai mãsu ganin addĩni yã ɗõra musu nauyin biyan zakkã da sauran ayyukan alheri, sunã ɗaukar sa kamar tãra da biyan kakkarai. Kuma akwai ƙauyãwa mãsu hankali sun sani Annabi manzo ne daga Allah, sunã ɗaukar abin da addĩni ya azã musu duka ibãda ne, sunã fãtar kusanta da shi zuwa ga Allah, Ubangjinsu. To su mutãnen ƙwarai ne, zã su shigã Aljanna.

(99) Kuma daga ƙauyãwã akawi waɗanda suke yin ĩmanida Allah da Rãnar Lãhira, kuma sunã riƙon abin da suke ciyarwa (tamkar) waɗansu ibãdõdin nẽman kusanta ne a wurin Allah da addu'õ'in ManzonSa. To, lalle ne ita (ciyarwar nan) ibãdar nẽman kusanta ce a gare su. Allah zai shigar da su a cikin RahamarSa. Lalle Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.

(100) Kuma mãsu tsẽrẽwa* na farko daga Muhãjirina da Ansar da waɗanda suka bi su da kyautatãwa, Allah Ya yarda daga gare su su kuma sun yarda daga gare Shi, kuma Ya yi mãsu tattalin gidãjen Aljanna; ¡õramu sunã gudãna a ƙarƙashinsu, suna madawwamã a cikinsu har abada. Wancan ne babban rabo mai girma.
* Yãƙin Tabũka ya kasa jama'ar Musulmi gwargwadon ĩmãninsu da ayyukansu da gabãtarsu a cikin addĩni, cikin darajõji da ɗabaƙõƙi. Darajar farko ita ce, Sahabban farko waɗanda suka tsere wa sauran mutãne ga shigã Musulunci da ƙarfin ĩmãni da yawan aiki da tsarkake zũciya ga aikin Allah.



9 - Suratu Al'taubah  2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 52644
العمر : 72

9 - Suratu Al'taubah  Empty
مُساهمةموضوع: رد: 9 - Suratu Al'taubah    9 - Suratu Al'taubah  Emptyالخميس 15 سبتمبر 2022, 4:41 pm


(101) Kuma daga waɗanda suke a gẽfenku daga ƙauyãwa akwai munãfukai,* haka kuma daga mutãnen Madnĩa. Sun gõge a kan munãfunci, bã ka sanin su, Mũ ne Muke sanin su. zã Mu yi musu azãba sau biyu, sa'an nan a mayar da su zuwa ga azãba mai girma.
* Kungiya ta biyu munãfukai mãsu zurfin wayo, sun san yadda suke ɓõye munãfuncinsu sabõda gõgewa da iya munãfunci har mutãne bã zã su iya gãne su ba, sai Allah Ya tõna su.

(102) Kuma da waɗansu, sun yi furuci* da laifinsu, sun haɗa aiki na ƙwarai da wani mummuna. Akwai tsammãnin Allah Ya karɓi tũba a kansu. Lallai Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.
* Wata ƙungiya wadda ta yi munãfunci, tã ƙi fitã zuwa yãƙi amma kuma suka ga sun yi laifi suka yi iƙirãri da cewa, "Sun yi laifi," sa'an nan suka tũba, Allah Ya karɓi tũbarsu.

(103) Ka karɓi sadaka daga dũkiyõyinsu kana tsarkake su, kuma kana tabbatar da kirkinsu da ita. Kuma ka yi musu addu'a. Lallai addu'õ'inKa natsuwã ne a gare su. Kuma Allah ne Mai ji, Masani.

(104) Shin, ba su sani ba cẽwa lallai Allah, ne Yake karɓar tũbã daga bãyin Sa, kuma Yanã karɓar sadakõkin su, kuma lalle Allah ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai?

(105) Kuma ka ce: "Ku yi aiki, sa'an nan Allah zai ga aikinku, da Manzon Sa da Muminai kuma zã a mayar da ku zuwa ga masanin fake da bayyane, sa'an nan Ya bã ku lãbãri ga abin da kuka kasance kunã aikatãwa."

(106) Kuma da waɗansu waɗanda* aka jinkirtar ga umurnin Allah, kõ dai Ya yi musu azãba kõ kuma Ya karɓi tũba a kansu. Kuma Allah ne Masani, Mai hikima.
* Wata ƙungiya wadda ita ba munãfuka ba ce, amma kuma ba su fita zuwa yãƙin ba, kuma bã su da wani dalĩli sai kasãla kawai da taushewar Shaiɗan. Waɗannan an jinkirtar da al'amarinsu har Allah Ya yi hukunci a kansu.

(107) Kuma waɗanda* suka riƙi wani masallãci dõmin cũta da kãfirci da nẽman rarrabẽwa a tsakãnin muminai da fakẽwã ga taimakon wanda ya yãƙi Allah da ManzonSa daga gabãni, kuma haƙĩƙa sunã yin rantsuwa cẽwa, "Ba mu yi nufin kõmai ba fãce alhẽri", alhãli kuwa Allah Yanã yin shaida cẽwa, su, haƙĩƙa, maƙaryata ne.
* Wata ƙungiyã ta munãfukai mãsu aiki dõmin tumɓuke ƙarfin Musulmi ta hanyar da bã a iya gãnewa da sauri. Kamarsu gina masallaci kusa da wani tsõhon masallãci da sũnan taimakon addĩni amma da nufin su raba jama'ar Musulmi,kuma sun sãmi wurin da zã su riƙa tãro da ɓõye kãyan yãƙi da shirin sharri ga Musulmi. Kamar ma'abũta Masjidil Darãr, wanda aka yi kusa da masallacin Kuba a Madĩna. Aikinsu bai tsaya ga lõkacin yãƙin Tabũka ba, sabõda haka aka ce: da bagewa ga wanda ya yãƙi Allah a gabãni, watau a gabãnin bayyanar fallasar munãfukai da yãƙin Tabũka.

(108) Kada ka tsaya a cikinsa har abada. Lalle ne, Masallaci wanda aka yi harsãshinsa a kan taƙawa tun farkon yini, shĩ ne mafi cancantar ka tsaya a cikinsa. A cikinsa akwai waɗansu maza sunã son su tsarkaka*. Kuma Allah Yanã son mãsu nẽman tsarkakuwa.
* Sunã son tsarkaka ta ɓõye da ta bayyane. Ta ɓõye sananniya ce: ita ce rashin munãfunci, kuma ta bayyane ita ce sunã kãma rũwa a bãyan sun karce kãshinsu da dũtse, kamar yadda ya zo a cikin Hadĩsi. Allah ne Mafi sani.

(109) Shin, wanda ya sanya harsãshin gininsa a kan taƙawa daga Allah da yarda, shi ne mafi alhẽri kõ kuwa wanda ya sanya harsãshin gininsa a kan gãɓar rãmi mai tusgãwa? Sai ya rũsa da shi a cikin wutar Jahannama. Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne Azzãlumai.

(110) Gininsu, wanda suka gina, bã zai gushe ba Yanã abin shakka a cikin zukãtansu fãce idan zukãtansu sun yanyanke. Kuma Allah ne Masani, Mai Hikima.

(111) Lalle ne, Allah Ya saya* daga mummunai, rãyukansu da dũkiyõyinsu, da cẽwa sunã da Aljanna, sunã yin yãƙi a cikin hanyar Allah, sabõda haka sunã kashẽwa anã kashẽ su. (Allah Yã yi) wa'adi a kanSa, tabbace a cikin Attaura da Linjĩla da Alƙur'ãni. Kuma wãne ne mafi cikãwa da alkawarinsa daga Allah? Sabõda haka ku yi bushãra da cinikinku wanda kuka ƙulla da Shi. Kuma wancan shi ne babban rabo, mai girma.
* Bãyan bayãnin nau'ukan kãfirai da alãmõminsu da yadda zã a bi wajen yankewa da su, da barin fage ga muminai na ƙwarai, sai kuma Yã kirãyi muminai zuwa ga mubãya'a ga Allah, watau ciniki, sa'an nan Ya bayyana musu kuɗin saye da abin sayarwa, ya ce: "Allah Yã saya daga muminai.".

(112) Mãsu* tũba, mãsu bautãwa, mãsu gõdẽwa, mãsu tafiya, mãsu ruku'i, mãsu sujada mãsu umurni da alhẽri da mãsu hani daga abin da aka ƙi da mãsu tsarẽwaã ga iyãkõkin Allah. Kuma ka bãyar da bushãra ga muminai.
* Sa'an nan kuma ya bayyanã a cikin wannan ãyã ta 112 siffõfin muminai waɗanda aka fuskantar da kiran neman ciniki da su.

(113) Bã ya kasancẽw*a ga Annabi da waɗanda suka yi ĩmãni, su yi istigifãri ga mushirikai, kuma kõ dã sun kasance ma'abũta zumunta ne daga bãyan sun bayyana a gare su, cẽwa lalle ne, sũ, 'yan Jahĩm ne.
* Bayãnin umurni da yanke wa kãfirai, kõ da sun mutu, da barin yi musu addu'ar alheri.

(114) Kuma istigifãrin Ibrãhĩm ga ubansa bai kasance ba fãce sabõda wani wa'adi ne da ya ƙulla alƙawarinsa da shi, sa'an nan a lõkacin da ya bayyana a gare shi (Ibrãhĩm) cẽwa lalle ne shĩ (ubansa) maƙiyi ne ga Allah, sai ya barranta daga gare shi. Lalle ne Ibrahim, haƙĩƙa, mai yawan addu'a ne, mai haƙuri.

(115) Kuma Allah bai kasance mai ɓatar da mutãne a bãyan Yã shiryar da su ba, sai Ya bayyanã musu abin da zã su yi taƙawa da shi. Lalle ne Alllh, ga kõme, Masani ne.

(116) Lalle ne Allah Yanã* da mulkin sammai da ƙasa, Yanã rãyarwa kuma Yanã matarwa. Kuma bã ku da wani masõyi, kuma bã ku da mataimaki, baicin Allah.
* Wannan ãyã tanã nũna cewa taklĩfin da Allah Yake azã wa bãyinSa na yãƙi da waninSa, bã dõmin ya wahalar da su ba ne. Yanã yi ne dõmin alheri a gare su, Shĩ Allah Mawãdaci ne, Yanã da ƙasa da sammai, kuma shĩ ne Mai yin halittar kõme.

(117) Lalle ne, haƙĩƙa, Allah Ya karɓi tũbar Anbabi da* Muhãjirĩna da Ansãr waɗanda suka bĩ shi, a cikin sã'ar tsanani, daga bãya zukãtan wani ɓangare daga gare su sun yi kusa su karkata, sa'an nan (Allah) Ya karɓi tũbarsu. Lalle, Shĩ ne Mai tausayi, Mai jin ƙai gare su.
* Yã fãra gabãtar da cewa, "Allah Yã karɓi tũbar Annabi da waɗanda Ya ambata tãre da shi," dõmin ya biyar ãyar da ke zuwa ta tũbar waɗanda suka yi zamansu, bã da wani uzuri ba, kuma sũ bã munãfuƙai ba, aka jinkirtar da maganar tũbarsu har a bãyan hõron kwãna hamsin bãbu mai yi musu magana, bisa hanin Allah. Kuma dã an ambaci karɓar tũbarsu kawai bã da an gabãtar da tũbar waɗanda suka fita ba, dã sai a ce sun fi waɗanda suka fita, dõmin an yi nassi a kan tũbarsu. Wanda aka yi nassi akan tũbarsa, yã fi wanda. aka bari a cikin duhu.

(118) Kuma (Allah) Yã karɓi tũba a kan ukun* nan waɗanda aka jinkirtar har ƙasa da yalwarta ta yi ƙunci a kansu, kuma rãyukansu suka yi ƙunci a kansu, kuma suka yi zaton bãbu wata mafakã daga Allah fãce (kõmãwa) zuwa gare Shi. Sa'an nan Allah Ya karɓi tũbarsu, dõmin su tabbata a kan tũba. Lalle Allah ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai.
* Sũ mutãne uku waɗan da aka jinkintar da al'amarinsu, a ãyã ta l06, sũ ne Ka'abu bn Mãliki da Marãratu bn Rabĩ'a el Umary, da Hilãlu bn Umaiya el Wãƙify. Sun ƙi fita, bã da wani uzuri ba, kuma a lõkacin da Annabi ya kõmo daga Tabũka, waɗanda ba su fita ba suka tafi suka faɗi uzurõrinsu na rashin fitã. Annabi ya karɓa musu Kuma ya nema musu gãfara. Amma su ukun, suka faɗi gaskiya cewa sun zauna ne bã dõmin munãfunci ba, sai dai abin yã kasance haka kawai bã da wani uzuri ba. To, Annabi ya ce su dãkata, sai abin da Allah Ya ce a kansu. Aka hana kõwa ya yi musu magana a cikin Madĩna, har mãtansu na aure. Suka yi kwãna hamsin a cikin matsuwa, sa'an nan Allah Ya sauko da tũbarsu.

(119) Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa, kuma ku kasance tãre da mãsu gaskiya.

(120) Bã ya kasancẽwa* ga mutãnen Madĩna da wanda yake a gẽfensu, daga ƙauyãwã, su sãba daga bin Manzon Allah, kuma kada su yi gudu da rãyukansu daga ransa. Wancan, sabõda ƙishirwa bã ta sãmun su, haka kuma wata wahala, haka kuma wata yunwa, a cikin hanyai Allah, kuma bã su tãkin wani matãki wanda yake takaitar da kãfirai kuma bã su sãmun wani sãmu daga maƙiyi fãce an rubuta musu da shi, lãdar aiki na ƙwarai. Lallai ne Allah bã Ya tõzarta lãdar mãsu kyautatãwa.
* Bayãnin falalar mutãne da ke zaune a Madĩna tãre da Annabi, a lokacinsa kõ bãyansa.

(121) Kuma bã su ciyar da wata ciyarwa, ƙarama kõ babba, kuma bã su kẽta wani rafi sai an rubutã musu, dõmin Allah Ya sãka musu da mafi kyãwon abin da suka kasance sunã aikatãwa.

(122) Kuma bã ya kasancẽwã ga muminai su fita zuwa yãƙi gabã ɗaya.* Sabõda haka, don me ne wata jama'a daga kowane ɓangare daga gare su ba ta fita (zuwa nẽman ilimi ba) dõmin su nẽmi ilimi ga fahimtar addĩni kuma dõmin su yi gargaɗi ga mutãnen su idan sun kõma zuwa gare su, tsammãnin su, sunã yin sauna?
* Bãyan yã ƙãre bayãni a kan falalar da Allah Ya fĩfĩta mazauna Madĩna da ita, sabõda haka bã ya halatta a gare su su sãɓa wa Annabi da zama a bãyan yã fita zuwa yãƙi. Sa'annan kuma ya yi idiraki da ishãrar cewa fitã zuwa yãƙi farillar kifãya ce; wasu sunã ɗauke wa wasu. Kuma bã ya kyautuwã a ce kõwa ya zama sojan yãƙi, a bar sauran ayyuka na lalũrar rãyuwa kamar fita neman ilmi, shi ma farillar kifãya ne tĩlas wasu su fita zuwa nemansa dõmin idan sun kõma ga mutãnensu sai su karantar da su. Hikimar ãyar tã fãra da maganar fita zuwa yãƙi kuma ta ƙãre da sakamakon kõmõwa daga makaranta dõmin nunawar fita zuwa gare su duka wajibi ne: wanda wani ke iya ɗauke wa wani. Allah ne Mafi sani.

(123) Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yãƙi waɗanda suke kusantar* ku daga kãfirai. Kuma su sami tsanani daga gare ku. Kuma ku sani cẽwa Allah Yanã tãre da mãsu taƙawa.
* Bayãnin yadda ake yin yãƙi ne; bã a fãɗa wa dukkan maƙiyã gabã ɗaya, na kusa da na nesa. Sai an fara da na kusa tukuna sa' nan nan a dinga fãɗaɗãwa.

(124) Kuma idan aka saukar* da wata sũra, to, daga gare su akwai waɗanda suke cẽwa: "Wãne a cikinku wannan sũra ta ƙãra masa ĩmãni?" To amma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma sũ, sunã yin bushãra (da ita).
* Taƙaitãwa da ƙãrin tanbĩhi ga abin da sũrar ta ƙunsa.

(125) Amma kuma waɗanda suke a cikin zukãtansu akwai cũta, to, tã ƙãra musu ƙazanta zuwa ga ƙazantarsu, kuma su mutu alhãlin kuwa sunã kãfirai.



9 - Suratu Al'taubah  2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn
مؤسس ومدير المنتدى
أحمد محمد لبن Ahmad.M.Lbn


عدد المساهمات : 52644
العمر : 72

9 - Suratu Al'taubah  Empty
مُساهمةموضوع: رد: 9 - Suratu Al'taubah    9 - Suratu Al'taubah  Emptyالخميس 15 سبتمبر 2022, 4:41 pm


(126) Shin, bã su ganin cẽwa anã fitinar su a cikin kõwace shẽkara: Sau ɗaya kõ kuwa sau biyu, sa'an nan kuma bã su tũba, kuma ba su zama sunã tunãni ba?

(127) "Kuma idan haƙĩƙa, aka saukar da wata sũra, sai sãshensu ya yi dũbi zuwa ga wani sãshe, (su ce): "Shin, wani mutum yanã ganin ku?" Sa'an nan kuma sai su jũya. Allah Ya jũyar da zukãtan su, dõmin, haƙĩƙa sũ mutãne ne, bã su fahimta.

(128) Lalle ne, haƙĩƙa, Manzo* daga cikinku yã je muku. Abin da kuka wahala da shi mai nauyi ne a kansa. Mai kwaɗayi ne sabõda ku. Ga muminai Mai tausayi ne, Mai jin ƙai.
* Bayãnin rahamar Allah game da aiko Manzõ daga cikin mutãne, cewa wata falala ce a gare su. Kuma shi Manzon nan ɗan'uwansu ne wanda bã ya son su da wani abu sai alheri, idan sun gãne dã sun bĩ shi, kuma idan ba su gãne bã, to, Allah Yã tsare shi daga sharrinsu, kuma Yã isar masa.

(129) To, idan sun jũya, sai ka ce: Ma'ishĩna Allah ne. Bãbu abin bautãwa fãce shi. A gare Shi nake dõgara. Kuma Shi ne Ubangijin Al'arshi mai girma.



9 - Suratu Al'taubah  2013_110
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
https://almomenoon1.0wn0.com/
 
9 - Suratu Al'taubah
الرجوع الى أعلى الصفحة 
صفحة 1 من اصل 1
 مواضيع مماثلة
-
» 7 - Suratu Al'a'raf
» 6 - Suratu Al - An'aám
» 71 - Suratu Nuh
» 6 - Sûratu'l-En'âm
» 38 - Sûratu's-Sâd

صلاحيات هذا المنتدى:لاتستطيع الرد على المواضيع في هذا المنتدى
منتديات إنما المؤمنون إخوة (2024 - 2010) The Believers Are Brothers :: (English) :: The Holy Quran is translated :: Hausa-
انتقل الى: